15....
Anfara gasar tsakanin sadauki da yarima, wadda ko wannensu yake kokarin nuna irin jarumtar da Allah yabasa, abun yabawa sadauki mamaki ganin yakasa kauda yarima, atake yayi wani yunkuri yatashi sama yafada kan yarima tareda jifa da takobin hannunsa, baba ibro yace yes se dana" Ajlah SADAUKI" atake aka yiwa yarima kasuwa uku lokaci guda, sadauki yadaga hannunsa sama ko akwai sauran Mai Jin kansa Shi wani ne? Wani ne yazo da katon icce zai bugawa sadauki ta baya, Ajlal dake murmushi tana kallonsa Wanda baima San tanayi ba, tace Ajlah kajuya kajuya Dan Allah! SADAUKI yabita da ido Dan baigane metake nufiba Cox sunyi nisa da juna, ganin yazo gab da sadauki yasaka Aljal yin gudu tamkar tsuntsuwa ta cabke wani takobi dayake hannun wani dogari tajefa saiti da sadauki dai2 nan sadauki yajuyo yazare ido yana kallon yanda takobin yazo dakuma daga inda yafito, ta kafafunsa yabi yasoki kafar gardin dake zuwa, ajiyar zuciya Aljal tayi, sadauki Kuma yajuya dasauri yana kallon wannan mutum daya fadi kasa, loudspeaker ya karba yana fadan ragon namiji shine Mai kaiwa maza hari ta baya Mai Jin kansa Shi namiji ne gaba da gaba da ake dashi, shin ko akwai Wanda yake jin kanshi Shi namiji ne yafito ga sadauki maza uban majaje zaki sa maza gudu sadaukin ragwayen maza, guri yayi tsiiit yayi kadi da loudspeaker yajuya zai wuce Sega wani kan doki yana haki, ganin hakan yasaka Dan tanin sakin dokin sadauki fari ne tas dokin gwanin sha'awa ' tsalle daya yayi yahaye kan dokinsa, suka fara fafatawa shida wannan jarumin bawani jimawa sadauki yakaishi kasa daga Shi har dokinsa, jarumin yace Dan Allah Karka kasheni, sadauki yayi murmushi bana kisa sedai Ina kashe zuciyar maza nasa tayi rauni, bana kisa Amma Ina illatarwa, bana kisa Kuma Ina nakasa jikin namijin dayake jin kansa waishi jarumi ne, Sannan Kuma Ina karye maza tamkar yanda ake karye Kara!
Yasa kafa yatake Shi so yakaji zancen, jarumin yace plsss Karka kasheni, sadauki yace inafa Zan maka illar dabaxaka kara iya daukar takobi ba, yasa kafarshi yatake masa hannu da kafa rak'ak'as kake ji alamar kasusuwa suna karyewa
Karfe shida na yamma suka dawo cikin gari, direct dakinsa yawuce yahada ruwan wanka yana bukatar Hutu sosai, Dan yadade Bai fita fafatawa irin wannan ba nura keyi se kuma kabir, Ajlal ma side dinsu tawuce tafada wanka saboda ranar da suka dauko tana fitowa tafara bacci, ummy tace Ke Aljal baccin yamma ba kyau fah, Ajlal tace ummy nagaji ne banida zabin daya wuce in huta, ummy tace kenan yau bazakiyiwa sadauki girkin dare ba, Ajlal tace wlh baran iyama nima rayuwa ce ina bukatar hutu, ummy tace toh Allah yasa karya fusata, Ajlal ta tabe baki tacigaba da kwanciyarta,
Tea take hadawa Sega shi yafito da alama bacci yake, bata kulasaba kuma bata Dena me take ba, sadauki yace ke Dan gidanku shine jiya kika ki zuwa kimun girki koh, bayan kinsan mun debo yunwa da gajiya, Ajlal tace yo nima ay gajiyar ce da yunwa Jan doki ay bakaramun Abu bane, sadauki yace ay cewa kikayi baki iya ba segashi kina gwadin sa'a dani Aljal tace daga dokin ne tamike tsaye takoma kitchen tacigaba da hada masa breakfast, kamar jira yake tagama yahau ci, Ajlal ta kura masa ido kamar Wanda yayi sati daya baici komai ba, sadauki yace ke kin kalli ubanki A'a kinzo kin tasani agaba se kallona kike sekace wani mirror, Ajlal ta tabe baki Ni adena zagin ubana ehe, sadauki yace idan Kuma aka k' ifa Ajlal tace koma miye dai iyaye daraja ne dasu, sadauki yace wlh idan kika Kara minti daya anan jikinki ne zai gaya, Ajlal tace ashe kana dukan mace, Albina tabanu arayuwa na tsani madokin namiji mai zagin iyaye, sadauki yajefa mata spoon din hannunshi tace wayyo Ni abbi naKuma wlh ban yafeba, tana fada ta lema aguje tabar gurin, sadauki yabita da kallo wannan yarinyar dole seta sakani yawan magana....
You lost! Try again | ||
o | o | |
x | o | x |
x | o | x |
New Game |