[07/08 11:09] pretty: 馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑 *DAGA WANKAN GIDA* 馃け馃徑馃け馃徑 Written by _meenaslimzy_ Copied,documented and Edited by: HAUSA NOVELS SOKOTO WHATSAPP No: 07068808039 Website : Abdulmkibab.hezat.com *Wanan paging farko nakune masoyana antyna Sahura da my luvly role model Maman nana(ma'am)I really luvs u irin sosai dinan馃槏* 1-5 Amina nafada miki baxakije wankan gidan nan ba saboda banga aya ko hadisi dayace dole sai anje wankan gidaba,gsky zanfada miki baxan dauki dawainiyyarki data yan gidankuba dolene kisan mexakifadawa kakarki SBD hajiya dik itace tadamu ta kwadaita miki xuwa gida wanka tunda cikinki ya shiga wata Tara take sintiri nibaxan iyaba yawwa馃槨 Kagama balain naka Ahmad to wallahi sainaje gida wanka saboda aladar gidanmu CE akaiba baxaace andainaba dik abinda xakayi kadade bakayiba kuma wallahi tallahi xankira anty Sahura infada mata takiraka tayi maka magana tunda naga ita kana ganin mutuncinta idan kuma kaki wlhy hajiya dakanta xataxo ta tafi dani yawwa馃槞 Amina zangani Nike aurenki kokece kike aurena xanje infadawa inna komi yanxun kafin in wuce wajen aiki. ********************salami alaikum,waalaiukumussalam barka da xuwa ahmadune a gidan namu sannu da xuwa INA kwana innah,lfy lau ya iyalin kowadai lfy ko?dik lafiya inna dama wata maganace naxo da ita injidai ko lafiya ahmadu'lfy lau inna maganace takawoni akan Amina iyayenta sunzomin da maganar wai lallai saidai akaita gida wanka nikuma banida wanan halin da zanrinka dawainiya da ita nace baxatajeba tace saitaje zatakira antynta tafada mata wallahi innah idan Amina taje gida wanka baxan iya daukar dawainiyaba Hmmmm innah tayi ajiyar zuciya tace kagama ahmadu kayi hakuri naji dik uzurinka kuma nasan bawani karfi garekaba amma kayi hakuri kabarta taje saboda haihuwar farice kaji kayi hakuri Allah yayi maka albarka'ameen innah shikenan nagode bari inkarasa wajen aiki to shikenan Ahmad Allah ya maka akbarka Sai anjima innah toka gaida aminar sosai ********************hello anty kintashi lafiya?lafiya lau ya yara dik kowa lfy yanaji muryarki kmr kina kuka anty wallahi rigima mukeyi da Ahmad akan xuwa wankan gida waishi babu abinda yadameshi da wanan aladar ta hausawa tunda ba aya ko hadisi馃槶yi shiru Auta dole yabarki kixo wankan gida idan bakixoba waye yakeso yakula dake dole yabi abinda mukeso tunda ya aureki wallahi tallahi koyaki koyaso xakije wanka gida ki kwantar da hankalinki nidakaina xanxo indaukeki dadi Yakama Amina ta kara narkewa da kuka anty ki kirashine saboda yaraina hajiya bayajin maganarta idan kece kuwa dole yabari"" yi shiru Amina zaibari ko wallahi musamu sabani Dan hajiya ma baxata amince da sabon tsarin da mijinki ke Neman kawo manaba inba hkba wallahi saimu daukeki gaba daya ki kwantar da hankalinki kinji Auta""""toh anty nagode sai anjima agaida yara toh ki kula da kanki 2:pm nadare Wayyoo Allah wayyo marata wayyo bayana aminace keta murkususu tanata zufa ciwo yadameta Ahmad ya juya mata baya yanata baccinsa"fusata tayi ta dukesa a baya yayi furgigit yatashi ke lafiya kikemum irin wanan dukan yafada a fusace dakyar ta iya bude baki tace mishi Ahmad marata inaga haihuwa xanyi dasauri yatashi yasaka jallabiya yace ta mike tashirya kafin yafita da mota sutafi Asibiti dasauri bejira mexataceba yafita dakyar ta mike rana duke tadauki hijabi da kayan data hada nahaihuwa tabi bayansa xuwa kofar gate already yafita da mota ita yakejira ganin halin datake ciki yafito yakamata yashigar da ita yarufe yaja motarsa Suna isa Asibiti yarinka horn megadi yafito ya bude musu gate yashige dagudu yanafitowa yahau kiran nurses sukafito aka kama Amina aka shiga da ita dakin haihuwa nan Ahmad tafara suntiri kafin a dubata yana nan tsaye nurse tafito yace yaya tace haihuwa CE waye xai xauna da ita yace shine mijinta bari yaje yadauko kanwarsa Assalamu alaikum Ahmad ne inna kubude Amina tana Asibiti naxone intafi da daya dagacikin yaran nan INA ta bude tace bari ataso zahrau kutafi yace to yananan tsaye ta taso zahrau ya juya suka shiga mota suka wuce......... Suna isa Asibiti wajen karfe 3:20 kasancewar gidan innah da asibitin akwai nisa yatarar da nurse guda daya a reception tana xaune sukayi sallama ta amsa yace sister ya mejikin tace da sauki tanasamum ciwo sosai insha allahu xuwa asuba ta haihu Ahmad hankalinsa atashe yace Allah yasa tace amin gabansane yafadi daya tuna cewa Amina idan ta haihu gida zaa tafi da ita Wanda hakan beyi masa dadiba Suna zaune aka kira sallah yatashi yacewa zahrau bari yayi sallahr asuba yadawo tace toh Da gudu nurse tafito tacewa zahrau ina mijin me haihuwa tace yaje sallah tace to dama zatafada mishi ansamu karuwa ta haihu tasamu ya mace alhamdulillah zahrau tace yayinda take kokarin kiran innah a waya tafarayi mata albishir Innah nice zahrau Amina ta haifi ya mace yayanma yaje masallaci besaniba guda inna ta rangada tace iyyeee Allah yaraya ta munsamu jikar farko a gidan nan bari inkira alhajin Zaria infada mishi tana kashewa Ahmad yadawo daga masallaci nan Zahra keshaida mishi anty Amina ta haifi diya mace bakin Ahmad yaki rufuwa saboda far in cikin yasamu me sunan innah Kafin gari ya waye labarin haihuwar amima yakarade dangimsu duka biyu nakusa Dana nesa murna a wajen kakar Amina baa magana nan da nan takira danginsu tafada Ahmad dik murnar dayakeyi hankalinsa tashi yakeyi idan ya tuna xaatafi da abar kaunarsa Amina wai gida wanka yasan halin yan uwanta basuda mutunci basudamuda yanada kudi ko babuba xaayita damunsa da bani bani shiyasa hankalinsa yake a tashe........ *Meenaslimzy* [07/08 11:09] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑 DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by *Meenaslimzy* 6-10 Ajiyar zuciya yasauke lokaci daya sallamar da nurse tayi mishi yadawo dashi daga dogon tunanin dayakeyi ya amsa mata da murmushi a fuskarta tace mishi dama taxo fada mishi angama gyara matarsa da jaririya saboda HK xai iya shiga yagansu ta juya cikin murna ya bita har wata kofa data nuna mishi yatura da sallama ya shiga Fuskar Amina daukeda murmushi take kallon mijinta yayinda tausayinsa yashigeta lokaci daya data tuna fitinar yau uwanta akan saitace gida wanka tanason mijinta tana tausayinsa batason abinda xai bata mishi rai tasan cewa bakaramin damuwa yake cikiba akan tafiyarta wanka gida xatayi iya kokarinta ganin ta kwantar masada hankalin akan tafiyar tata xakuma ta bashi hakuri akan musayar miyau da sukayi a safiyar ranan da xata haihu""""murmushi tayi sanan lokaci daya tayi ajiyar zuciya tadawo da dubanta gareshi yadda yadauki jaririyar ya kura mata ido yana kallonta cikeda so da kauna saita tsinci kanta da murmushi ta matso kusa dashi ta dafashi yadago Kansa ya maida dubansa gareta at d same time shima fuskarsa dauke da murmushi Ahmad takirayi sunansa da wata irin murya me taushi yadago kai batare daya amsaba yana rungume da jaririyar tacigaba da cewa Dan Allah kayi hakuri mijina akan bata maka rai danayi a jiya da safe kayafemun kaji mijina a lokacin hawaye nabin kumatunta tacigaba da cewa kayi hakuri da mgnr xuwa wanka gida ka kwantar da hankalinka xandawo gareka nima baason raina bane xanje gida wanka tunda wanan aladar andade da dainata mutane sunwaye tunda ba musulinci yace ayiba gidanmune kawai sukadauki xuwa wankan gida aladarsu amma kayi hakuri ka kwantar da hankalinka xandawo gareka da zarar nagama wankan kwana arbain dinda akeyi na aladar hausawa kaji mijina"""""kura mata ido yayi lokacinda tagama maganar yasa hannu yashare mata hawaye yace kidaina kuka Amina nahakura already narigada nayi magana da innah tabani hakuri na amince kada kisakeyin kuka kinji abar kaunata ya rumgumesu duka itada jaririyar yanajin son matarsa da yarsa cikin zuciyarsa yayinda dukansu kowa da abinda yake sakawa a ransa.. Kwankwasa kofarce tadawo dasu duka daga cikin tunanin da sukeyi rungume da juna da Sauri tasakesa yaje yabude kofar lokacin gari yayi Haske innah CE da Zahra suka shigo fuskarta dauke da murmushi tanacewa nayi kishiya naxo inganta kota fini kyau fuskar Zahra dauke da murmushi ta amshi yarinyar a hannun Ahmad ta mikawa innah.....tubar kallah masha allahu kawai innah ke maimaitawa yarinya kyakkyawa da ita Allah ya rayata zahrace ta amsa da amin itako Amina sai sunkuyar da kai takeyi tana murmushi ina ta kalli Amina cikeda kulawa tace sannu Amina kinji Allah ya baki lafiya kema kinji badai wata matsala ko Amina tace babu matsala innah tace to alhamdulillah dama cewa nayi bari inlekoku inkoma gida saboda nasan su sumayya na gida na hada muku abin karyawa Sunata zumudin zuwa ganin sabuwar jaririya sumayya da son yara Allah yasa dai tabari yan barka su dauka馃おdukansu sukasa dariya sukayi sallama da inna ta wuce Misalin karfe 8:30 hajiya da anty Sahura suka shigo asibitin da sallamarsu suka shige dakinda Amina ke kwance da jaririya da Zahra da Ahmad da faraar Amina ta amsa farin ciki fal a fuskarta ganin yan uwanta itama sunxo Dan risunawa Ahmad yayi yagaida anty Sahura da hajiya suka amsa ba yabo ba fallasa ganin yan uwan Amina yasa Zahra kanwar Ahmad ficewa tabasu guri Ahmad din juyawa yayi zaifita anty Sahura ta dakatar dashi da cewa tsayawa xakayi muji ina muka tsaya da maganar tafiya da Amina wankan gida saboda munga kamar kafi kowa kaunar matarka to dolene mutafda ita akanka baxamu fasa aladar gidanmuba ya dukar dakai yace anty dama nahakura xataxo wankan gida dama nabarine inyi magana da innah mahaifiyata muyi shawara to ta amince Hajiyace ta watsa mishi wani kallo tace da xaka nuna mana kunfi kowa soyayya ne to ba Wanda ya isa ya juya mana aladar gidanmu saboda haka daga asibitin nan gida zamu wuce da ita idan munje gidan zamu tura a kwaso kayanta....""""bada son ran Ahmad ba yace to hajiya saboda bayasonyim jayayya da surukansa Zuciyarsa cikeda kunci yafita harabar asibitin yana tunani kala kala....... Anty sahurace zaune gefen gado hanunta dauke da jaririya takecewa Amina ke yar sarki miji koh kece mecewa baxakixo wanka gidaba inhar Ahmad bayaso to kibiye masa kixauna gidanki keba iyayiwa kanki wankan jego zakiyiba yadda yakamata ki lalace kinaji kina gani ya auro wata""""""Amina zuciyarta ciketake da kuncin maganganun da hajiya da Anty Sahura sukafadawa mijinta bataji dadiba aikobakomi shike aurenta kuma dole a bishi a hankali a lallasheshi ya amince bawai ayita fada masa maganganu marasa dadiba gaskiya bataji dadiba ita baxata biyewa hajiya da anty Sahura su kashe mata aureba tashaji a labarai a gaske daga wankan gida ne akeyin sanadiyyar mutuwar aure ita tanason mijinta......... ********************nursece ta shigo da takaddar sallama a hanunta ta mikawa Amina da takaddar magani ta shaida mata zasu iya tafiya gida nantake Amina takira Ahmad take shaida masa ansallamesu yace to dama yana harabar asibitin shida zahrau ...... Shigowa yayi da sallama yatarar sunhada kaya anty Sahura rike da jaririyar suka fice xuwa mota dukansu sukashige gidan baya inda zahra ta zauna a gaban mota yajasu a hanyane yakirayi innah yake shaida mata a waya cewa an sallamesu suna hanyar tafiya gidan iyayen Amina saboda kadasu sumayya suyi wahalar xuwa Asibiti innah tayi ajiyar zuciya tace shikenan bakomi xanfada musu saisuje gidan sukayi sallama takashe wayar Suna isa kofar gidan Ahmad yayi parking Zahra ta tayasu shiga da kaya cikin gida tafito taxauna a mota tanajiran yayanta""""binsu yayi har dakin da aka warewa Amina Dan zaman jego yayiwa jaririyarsa huduba da sunan innah wato HAUWAU yamikawa Amina ita ya kalli Inda anty Sahura take zaune tana cika tana batsewa yace sufada mishi abubuwan bukata ta bude Jakarta ta Ciro zungureriyar takarda data cikata fam da rubutu ta mika masa saida gaban Amina yafadi a ranta takecewa lallai anty wato harda list tayiwa Ahmad zuciyar Amina na kuna tasan cewa mijinta ba hali gareshiba rufin asirin Allah ne da shagon atamfofi dayakedashi a kasuwa tasan bakaramin takura xaiyiba a ranta tace akwai Allah Ahmad yana karbar takarda yajuya batare da ya budeba yaficewarsa yasamu Zahra a mota yaja suka wuce gidan innah....... *Meenaslimzy* [07/08 11:09] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* _Written by_ *Meenaslimzy* *DEDICATION TO hauwau muazu amir* 1鈨�1鈨�-1鈨�5鈨� Ahmad yanata sauri yaje yasauke Zahra a gida saboda yasamu innah su tattauna abinda xaayi na jego....suna shiga gida cikin faraa dik kannensa ke gaisheshi sukeyi masa barkar samum karuwa da yayi ya wuce su yashiga ya tarar da inna tana karyawa nan ya xauna tace azubo mishi kunu.da kosai aka zubo mishi ya xauna yafara ci kenan saiya tuna da farar takadar da akabashi a gidansu amina Yana kurbar kunun tsamiya ya bude takaddar abinda yaganine yasa dakyar ya iya hadiye kunun daya kurba nan da nan fuskarsa ta canja tashin hankalin ya bayyana A fuskarsa ajiye kofin yayi ya kalli inna yaga shitake kallo ganin fuskarsa ta canja innah tace lafiyadai ko ahmadu Murmushim karfin hali yayi yace lafiya lau Inna tace wanan farar takaddar danake gani a hannunkafa yace a gidansu amina akabani abubuwan dasuke bukatane Gaban inna saida yafadi saboda tasan halin yan uwan matar danta basuda mutunci tun daga kan kayan aure da aka kai musu suka raina tasani cewa karantattun mutanene dakyar ta hadiyi miyau tace me suka rubuta?""murmushi Ahmad yayi yace a lissafin da sukayimun wurin kayan dubu Dari sukayimun harda kayan abinci buhun shikafa itacen wanka da sauran abubuwan bukata innah a halin yanxun banida wanan kudin wallahi kuma nasan akan wanan list din bakaramin fada xamuyi da yan uwan aminaba yakarashe maganar muryarsa tana rawa kamar xaiyi kuka Cikin bacin rai inna kecewa xaayi musu babune abinda kakedashi shixakayi aibakaibace sudauki yarinyar sutafi da ita gida wankaba bayan yanxun zamani ya canja andaina daukan yara atafi dasu wankan gida gaskiya wanan karon baxan dauki rashin mutunciba idan mundauka lokacin kaikayan aurenka""" Ahmad kurawa inna ido yayi saboda tunda yakeda mahaifiyarsa shine babban danta betaba ganin bacin ranta har tayi fushi hkba ajiyar zuciya yayi yace kiyi hakuri inna ki kwantar da hankalinki yanxun musan abinda xamuyi a gurina dai innah wlhy dubu goma sha Biyar nake mallaki yakarashe maganar gwanin tausayi Innah tausayin Dan natane yakamata tace a gurinta akwai dubu biyar xatabashi ya hada yasiya musu abinda yasamu yakai musu bari in kira sumayya taxo kuje tare kasuwa daganan kukai musu"""yayi ajiyar zuciya yace nagode innah Sumayya!!!inna takirayi sunanta ta amsa ta shigo dakin cikeda ladabi taxauna gani innah "" dama yayanku xaki raka kasuwa yanxun xakuje gidansu amina daganan kiyi musu barka cikeda murna sumayya ta mike tace bari indauko hijabi yaayaah yace to kisameni a mota ya mike yacewa inna saimun dawo Tafiya yakeyi a cikin mota zuciyarsa babu abinda take saka masa sai tunani kala kala yanda xaije gidansu amina yakai musu abinda yakedashi yasan xaa kwashi drama"""sumayyace ta dubi yayan nata tace lafiya yaayaah naga dik yanayinka ya canja murmushi ya kakalo yace bakomi Sumy ta gyada kai Sunyi siyayya daidai ta me karamin karfi danginsu kayan tea shinkafa da kayan masarufi pampers din yara da sauran abubuwan jego sumayya ta tayashi kwasa sukasa a mota suka kama hanyar gidansu amina gabanshi na faduwa Dan besan mexai tarar ba A gidansu amina kuwa ancika domin amina itace autar gidansu kasancewar mahaifiyarsu tarasu kakarsu CE kexaune a cikin gidan mahaifiyar babanta dayakeda rai amma shikanshi hajiyar tafi karfinsa sai yadda takeso yakeyi dik hayaniyar da akeyi a dakin na yan barka amina hankalinta bayajikinta yana tare da mijinta da akabashi farar takadda tunaninta wani Abu ne aka rubuta a takkadar da akabawa Ahmad yanxun ya xaiyi idan bashida wanan kudin tasan mijinta ba karfi gareshiba bakaramar matsala zaasamu dashi da yan gidansuba batagama tunanin datakeyiba tajiyo muryar sumayya tana sallama a kofar dakin firgigit tadawo daga tunanin da takeyi ta kakalo murmushi tace sannu da xuwa sumayya kishigo Ta bi tagefen wadanda ke xaune a tsakiyar dakin sunacin dumamen tuwo ba Wanda ya amsa mata sallama ta haye saman gadon tadau jaririya ta rungume da murna a fuskarta tace anty amina da yaayaah Ahmad muke gashinan shigowa saida gaban amina yafadi saboda tunanin mesukaxo dashi Yarane sukagani suna shigowa da yan kayayyaki a ledoji manya tsugul tsugul hajiyace tace kai waya aikoku da wadanan kayan karaf sumayya tace yaayaah Ahmad ne hajiya ta wurgawa sumayya wata harara tace lallai akwai balai wadanan kaya sune xasu ishi jikata zaman jego da girkin jego da xamuyi har kwana bakwai wallahi Ahmad be isaba Mu xaimaida matsiyata......... Batakarashe maganar ba Ahmad yayi sallama a kofar dakin gabansa tana faduwa yadan tsuguna yace hajiya ina kwana ya dukar dakai """" hajiya tace daban kwanaba zakaganni Ahmad baka isa ka maidamu matsiyataba wadanan kayan fa kamar mun roko? _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* *Written by* *Meenaslimzy* Dis page is devoted to Faty dan Maliki and Faty Nasir Maman maamaah 1鈨�6鈨�-2鈨�0鈨� Tambayarka nakeyi meka daukemu kayi sunkui da kai kamar mutumin arziki tundaga aurenka da amina mukasan cewa ba abin arziki a wanan shirgin kai ka kawo mana wadanan kayan a matsayin kayan jego ga matsiyata to wlhy kasani dole ka karosu dan baxasu isaba SBD yan zaman jego dole a girka abasu suci inba sokakeyi atafi damu a bakiba hajiya ta karasa magana cikin fushi """ Dik abinan da hajiya kefada Ahmad ya sunkuyar da kansa zuciyarsa tafarfasa takeyi Bacin rai kamar ya kwarma ihu zuciyarsa cikeda kunci yadago kai idanunsa kmr garwashi sunyi jajir hada idanu sukayi da Amina yaga tsantsar tashin hankali a fuskarta tabbas yasan tanacikin kunci a wanan lokacin dakyar yasaita kansa ya bude baki yace hajiya wadanan kayan danakawo yanxun basuyiba kenan nibanida kudi wallahi iya abinda nakedashi nayi muku kenan niba karfi gareniba kuyi hakuri xuwa lokacinda xansamu wasu kudin insha allahu Ahmad kenan tobaka isaba inji hajia dik yan dakin sukabita da kallo kowa da abinda yake sakawa a ransa wasu cikinsu Ahmad yabasu tausayi ganin irin wulakancin da surukarsa tayi masa saboda andauko matarsa wankan gida Hajiya tacigaba da cewa wallahi nanda jibi ka karo mana abinda mukasaka ka kawo inba hkba har gidanku xanje wajen mamanka inji ko itace ta hanaka siya mana abinda yadace nasan idan naje wajenta ita zatasaka dole kayi Ahmad da ransa yagama baci wulakantashi da akayi cikin mutani yatashi ya fice dakin sumayya data xama kmr gunki a wajen ganin rashin mutuncin da kakar anty Amina keyiwa yayan nata batada yadda xatayi ta tashi tabishi da sauri"""a gayas kibishi kuxageni idn kunje hanya hajiya ta fada Haba hajiya gaskiya banji dadin abinda kikayiwa Ahmad ba fisabilillahi kukanku kunsan ba karfi gareshiba rufin asirin Allah ne kawai amma bekamata a Dora mishi nauyin abinda baxai iyaba"""hajiya sakin baki tayi tana kallon Amina wacce kefadan wadanan maganganun fuskarta cikeda kunci da bacin ran abinda akayiwa mijinta Sannu me miji kin nuna mana kinfi kaunarsa akanmu kenan ana Neman a kwatar miki yancinki kinaso ki watsa mana kasa a idanu ki nuna mana Kinyi aure bakida kunya to baki isaba wallahi inji anty Sahura data karbe zancen kafin hajiya tace wani Abu Zuciyar Amina cikeda kunci da bacin rai tasan cewa Ahmad yanxun yayi fushi da wuya ya kara tako kafarsa gidansu shikenan ta shiga uku yan uwanta suna Neman kashe mata aure daga xuwa wankan gida yanxun ya xaayi ta lallashi mijinta wasu hawayene masu zafi suka zuraro mata a fuska ************* Tun a mota sumayya ke lallashin yayan nata tana bashi hakuri ganin yadda idanunsa sukayi ja bacin rai ya bayyana a fuskarsa ko kallon inda take beyiba yacigaba da tuka motarsa Allah ne ya kawo su gida lafiya ko parking begamaba yafito ya shige gida da sauri sumayya ta Mara masa baya Sallamar dayayima babu Wanda yaji a tsakar gidansu kasancewar kannensa keta faman aikin safe kafin ayi shirin xuwa gidansu Amina barka Innah CE xaune a falo yashiga ya xauna yana huci idanuwansa jajir cike da tashin hankali Ahmad lafiya naganka haka inna ketambayarsa dakyar ya bude baki cikin dasasshiyar murya yace innah baxan dauki wulakanci da kaskanci irin na gidansu aminaba"""mekuma yafaru yanxun? Inna munje gidan munkai kaya kakar Amina ta raina tanacewa na maidasu matsiyata Ahmad ya kwashe dik yadda sukayi yafadawa innarsa Hankalin innah bakaramin tashi yayiba tace gaskiya Ahmad bakai Saar surukaiba me akeyi da karantattun mutane gaskiya wanan karon bazamu dauki wulakanci da rashin mutunciba kayi hakuri ka kwantar da hankalinka inajiran hajiyar taxo inada amsar dik maganar daxata fadamun baxan dauki wulakanciba DAGA WANKAN GIDA sai yaxama fitina da balai ya xama sanadin karewar dik abinda ka mallaka dan shagon sukeso su amshe ribar da uwar kudin to sunyi karya kayi hakuri ka kwantar da hankalinka kaji dakyar Ahmad yace to innah Yanxun katashi kaje gida ka shirya katafi kasuwa abinka kaji kada kasaka damuwarsu a cikin ranka kaji Allah yabada saa kaji "" ameen innah nagode saina dawo ya mike yayi mata sallama ya wuce Yana fita sumayya tadawo kusada inna ta xauna tanabata hakuri ganin yadda mahaifiyarsu me hakuri ranta yabaci ************* Aminace zaune da waya a hannunta tanata kiran Ahmad tasan yanxun yana kasuwa dole takirashi tabashi hakuri ta lallashi mijinta tayi mishi kira yafi sau goma yaki daga wayarta hknan tayi hakuri ta ajiye wayar zuciyarta cikeda kunci da damuwa ********** Ahmad kuwa ganin kiran Amina a wayarsa zuciyarsa tadada harzuka saboda gani yakeyi aidik sanadintane akayi masa wulakancin da akayi masa tana kallo ta kasayin wani Abu saboda HK baxai dauki wayarba taxauna da yan uwan nata ******* Kuka sosai Amina keyiwa kanwar mamanta hajiya rukayya dataxo barka tanafada mata abinda hajiya da anty Sahura sukayiwa Ahmad gashi tanata kiran wayarsa yaki dagawa Bakaramin tausayi tabawa hajiya rukayyaba tayi murmushi tace Amina kiyi hakuri dole Ahmad yayi fushi saboda kowaye akayi masa haka baxaiji dadiba kiyi hakuri da hajiya kinji harda rikicin tsufa Dik abinda suke fada hajiya tanajinsu a kofar daki inda take xaune a tabarma ta xabura tashigo dakin tace sannu Amina wato kanwar uwarki taxo kun hadu kuna zagina to meyasa bazaku taru Ku dukeniba Allah ya baki hakuri cewar hajiya rukayya takama bakinta tayi shiru saboda tasan halin hajiya akan HK saita hadasu itada aminar ta zage amma dole tayi bakin kokarinta ganin hajiya da Sahura basuyi sanadin auren yar marainiyar Allah ba DAGA WANKAN GIDA...... *Meenaslimzy* [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy 2鈨�1鈨�-2鈨�5鈨� Hajiya rukayya ganin hajiya tafita tana sababi yasa tacewa Amina bani number wayar mijin naki insha allahu idan nakoma gida xankirashi kinji aminatu gyada mata kai Amina tayi ta dakko wayarta tabata number Ahmad din kmr yadda ta bukata nandai hajiya rukayya tayi ta bawa Amina hakuri ganin yadda hankalin Amina yatashi lokaci guda ta fita hayyacinta dakyar tasamu Amina tayi shiru sanan ta mika mata jaririyarta daketa faman kunakunai tanaso a shayar da ita Tamika mata ita tace bata abincinta kinji ta amsheta ba musu ta rungume ********** Malam Ibrahim shine mahaifin Ahmad Wanda yakeda mata daya sunanta Hauwa anace mata innah yaransu biyarne a duniya Ahmad shine babba me shekaru 37 a duniya sai zainab me bimasa da itama tayi aure tanada yara biyu ummul khairi da Jabir sai Rabiatu dake biwa zainab din itama yarta daya sunanta Khadija suna CE mata Mimi sanan sumayya kebiwa kebiwa rabiah sai Zahra autar innah wanan iyalin suna zaunene cikin rufin asirin Allah kasancewar malam Ibrahim ba karfi gareshiba shagon saida atamfofi gareshi dashi yake yiwa duka iyalan nashi abubuwan bukata wadanda ke xaune a unguwar muazu dake garin kaduna Malam Ibrahim shiya Dora Ahmad akan xuwa shagon atamfofi yaxauna tun yana yaronshi.a HK yataso har ya girma lokacin ne malam Ibrahim yabar xuwa kasuwa a HK Ahmad kexuwa har yaxamemishi jiki ya rike sanaar babansa Kwatsam ciwon kai me tsanani Yakama malam Ibrahim kwanansa daya Allah yayi mishi rasuwa mutuwar data taba wanan dankaramin family din kasancewar mutuwar mahaifinsu bayan rasuwar mahaifinsune Ahmad yacigaba da rikon shagonsu har Allah yacigaba da bunkasa mishi sanarsa yasiyi yar karamar mota Honda civic ja dayake xuwa kasuwa munna wajen wadanan iyalan baa magana kannensa suka tayashi murna sosai tare dayi masa Fatan alheri Rayuwace taci gaba ranan Ahmad na xaune a kasuwa shida abokinsa Aliyu dake kusa da shagonshi suna yar hira kowa yana kofar shagonsa yaga wata kyakkyawar yarinya taxo shagon Aliyu siyayya nan ya yaba da hankalinta bayan tagama siyayya yatambayeta sunanta ba bata lokaci tafada mata sunanta Amina kuma suna xaunene a sabon garin tudun wada kagoro ya bukaci tabashi number waya tabashi suka rabu da niyyar saiyaxo.gidansu ta tafi Malam suleman yanada mata sunanta hadiza ba fullatanace kyakktawa ta asali sunada yara shida yarta ta farko macece Sahura tana aure a Riga chikum da yara hudu sai saudat itama tanada aure da yara uku sai abubakar sai yusuf sai umar da autarsu Amina malam suleman bawata sabaa yakeda ita me karfi aikin gwamnati yakeyi karamin ma aikacine dayake aiki.a local govement Dan asalin garin Zaria ne yana xaune lfy da iyalanshi duka Inda yadauko mahaifiyarsa hajiya Aisha suke xaune tare a gida daya har ya aurar da Sahura da saudat sauran mazan kuma shiyaba kowanne kudi suke dauko gwajjo suna saidawa abubakar yusuf da Aliyu dukansu sungama secondary school basu cigaba ba saisukafara Sana'a sai Amina dake SS1 a makarantar mata dake unguwar sunusi Hajiya mahaifiyar babansu Ahmad macece masifaffiya me kwadayi da son abin duniya dik wanan abubuwan datakeyi malam suleman bayaso zuciyarsa batayi mishi dadi idan.yaga surukansa sunxo gidan mazajen saudat da Sahura hajiya tana rokonsu kudi suna bata sanan gawata dabia data dauka ta dakko yaransa wanka gida dukansu.saudat da Sahura ba Wanda baakawoshi gida wankaba kuma baa kwashewa lafiya da hajiya HK xaa gama sukoma gida Babu yadda mahaifiyarsu xatayi hknan take hakuri gashi saudat da Sahura babu abinda sukabari na hajiya wajen rashin mutunci kometakeyi shi sukeyi suke Goya mata baya idan mahaifiyarsu tayi musu fada suce kakarsuce hakanan take hakuri xama da hajiya har ranan aka wayi gari da ciwo Yakama mahaifiyarsu Amina aka kaita Asibiti akace hawan jinine yakamata hankalin malam suleman yatashi sosai saboda yasan cewa bakin cikin halin hajiyane yasawa matarsa ciwo ba bata lokaci yakira kanwar matarsa hajiya rukayya ya shaida mata suna Asibiti yar uwarta babu lafiya hawan jini. yana tsaye hajiya suka shigo gaisheda mamansu Amina saitake tambayarta keko tunanin me kikeyi hawan jini yakamaki babu Wanda ya tankawa hajiya a dakin shidai abubakar ransa zafi yakeyi ganin tambayar rainin hankalin da hajiya keyi dayasan HK xatayi da bekawota ba Ko kokafin hajiya rukayya taxo Allah yayiwa Maman su Amina rasuwa bakaramin tashin hankali malam suleman yashigaba ganin rasuwar matarsa me hakuri da kawaici shikenan yagama aure a duniya Bayan rasuwar Maman Amina da kwana bakwai abubakar da yusuf sukace baxasu xaunaba xasu tafi Neman kudi da xasu rike kanwarsu da mahaifinsu kasancewa yayyinsu mata dik sunada aure mahaifinsu yasanya musu albarka sukatafiyarsu garin Lagos sukabar umar karaminsu yanakula da mahaifinsu da kanwarsu Tun bayan rasuwar mahaifiyarsu Amina hajiya taxama komi itace kamar itace uwarsu Amina babu yadda Amina xatayi hakuri takeyi da hajiya da dik motsi saitacewa Amina kina gama makaranta fito da miji zakiyi kema ayi miki aure saidai Amina tayi murmushi To bayan Amina tadawo kasuwane take fadawa Hajiya yadda sukayi da Ahmad murna wajen hajiya baa magana saboda a cewarta jikarta tasamu miji Dan kasuwa me kudi ********** Ahmad yanadawowa kasuwa yasanar da innahrsa yahadu da wata yarinya yafada mata dik yadda akayi tace to yaje gidan yagani Allah ya tabbatar da alheri yace amin Ahmad tunda yaje gidansu Amina suka kara daidaita Kansu suke gudanar da soyayyarsu a HK hartakai ajin karshe a secondary Ahmad ya bukaci yaturo magabatansa Amina ta amince Ahmad ya tura kanin mahaifinsa akayi komi aka tsaida bikinsu Amina bayan tagama makaranta haka rayuwa tacigaba da tafiya har Allah yasa Amina ta kammala jarabawarta akafara shirin biki yan uwanta sunyi rawar gani yusuf da abubakar Dan sunada zuciyar nema sunyi mata kaya daidai karfinsu hajiya rukayya ma baabarta a bayaba itama ta taka rawar gani sosai itada yaranta suka hado nasu yayyinta saudat da Sahura ma baabarsu a bayaba tundaga kawo kayan lefe da yan uwan Ahmad sukayi akafara rigima da hajiya Dan ta raina a tunaninta Ahmad me kudine xaisaki kudi wajen biki taga ba hakaba A HK aka gabatar da bikin Amina da Ahmad dik abinda dangin Ahmad sukayi saisun rana HK.yan uwan innah sukatafi da yan uwan Amina a baki shidai Mahaifin Amina sai ido yasa musu saboda yana tsoron masifar hajiyarsa burinsa yarabu da ita lafiya kullum yana daki sabida retire da yayi a wajen aiki.... BAYAN BIKI Haka rayuwa tacigaba da tafiya Ahmad da Amina suna xaune lafiya sanan surukarta da yan uwan mijinta suna kaunarta sosai kasancewarta yarinya amma me hankali dasanin yakamata dik zugar da anty Sahura da Anty saudat akeyi mata akan yan uwan mijinta da mijinta bata dauka tana xaune dasu lafiya Kwatsam Amina tafara rashin lafiya Ahmad yakaita Asibiti nan likita yadubata yake shaida masa cewa matarsa Nada ciki murna a wajen Ahmad baa magana bayan dawowarsa gidane yaje gidansu yake fadawa innah Amina batada lafiya ga abinda likita yace tanada juna biyu itama tayi murna saboda xatasamu jika tawajen Ahmad nan suka yi shawara akan sumayya zataje taxaunadasu a unguwarsu dake kinkinau ta rinka taya Amina aiki tana xuwa makarntarta daga can Amina bakaramin dadin zamada sumayya takeyiba saboda batada son jiki komi itakeyiwa matar yayan NATA Tunda labarin Amina Nada ciki yaje gidansu hajiya tashiga murna akan kudirinta na dauko jikokinta wanka gida dakanta taje gidan ta shaidawa Amina akan aladarsu taxuwa wanka gida saida kirjinta ya buga data tuna aladar hajiya tadauko wankan gida ta amsa da xata fadawa Ahmad din nan hajiya taga sumayya a gidan ta yatsina fuska tace meye nadauko yarinya salon axo aga abinda yakeyi miki taje tafadawa uwarta asa miki ido Amina bataso wanan maganar da hajiya tayi a gaban sumayya ba saboda babu dadi saidai murmushi da sumayya tayi tabar wajen Bayan tafiyar hajiyane Ahmad yadawo kasuwa Amina kefada masa abinda hajiya tace saida gabanshi yafadi saboda yasan halin kakar Amina da yayyinta Yace gaskiya shi beyardaba hankalin Amina bakaramin tashi yayiba saboda tasan idan hajiya taji ba karamin rigima xaayi da itaba akan maganar xuwa gida wanka Dan babu me canja mata raayi gashi dama hajiyar haushin Ahmad tajeyi a cewarta kullum cikin babu yake kudinsa baya ciwuwa yana Dan kasuwa sai makon tsiya Cikin Amina yafara girma sumayya takoma gida tunda antyntata tasamu lafiya tunda cikin Amina yafara girma kullum cikin waya suke da hajiya akan maganar jadadda mata xuwa wanka gida hajiya batasan Ahmad beyardaba Amina takasa fada mata Bayan kwana biyu ne Amina takirani hajiya take shaida mata Ahmad fa beyardaba nan tafara surfa masifa xataxo har gida tasamesa..... *CIGABAN LABARI* Ahmad na xaune da abokinsa Aliyu suna hira yanayi masa barkar haihuwa da akayi masa sai Aliyu yaga dik fuskar Ahmad babu walwala yanda yasaba aliyun ketambayarsa ko lafiya Ahmad ya kwashe dik abinda kefaruwa yafadawa abokinsa cikeda damuwa Aliyu ya tausayawa Ahmad matuka sanan yace mishi inada shawara da xanbaka akan wanan tsohuwar Dan saika tashi tsaye.... _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy 2鈨�6鈨�-3鈨�0鈨� Ahmad yadada kasa kunne yaji me Aliyu xaice...Aliyu ya numfasa yace gaskiya banji dadin abinda akayi makaba Ahmad amma kayi hakuri shawara dayace xanbaka ka dauke kafarka daga xuwa gidansu dik abinda zasuce ka toshe kunnuwanka ka kyalesu kasa musu ido Dan abinda kasamu kabawa kannenka sukai musu sanan kome wanan tsohuwar xatafada kada ka biye mata saboda koba komi yanxun itace a matsayin surukarka idan ka fada mata wata magana kafadi amsa zatace kayi mata rashin kunya ka kyaleta kajiko""Ahmad yace nagode sosai da wanan shawarar taka ******** Bayan kwana biyu yakasance ranan kauri kenan ranan da ake dama kunu yan uwa su taru aminace kwance a kan gado tunani yayi mata yawa yau kwana biyu kenan rabonta da ganin Ahmad dik hankalinta baa kwance yakeba gashi yaune dama kunu hajiya tasata gaba saita kira Ahmad ya kawo musu gero da naman kai da xaadafa abawa mutane dik kiran datakewa Ahmad yaki dagawa Anty sahurace da anty saudat suka shigo sukaganta tayi shiru.tanata tunani ga yarinya tanata tsala kuka anty saudat CE tace Amina wai har yanxun Ahmad be dauki wayarba meyake nufi damu nema yakeyi ya toxartamu a dangi dik mungama fadawa mutane xaayi qauri xaa dama kunu amma Ahmad bexoba lallai ya cika Mara mutunci wallahi kuma zaisha mamaki dik maganar da anty saudat keyi Amina ba abinda takeyi sai kallonta saboda jitakeyi kamar ta tashi ta rufesu da duka saboda koma meye Ahmad yayi musu sune sukaja tunda su suka kara zuga hajiya akan adawo da ita wanka gida Anty sahurace tace wato banza damu kikayi kenan kikayi ga yan iska sunxo suna magana ko to wlhy kisani kece xakisha kunya tunda haka kawayenki xasuxo ranan suna ya kunyataki itadai Amina ba tace komiba haka suka gama sababinsu suka fice xuwa dakin hajiya ********* Innah CE xaune da yayanta zainab da rabiah kannen Ahmad suna shawarar abinda xaakai gidansu Amina saboda dama kunun jego da akeyi ranan kwana uku da haihuwa zainab ta bude Jakarta taciro kudi dubu uku tabawa innah tace gashi a auno gero mudu Biyar akai musu innah tasa mata albarka rabiah ma tabada dubu biyu tace a hada akara asiyi suga akai itama innah ta karba tayi mata godiya nan suka cigaba da tattaunawa Sallamar Ahmad CE sukaji a tsakar gida dukansu cikin faraa suke amsawa ya shigo dakin dik suka gaisheshi innah CE tabashi kudin da kannen nashi suka kawo gudun mawa yace ta rike yaciro kudi dubu Biyar yabawa innah yace a siyi nama a hada abawa Zahra da sumayya sukai gidansu Amina innah tace kai baxakaba yace ba yauba yanxun Sauri yakeyi xaije kasuwa ya bude shagon saboda yanxun hade haden kudin rago yakeyi innah tace Allah yabada saa yatafi ********* Karfe daya su sumayya sukadawo innah tace maza suci abinci Zahra da antysu rabiah suje gidansu Amina sukai wadanan kayan na kunun jego.Zahra nata murna xatakoma ganin jaririya rabonta da ita tun a Asibiti Hajiyace xaune tanata sababi akan Amina ta auri matsiyaci marowaci gashi yasa suntara mutane bekawo komiba bata karashe maganar ba taji sallama su zahrane da rabiah tare da yarta Mimi suka shigo mutanen dake tsakar gidane sukayi musu sannu da zuwa amma hajiya dasu anty saudat ko kallon arxiki basuyi musuba sune suka gaishesu suka amsa da kyar Zahrace tayi jagora har dakin da Amina take tanaganinsu tayi sassanyar ajiyar zuciya saboda tagama sadakarda baxasuxoba cikin faraa rabiah tace sannu Anty Amina kasancewar HK suke kiranta dukansu tunda matar yayansuce suka gaisa a mutunce rabiah kece mata bakiyi fushiba sai yau mukaxo itadai Amina sai murmushin karfin hali take Hajiyace da anty saudat suka shigo dakin danganin mesukaxo dashi suna shigowa tahau bude kaya sugane da gero sai Dan nama da ke cikin wata Dan karamin buhun bakko Rabi tabdijan hajiya tace gaskiya sanan gero baxai isa jamaarmubama ballantana makota gero loka Biyar haba komi Ahmad sai ya nuna shi matsiyacine komi babu Rabiah CE tayi saurin dago kai tana kallon hajiya jin ankira yayanta da matsiyaci kafin tace wani Abu anty saudat takarbe maganar da cewa wallahi Amina ba kiyi Saar mijiba me akeyi da miji me shegen makon tsiya komi yace babu Rabiah da zahra mamaki ya rufesu ganin yadda ake ciwa yayansu zarafi ana zaginshi a gabansu ba kunya ba tsoron Allah dakyar rabiah ta hadiyi miyau saboda Bacin rai tace kiyi hakuri abinda mukedashi kenan kuma baxamu matsawa kanmu ba wallahi zuciyarta na tafarfasa take fada hajiya tace wayasan meyakai gidan naku dik kunbi kun kanainaye komi kilama ragewa kukayi ta juya tafice saudat ta bita suna fita rabiah ta mike a fusace tacewa Zahra tadauki Mimi su wuce Amina ta riketa ta rusheda tana bata hakuri kuka takeyi sosai gwanin ban tausayi ganin kukan da Amina keyi yabawa rabiah tausayi ta xauna tanata lallashin Amina tausayinta yakama tace kiyi shiru kishare hawayenki anty Amina dakyar tasamu tayi shiru nan Amina kecewa rabiah wlhy Maman Mimi ina cikin matsananciyar damuwa ko abinci dakyar nakeci Ahmad shima ya juyamin baya saboda abinda su hajiya suka mishi gani yakeyi kamar ninasasu takara rushewa da kuka Zahra NATA lallashinta Rabiah tace kiyi hakuri xanyi magana da yaayaah Ahmad din insha allahu xaikiraki kinji komi xaibwuce kicigaba da hakuri kowaye akayiwa HK dole ransa yabaci saboda cin mutunci bashida dadi kinji xamutafi insha allahu damu dawo nida yayan zainab kinji ta kwantar mata da hankali sanan suka fito sunayiwa yan gidan sallama ba Wanda ya amsasu sai yan aikin kunune sukace sai anjima ******* Innah gaskiya yan uwa Amina basuda mutunci bakiga cin mutunci da cin fuskar da sukayiwa yaayaah Ahmad ba agaban Mu saboda ranmu yabaci innah gaskiya yaayaah beyi Saar surukaiba rabiah takarashe magana cikeda damuwa Zainab dake gefen innah sai huci takeyi ranta a bace dajin abinda yar uwarta kefadawa mahaifiyarsu abinda akayi musu innah wlhy da dani akaje wlhy baxan taba fitowa ban basu amsa daidai da bakinsuba amma xasusha mamakin rayuwa wlhy marasa mutunci Innah tace kada insakejin wanan maganar a bakinki zainab koba komi kunhada zuriah dasu kuma yarsu Amina ba HK takeba ita yarinyace mai mutunci da son jamaa da sanin yakamata kodan haka saimu hakura idan sunyi mana darajar yarinyar Zahrace dake gefe tacewa innah kuma Dan Allah innah kisa yayah Ahmad yakira anty Amina Dan tunda yaje gidan akayi mishi wanan wulakancin kokiransa anty Amina tayi bayan dauka dik tarame sai kuka takeyi innah saikin tausaya mata wlhy innah anty Amina tabani tausayi dukansu jikinsu yayi sanyi da kalaman Zahra akan matar yayan nasu innah CE tacewa zainab ta kira mata Ahmad a wayarta tayi magana dashi ba musu ta danna kiransa Ring in biyu yadauka a tunaninsa zainab CE sauyaji innah CE saida gabansa yafadi saboda yasan kila wani rashin mutuncin yan uwan Amina sukayi muryar innah CE tadawo dashi daga tunanin dayakeyi tace ahmadu idan ka tashi kasuwa kazo gida ina nemanka kaji ya amasa da to ta kashe wayar.... ******* Bayan magriba Ahmad ya shigo gidan ya shigo dakin inna yaxauna a gefen gadon yaxauna yajirata ta idar da lazimi datakeyi bayan sallahr magriba tashafa shima ya shafa suka gaisa nan take fada masa halina da Amina ke ciki na da ina amsa wayarta dayayi Haba Ahmad bekamataba kada ka mance marainiyar Allah CE sannan yarinyar nan ba ita tayi makaba yan uwantane mexaisa kadauki wanan hukunci akanta kasakata a damuwa ga jego tanayi ko abincin kirki ance batayi gaskiya banji dadiba dik abinda make ciki kaji tsoron Allah akwai hakinta akanka Allah saita kamaka akan haka kayi hakuri kaji kakirata Ahmad dan Allah yayi ajiyar zuciya yasan ransane ya baci amma xaiyi kokari yakirata su daidaita gidansune baxai kuma zuwaba Ajiyar zuciya yayi yakalli inna data xuba masa idanu cikeda tausayin Dan nata tasan yana cikin damuwa amma xata tayasa da addua yace insha allahu xaikirata tace Allah yayi maka albarka yace amin tace ga abincinsa nan a kula yace dashi xaitafi yadauka yayi mata saida safe yatafi Ahmad kwance a doguwae kujera a falo bayan taci abinci yayi wanka yadauki wayarsa yadanna kiran Amina..... Aminace ringume da yarta ta na shayar da ita wayar Ahmad tashigo jikinta har rawa yakeyi ta dauka tanajin muryarsa yana sallama ta fashe da kuka *Meenaslimzy* 08166177830 for comment [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy Wanan page din nakune masoyan wanan labarin Allah yabar zumunci ina sonku irin sosai dinan鉂� 3鈨�1鈨�-3鈨�5鈨� Ahmad kawai bakin Amina ya iya furtawa yayinda kukanta ya tsananta zuciyarta ta karye batajin xata iya rayuwa babu Ahmad kwana biyu kadai da yayi be kirataba tashiga matsananciyar damuwa da baxata iya jurewaba""""kuka sosai takeyi a wayar shiko Ahmad kukan Amina ba karamin kona mishi zuciya yakeyiba saboda shiyasan yanason matarsa sosai itama kuma tanasonshi amma halayen yan uwanta baxai iya jurewaba dik son dayake mata. Gyaran muryar yayi yace kiyi shiru kinji wlhy ina sonki nikaina nasan bakaramar wahala xanbawa zuciyaba idan na nisanceki amina kece farin cikina kece sanyi idaniyata wlhy Amina baxan iya jure rashinkiba naso ace wanan lokacin munji dadin rayuwa munxauna a wuri daya ina kallonki keda gudan jinina nadade ina jiran wanan lokacin amma kash "banida yadda xanyi iyayenki sundaukeki suntafi dake WANKAN GIDA kiyi hakuri kinji?shima kanshi besan lokacinda hawaye ya wanke mishi fuskaba Kalaman Ahmad bakaramin sanyayawa Amina zuciya yayiba dikda lokaci guda taji tausayin mijinta yakamata tasan cewa suna cikin matsanancin yanayi saidai Allah fatanta da adduarta a kullum Allah yasa kada kakarta da yan uwanta suyi mata sanadin aurenta DAGA WANKAN GIDA.... Jin shirun yayi yawa yasa Ahmad yin gyaran murya hade da cewa Amina bakidaina kukan ba koh?kinaso kitadamun hankali inkasa barci ko?girgiza kai tashigayi kamar yana ganinta cikin shagwaba tafara magana Dan Allah Ahmad kada ka nisanceni idan ka nisanceni bansan halin daxan shigaba bayan Kaine jigon rayuwata mijina farin cikina Wanda nake alfahari dashi akoda yaushe Dan Allah kayi hakuri abinda hajiya tayi maka kaji? Kada kidamu ya wuce xamu rinkayim waya amma baxanxo gidankuba kinji kuma kada kitambayeni dalili kiyi hakuri xan rinkajin muryarki"" toh kawai tace badan ranta yasoba... Sundan taba hira yana tambayarta lafiyar baby kafin sukayi sallama yakashe wayar ....bakaramin sanyi Amina taji a zuciyartaba koba komi yau zatayi bacci me dadi ******* Dasafe bayan Ahmad yayi shirin tafiya kasuwa Ahmad yakira Amina Dan su gaisa da fara,a ta dauki wayar suke magana da mijinta cikinso da kaunar juna suke musayar kalamai masu sanyaya rai kowa yana fadawa Dan uwansa yadda yayi missing dinsa a haka sukayi sallama ta manna mishi kiss a waya.....hajiyace tsaye a kofar dakin tana kallon ikon Allah lallai Amina batada zuciya wato dik abinda yaron nan ya shuka musu ita tana nan makale dashi to xatayi maganinta Koda Amina ta dago kai sukayi ido biyu da hajiya saida gabanta yafadi amma saita dake zuciyarta da murmushi dauke da fuskarta tace hajjaju ina kwana antashi lafiya? Hajiya bata amsaba ta karaso cikin dakin taxauna bakin gado sanan tace da ban kwanaba xaki ganni?yar kwal uba Mara kunya Mara zuciya dik abinda yaron nan yayi mana nadauka yadda yakyaleki kema xakibawa banza ajiyarsa Ashe kina manne dashi Ko meye yayi mana kece kike zubar mana da mutunci nadauka kin auro Dan arziki inda xamuji dadi Mu.huta Ashe gayyar tsiya kika auro kinxo gida wanka babu abinda ya amfana sai tsiya da babu to wallahi Amina kishiga hankalinki inba hakaba bakaramin saba miki zanyiba Mara zuciya kawai Haba hajiya waime Ahmad yayi mukune HK kawai DAGA WANKAN GIDA sai kuyitace mishi matsiyaci to ko damacan fa hajiya ba karfi Ahmad gareshiba Dan Allah kuyi hakuri akan dik abinda xaikawo komi xai wuce mana... Lallai Amina bakida kunya yanxun har munkai matsayin da xanfada kifada saboda mijinki sannu daddawa sarkin miji Aida tashi kikayi kika mareni sai insan kincika tabbatarciyar Mara kunya saboda mijinki kike fadamun magana lallai kin isa Kinyi aure kin haihu bari yan uwan naki suxo hajiya tamike ta fita tanata masifa... Zuciyar Amina ba karamin zafi take yi mata ba da kuna a dik lokacin da ake zagin mijinta bakaramin kunci da takaici takeyiba amma bakomi rayuwa CE tafashe da kuka itakadai a daki... ******* Ahmad da sassafe yake bude shago saboda yasamu yayi ciniki ya harhada abinda xaihada ya aika gidansu Amina dashi na suna yana xaune a shago shikadai babu abinda yake tunani sai halin da suka sunci Kansu shida matarsa Amina sunason kasancewa da juna suyi farin ciki da yarsu amma babu dama andauke maisu anhanashi ganinsu saboda tsabar masifa kai Allah ya wadaran wanan aladar WANKAN GIDA abinda ba musulunci yakawoshiba amma mutane sundage sundaukeshi sun rungumeshi gaskiya idan Amina tacigaba da zaman gida to yasan xai iya fadawa wani hali tunanin da Ahmad yaketayi kenan shi kadai a shago... ******** Anty saudat CE taxo gidan kasancewar kullum saisunxo itada anty Sahura gidan a cewarsu zaman jego suke xuwayi saboda hajiya batada karfin aiki sukeyin komi Suna xaune a daki hajiya na labartawa anty saudat yadda sukayi da Amina da safe tanafada mata tana daga murya ita tagaji da rashin kunyar Amina domin ba Wanda yakesata tayi musu sai Ahmad gashi tunda yaxo yakawo wadanan matsiyatan kayan bekara dawowa ba gashi yau shinkafar da xaa dafa ma babu batasan ya xaayiba To hajiya ai maganar shinkafa me saukice ai gab da xata haihu naje gidanta naga yasiyo buhun shinkafa ya ajiye sai aje a dauko kawai daganan abubuwan da bamu dashi dik a hado koya kikagani hajiyarmu? Hajiya ta washe baki tace hakan xaayi yanxun nan ma kitashi ki amshi makulli a hannunta anty saudat ta mike Tashiga dakin Amina da sallamarta tace sannu mejego yaya baby da faraarta take maganar Amina ta kakalo murmushin dole tace lafiya lau saboda dik abinda suke fada tanajinsu kasancewar dakin datake kusa yake Dana hajiya"""dama makullin gidanki xakibamu xamu dibo shinkafa saboda babu wadda xaa dafa yau gaban Amina saida ya fadi zuciyarta na harbawa ta mika hannu ta dauko jakarta dake gefen gado ta Ciro tabata ta juya ta fice ******* Anty saudat na isa gidan batasha wahalaba ta kwashe komi buhun shinkafa manja da mangyada hatta maggi saida ta kwashe batabar komi a kitchen din Amina ba har bed room dinta ta shiga ta bincike ta saci nasata Wanda itace xatayi amfani dashi ta boye sanan ta fito ta rufe gidan takamo hanyar GIDA..... Tana isowa GIDA dakin hajiya ta shisshiga da kayan cikin rada hajiya keyi mata magana yanxun saude abinda nakeso kiraba shinkafarnan biyu kikai shago a bamu kudi Wanda xamu boye Mu fita kunyar yan suna idan munga abinda yakawo baxai isaba tunda shi matsiyacine kullum babu koya kikace saudat tace hakan xaayi hajjaju Allah ya kara miki Nisan kwana bari in kai indawo inshiga mugaisa da baba hajiya ta tabe baki saidai gaisuwar amma babu abinda yake amfanawa sai zaman daki da karance karance waishi tsohon Dan boko saikin dawo kawai...... ******* Da yamma bayan Ahmad yadawo gida yana bude kofa yagane anshigo dakin saboda yadda ya tarar da dakin a birkice saida gabanshi yafadi shikenan barayi sunshigo sunyi musu sata to ta ina suka shigo bayan ya tarar da kofa a rufe tambayar da yakeyiwa kansa kenan ya wuce direct bed room yaganshi a birkice yafito yashiga kitchen yana shiga ya kalli inda suke ajiye kayan abinci wayam innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai yake maimaitawa barayi sunshigo sun kwashe kayan abincin daya tanada saboda lokacin da Amina xatadawo DAGA WANKAN GIDA shikenan sun takaitasu yadda kayan abinci ke tsada yayi tanadi anrusa yafito palor yaga kayan kallonsu na nan baasaceba abinda ya daure mishi kai kenan batayi su shigo sukasa daukar komi sai kayan abinci? Gabansane yafadi daya tuna cewa yan uwan Amina xasu iya xuwa suyi mishi wanan aika aikar amma idan sune kuwa wanan karon xai gwada musu bayida mutunci Dan basu suka siya mishiba tunda rashin hankalinsu har yakai suxo su kwashe mishi kayan abinci har gida amma bari yakira aminar yaji kafin ya yanke hukunci....ya danna kiran Amina... 08166177830 for comments _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃檰馃徑鈥嶁檧馃檰馃徑鈥嶁檧馃檰馃徑鈥嶁檧DAGA WANKAN GIDA馃檰馃徑鈥嶁檧馃檰馃徑鈥嶁檧* Written by Meenaslimzy Another page for u Maman Nana(Mommah)I Luv u soo much鉂� 3鈨�5鈨�-4鈨�0鈨� Kiran Ahmad ne ya shigo wayar Amina Wanda ya haddasa mata fargaba saboda tasan tabbas yaje yaga aika aikar da anty saudat tayi""""wayar tanata ringing dakyar ta saita natsuwarta tare da yin sallama"""Ahmad ko amsa sallamarta beyiba bakinsa har rawa yakeyi saboda tsananin bacin rai saboda yanaso ya tabbatarda hasashensa Amina waye yaxo ya kwashe kayan abincin Dana siya tunkafin ki haihu? Gabantane yayi mummunan faduwa saboda batayi zaton kayan abincin duka aka kwasheba tayi tunanin kwasowa sukayi lallai ta Shiga uku shikenan sun hadata da mijinta take fada a zuciyarta tambayar yakara jeho mata a karo na biyu yadawo da ita daga tunanin data fada. Bakinta na rawa tace Ahmad anty saudat CE taje gidan dibowa nibansancewa duka suka kwasoba kayi haku....bata karasaba cikin fada yace kifadawa anty saudat din tayi gaggawan dawowa da kayan abincin data dauka inba hakaba wlhy tallahi xan nuna muku bacin raina wlhy tallahi tunda rashin hankalin yayi yawa to wallahi baxan yardaba idan kuma Baku dawo dashiba to wallahi xan fanshe a abincin sunan da xankawo muku wallahi kinji na rantse saidai komeye xaifaru yafaru nagaji da rashin mutunci ya katse wayarsa bejira mexataceba..... Rushewa da matsanancin kuka tayi shikenan tashiga uku tasan cewa sun kure Ahmad ne yayi zuciya tunda a iya zamanta dashi betabayi mata haka ba kuka takeyi ba kakkautawa.... Kukan datakeyi ne hajiya nadakinta ta idar da sallahr magriba ta jiyo ta zabura ta shigo da sauri tanafadin Amina waya mutu kika cika mana gida da kuka? Wani Abu ne yaxo yatokarewa Amina kirji saboda bakin ciki dakyar ta bude baki tafara fada mata yadda sukayi da Ahmad din takara rushewa kuka Murmushi hajiya ta saki lallai Ahmad ya cika Mara mutunci saboda tsinanniya shinkafa da mangyada yake tada jijiyoyim wuya yakiraki ya tada miki da hankali to wlhy kome xaiyi ya Dade beyiba ya kaini kotu akan shinkafa tunda shi matsiyacine kome xaiyi yadade beyiba ke kuma tunda kinxama sallamammiya saikiyita kukan kinga tafiyata tafice a dakin tanata masifa....... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun take maimaitawa kamar an tsikareta ta zabura tayi dakin Mahaifin ta tana kuka ta zube a kasa tana fadin shikenan baba su hajiya xasu kashemun aure DAGA WANKAN GIDA nashiga uku baba kasa baki kaji kataimakamun takarashe maganar tana kuka me ban tausayi Lallashinta Mahaifin nata yashiga yi dakyar tayi shiru yace insha allahu aminatu babu abinda xaisamu aurenki kicigaba da hakuri in Allah ya yadda Ahmad baxai sakekiba kinji kicigaba da hakuri dik abinda yake faruwa inasane banida yadda xanyine saboda mahaifiyata CE kinji kici gaba da hakuri yayita lallashinta tashare hawayen tace nagode baba ta juya ta fita""""girgiza kai yakeyi cikeda tausayin Amina ******washe gari*** Allah Allah Ahmad yakeyi Safiya tayi yana gama shirinsa ya nufi gidansu ya Sanar da innah abinda ke faruwa yana xuwa gidan ya Tarar da mutane cike da gidan kasancewar gobe suna yan uwan babansa Dana mamansa sunxo haka yayita ratsa mutane suna gaisawa yashige kuryar dakin inna ya tarar da itada zainab kanwarsa suna lissafin abinda xaayi ya gaisheta ta amsa shima zainab ta gaisheshi ganin fuskarsa kamar da damuwa zainab ketambayarsa lafiyadai ko yaayaah Yasauke ajiyar xuciya yace ba lafiya nan ya kwashe dik abinda yafaru yafada musu da yadda sukayi da Amina yafada musu cikeda bacin rai kuma yayi rantsuwa akan haka Ahmad!!inna takira sunansa yadaga kai yakalleta batareda ya amsaba tace hukumcin daka dauka yayi daidai amma kada ka matsa sudawo dashi kaji kasiyi wata ka kara ka aika musu kawai kabarsu da rashin mutunci tunda basu gaji mutunciba Mu yan mutuncine inaso Mu.rabu lafiya kada ayi tashin hankali kaji yace to innah yanxun xanfita xandawo inkawo komi akai musu innah tace to a dawo lafiya ya five... ********* A kasuwa yadauki Aliyu suka shiga Dan kudin dake hannunsu.yayi musu siyayya na abinda xaaci a suna aliyune yace ya siyi shinkafa mudu goma goma haka kuwa akayi Ahmad dik ya sissiya ya amshi dinkunan me jego a cikin kasuwa daya bada dik yasa a mota ya nufi gidan innah Yana zuwa beshiga da kayanba yakira Zahra da sumayya yace suxo suje gidansu Amina ya aikesu ba musu sukabi bayanshi ko wacce sanye da hijabi yana fita ya tarar musu me napep ya loda kayan yace idan sunje yajirasu yadawo dasu ya juya ya shige motarsa yaja ya koma kasuwa..... ****** Amina CE xaune anyi mata lallen suna gidan cikeda mutane kasancewar yan uwansu na Zaria dik sunxo suna zuciyarta cikin fargaba take tunda tayi waya da Ahmad yanxun idan Ahmad bexoba ai tashiga uku da wanan tunanin taji sallamar sumayya suna gaisawa da yan tsakar gida hannunsu itada Zahra Niki Niki da kaya suka gama shigowa dashi suka gaisa sama sama Zahra ta mikawa Amina kayan fitar suna sukayi sallama suka wuce...suna fita hajiya da anty Sahura suka shigo da sauri suga me aka kawo.. Kan ubancan anty Sahura tace wanan shine abinda ya aiko dashi to wallahi tallahi xaisha mamaki shinkafa ko Rabin buhu batakaiba sanan mangyada Rabin galan saboda ya maidamu matsiyata da kayan miya da maggi ba drinks din da xaaba mutane ba ruwansha ballantana abun rabo shikenan dik xamuyi amma wallahi tallahi xaiyi mamaki kwayar shinkafa baxamuba yan uwansaba idan sukaxo takarashe maganar cike da fada Hajiya ta karbi zancen da kedai Amina baki Saar mijiba tir da matsiyaci Wanda beda komi sai tsiya bashiba ba yan uwansaba to yaje ya rike shine matsiyaci juya yayyinki sun aiko da kudi abubakar da yusuf kamar sunsan cewa matsiyacin baxaiyi komiba Allah ya wadaran halin ahmadu ta fice a dakin tana sababi Amina kukan zuci takeyi kawai ga kunyar yadda hajiya da anty Sahura suka yita zagin mijinta a gaban mutane itadau dadinda taji dik zagin da sukayiwa Ahmad Allah yasa su Zahra suntafi Dan tasan ba abinda xaihana sumayya bata kwashe tafada a gida ba xatayita addua Allah yasa kada sukashe mata aure DAGA WANKAN GIDa... ***** Ahmad na xaune a shago yanajiran kiran waya yaji ko xaayi korafi Dan ya tanadar musu rashin mutuncin da xaiyi musu amma shiru ba Wanda ya nemesa har gamma.. "*** Gidan innah kuwa zainab CE xaune take labartawa rabiah da wata kanwar innah wato mama jummai abinda yake faruwa nan take fada musu ita takosa suje suna Dan tadauki alkawarin dik Wanda ya takaleta a gidan sunan saita rama ko maganar banza saita mayar saita nuna musu tsantsan rashin kunya tunda basuda mutunci mama jummai ta amshe zancen da cewa na goyi bayanki zainabu dik abinda sukayi mana murama sai a dawo daidai tunda su dangin marasa mutunci ne rabiah ma tace haka xaayi da wanan shawarar suka mike suka cigaba da aikin suna RANAR SUNA 馃槏馃槏馃槏ina jiran comments dinku akan next page 08166177830 _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy Dis page is for u Amina Abdullahi radda (Meeniosky)my stubborn sister I love u Lodi lodi鉂� 4鈨�1鈨�-4鈨�5鈨� RANAN SUNA Da sassafe Ahmad ya tashi yaje ya dauki Aliyu a gidansa suka dauko rago wajen Wanda yabawa kudin...Aliyu ya wakilta yaje gidansu Amina da me pida a yanka musu ragon kuma ya fada musu an radawa yarinya sunan innarsa HAUWA,U... Ahmad ya daukosu Aliyu da me pida yasaukesu a kusa da gidansu Amina yaja motarsa ya wuce suna zuwa aliyune yayi sallama a kofar gidan umar ne ya amsa masa daga cikin dakinsa dake kofar GIDA ya leko suka gaisa Aliyu yayi masa bayanin daga inda suke Sanan umar ya shiga cikin GIDA yake Tarar da Amina yake fada mata ga abokin Ahmad nan da rago yakawo xaa yanka sanan Ahmad yace sunan yarinya HAUWA,U sunan mahaifiyarsa ne tace to shikenan wadanda suka kwana dakinta ne sukace Allah ya rayata ameen Bayan angama yanka rago Aliyu yasa me pida har cikin GIDA ya shiga da ragon daidai hajiya tafito wanka ta kalli ragon a wulakance ta shige dakinta......me pida ya ajiye musu Yakama Kansa... Su Anty Sahura ne xaune da yan uwansu sunata aikin abincin suna da xaaci ko kafin karfe sha dayan safe sun kammala dafa abincin da xaaci kowa ya shirya tsaf an fara gudanar da shagalin suna Dik abinan da akeyi Amina tana xaune a dakinta tasha ado cikin dinkakkiyar super Holland Ahmad ya dinka mata anyi mata dinkin zamani yayi mata kyau itama jaririya ansa mata kayanta me kyau tana rungume a jikin mamanta...Amina tunda garin Allah ya waye gabanta yake faduwa jikinta tana bata tabbas wani Abu xai faru amma ko menene Allah yasa ya zama alherine..... ****** A gidansu inna kuwa komi ana gudanar dashine cikin kwanciyar hankali da farin ciki yan uwa dik sunxo anata shagalin suna su Zahra da sumayya ansha dinki iri daya Dana yayyinsu rabiah da zainab sunfito sunyi Ras dasu anata ciye ciyen abinci da yan uwa... Innah na xaune cikin dakinta ta hada kayan barka da xaakai gidansu Amina da nasu da sukayi mata da Wanda dangi ke kawowa suna zaunene itada mama jummai a daki ta kalli mama jummai tace yakamata fa kuxo Ku shirya kutafi gidan sunan nan rana tayi kiyiwa wadanda xaku tafi magana dasu zainabu""tace to ta fita.... A dakinsu sumayya ta tarar dasu zainab tace suxo sutafi gidansu Amina domin rana tayi yakamata su wuce ba musu kowa ya mike tunda dama a shirye suke"""""mama jummai tasamu innah a daki ta dauki jakar kayan barka a kai tayi mata sallama suka tafi ******* Assalamu alaikum gafaranku dai mama jumai kecewa da suka isa gidansu Amina da faraa wadanda ke zazzaune a tsakar gidan suka amshesu sannunku da zuwa"""yawwa suka amsa suka nufi dakin Amina da fararsu suka shiga Ku xauna mana ga guri hajiya rukayya ta shimfida musu tabarma a tsakar dakin dik suka xauna aka sake gaisawa mama jummai ta dauki jaririya takarayiwa Amina barka Hajiyace da su saudat da Sahura a daki sunajin yan gidansu Ahmad sunxo amma sukaki fitowa saida hajiya rukayya tashiga tace musu suxo mana ga baki anyi"""a wurinki suke baki inji hajiya wadanan har bakin arzikine da xakixo ki ishi mutane kije gamunan zuwa hajiya rukayya ta juya cikeda bacin rai bataji dadin abinda hajiya ta fada ba amma bakomi ko meye tanayine Dan Amina take yi.... Su zainab dai zama suka cigaba dayi suna xaune bayan minti goma da shigowar hajiya rukayya sanan anty Sahura ta shigo dakin tana yatsina fuska dakyar ta bude baki tace sannunku ta mike ta fita ...sudai kallo suka bita dashi.... Saudat CE rike da plate daya na shinkafa Sahura rike da plate din shinkafa suka shigo dakin suka ajiye a wulakance suka dibo pure water suka ajiye musu ga abinci nan sukace Zainab CE ta zabura tace bakuga wai Mu shida bane harda kanwar innah xaku kawo mana plate biyu na abinci saboda tsabar iskanci.....zuciyarta a hassale ta fada saboda tsabar bakin ciki..... Dariya saudat tayi abincin da yayanku yakawo muka Baku ba Wanda Mu muka hadaba kinsan yayan nakune kullum cikin babu saboda tsiya Kada kikaracewa yayana matsiyaci idan ba hakaba zan shayar dake mamaki yanxun nan wallahi Rabiah ta amshe zancen da cewa ai tsiya a gidanku takare tunda gashi munxo bakuyi mana tarbar mutunciba saita rashin mutunci saboda gadonsa kukayi muko bamu gaji rashin mutunci ba daga dangin uwa ko har uba wallahi..... Anty Sahura ranta ya baci cikin huci take cewa to waye yayi gadon rashin mutunci?karaff Zahra dake gefe tace Ku bata karasaba anty saudat ta sharara mata mari bata sauke hannuntaba zainab itama ta kai mata mari tana huci akan me xaki mari kanwata Dan tafadi gaskiya...... Hajiya rukayya ta mike tace haba Sahura meye haka kikeyi wadanan mutanenfa arziki ya kawo su ba tsiyaba saboda haka kada insakeji.... Hayaniyace ta fito da hajiya daga dakinta ta nufo dakin Amina tana shigowa a gigice tagansu tsaye carko carko lafiya naganku tsaye haka? Anty Sahura tace wanan yar iskarce ta mari saudat saboda ance yayansu matsiyacine...iyyeee to karya akayi ai tsiya ta tattara takarewa Ahmad wlhy kuma tunda ya nuna shi matsiyacine a haka zaikare hajiya tafada mama jummai ta Mike tace; Bantaba ganin tsohuwar banzaba kamarki ai nayi tunanin cewa dakikaxo xaki musu fada Ashe karawa xakiyi akan abinda sukayi lallai yanxun mukaga inda wadanan yara sukayi gadon rashin mutunci mudai Allah yasa kada jikarmu ta gado rashin mutunci dik da uwarta mutuniyar arzikice amma rashin mutunci jini yakebi tunda wadanan suka biyoki ta nuna Sahura da saudat da yatsa.. Kada ki kuskura ki kara nunani da Dan yatsa wlhy inji saudat....idan na nuna dukana xakiyi karamar Mara kunya?.... Sannu babbar Mara kunya inji Sahura zuciya ta dibi zainab ta dauki plate din shikafa ta watsawa saudat a jiki saboda dik tafi bata haushi tafi kowa rashin mutunci...... Aiko Sahura ta kaiwa zainab duka bata ankaraba aikowa rabiah dake gefe ta cukumota sukafara dambe tana dukanta kamar Allah ya aikota saudat tashigarwa Sahura nan fada ya kacame hajiya na gefe tana fadin niban haifi ragwayeba kuyiwa dangin matsiyata duka..... Aiko mama jummai tayi kukan kura ta ingije zainab da rabiah tashiga dukan Sahura da saudat abinka da karfin kauye dukansu take yi suna ihu mutanen GIDA suka cika daki wata yar uwarsu hajiya tayi kan mama jummai da duka aiko ta daddage ta sakar mata nushi a baki sai jini takoma gefe a guje.... Zainab da gangan ta rugo da gudo xatayo kan wadda aka nusa aiko cikin Saar kudirinta ta ingije hajiya tafadi kasa warwas kwankwasonta ya bugu a kasa hajiya ta saki yar kara saigata warwas a kasa ta dafe kasa ga zugi daya ziyarci hajiya hajiya a kwankwasonta mikewa tayi kokarin yi ta shige daki ta turo kofa tunkafin a ji mata ciwo.... Itadai hajiya rukayya bakin ciki ya hanata cewa komi domin tasan kome yafaru hajiyace da jikokinta ne sukaja ba Wanda ke bata tausayi sai Amina dake faman rusa kuka tana fadin tashiga uku Dan Allah kudaina Daga windon daki hajiya ta leko da kai tana cewa gayyan na ayya kuxo Ku fitar mana a GIDA Ku kyalemun jikokina kuma wallahi ni sainasa Mahaifin Amina yakira matsiyacin danku ya sakarmun jikata tunda har gida kukaxo kuka rufe jikokina da duka.... Rabiah CE tace kifito mana wlhy da saina rufe idona nayi kasa kasa dake tunda kin yadda girmanki tsohuwar banza kawai Mara mutunci... Mama jummai ta karba basaikince a sakar miki jikaba xaa saka ni sainasa Ahmad ya saki Amina indai ya haifu ta zari gyalenta tace kuxo mutafi kubar musu gidansu matsiyata kawai.....su zainab suka take musu baya""Sahura da saudat yashe a kasa anbarsu a kwance da duka da suka sha da kyar suka mike suna fadin wallahi kin gama zama da Ahmad...tunda sukayi mana rashin mutunci...suka wuce dakin hajiya Sauri sauri suke tafiya mama jummai sai sababi takeyi tanafadin muje gidan a kira ahmadun nixan zayyana mishi dik abinda yafaru hajiya rukayya CE biye dasu tana basu hakuri ko sauraronta basuyiba suka shige napep... Sumayyace tace mama jummai munbaro musu kayan da mukatafi dashi rabiah tace ai Amina muka kaiwa basuba sujecan da tsiyarsu...a HK suka iso gidan sunata masifa da hayaniya suka shiga gida innah ta fito da sauri tana tambayar meyafaru mama jummai tace meye ma baayiba Ahmad ya auro tsiya nan ta kwashe komi tafadawa innah Hankalin innah ba karamin tashi yayiba lallai dole Ahmad yasan yadda xaiyi da wanan jarababbun mutane dole a kawo karshen masifar nan Kodai ya amsota takoma gidanta ko kuma yasakar musu yarsu *Allah ya baki lfy ingantacciya yasa anyi aikinan a saa kutayamu addua anyiwa antyna aiki yau da safe anty sahurata* _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy *Sakon gaisuwa gareku nagode da kaunarku a gareni,momyn ciyama,unaisalv,Maryam mai Riga,Maryam &zainab from dandalin bilkisu bilyamin and bilkisu tinja from ZBI* 4鈨�6鈨�-5鈨�0鈨� Ahmad na xaune tunanin duniya yakeyi kala kala akan halin dayake ciki wayarsace tafara kara yana dubawa da Sauri yaga innah CE ke kiransa da tsakar ranan nan gabansane yafadi tabbas wani Abu yafaru koma meye Allah yasa alherine dauka yayi ya kara a kunnensa yayi sallama daga can bangaren inna ta amsa kafin yayi magana tace ahmadu dik inda kake kaxo Gida yanxun nan inason ganinka yace to innah ganinan ta kashe wayar gabansane ya cigaba da faduwa babu abinda yake ambatawa sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun a haka ya rufe shagon ya nufi gidan innah..... Yana isa gidan uwar dakinta ya shige ya xauna bakin gado ya Tarar dasu duka da yan uwansa da mama jummai a dakin suka Dan gaisa sama sama sannan ya dubi innah yace gani innah Allah yasa dai lafiya.... Ba lafiya Ahmad abinda inna tafada kenan saida gabansa yafadi zuciyarsa ta tsananta harbawa....sanan ta kwashe dik abinda yafaru dataji a wajen su mama jummai tafadawa Ahmad sanan ta Dora da cewa Ahmad ka auro dangin marasa mutunci wadanda basu gaji arzikiba to tun wuri na yanke shawara akanka Ahmad.....""""gaban Ahmad ya tsananta faduwa shikenan yasan cewa xaayi ya rabu da Amina shikenan besan yadda xaiyi da sontaba zuface ta cigaba da tsattsafowa Ahmad dakyar ya bude baki yace inajinki innah cikin dasasshiyar murya.... Inna ta cigaba da cewa Ahmad gobe nakeso kaje gidansu Amina kabawa iyayenta zabi cikin biyu kodai subaka Amina kataho da ita Ku wuce GIDA idan yaso sumayya taje ta tayata jegon a can ko kuma ka sakar musu yarsu ai ba itakadai bace ya' umarnine wanan nabaka ba shawaraba kaji na fada maka koh?"""hankali tashe Ahmad yace toh'katashi katafi na sallameka inajiranka gobe....ya mike jiki a sanyaye ya fita yan uwansa sun matukar tausayawa yayan nasu ganin halin dayake ciki saidai sukansu sunsan wanan itace maslaha ko saboda fitinannun yan uwan matarsa"".... ******** Amina ko xaki mutu sai Ahmad ya sakeki kingama zama da Ahmad yan uwansa suxo har GIDA Suci mana mutunci a bainar jamaa banda tsiya da suke tafe dashi kiyi tunanin xaki cigaba da xama da Ahmad to wlhy kinyi kadan indainina haifi suleman ubanki to wlhy dole yasa Ahmad yasakeki kinji nafada miki shashasha ke ko haushin abinda akayi mana bakijiba sai kuka kikeyi saboda ankori kannen ubanki sannu baure sarkin kuka aiko xaki kukan jini kingama zama da Ahmad saidai idan kinyarda muyafeki kuma insa suleman ya miki baki..... Hajiya dik batakai hakaba inji Anty saudat kiyi hakuri hajiya ki kwantar da hankalinki ai yadda sukaci mana mutunci hardake aka ture kika fadi a kasa to sunjawa Dan uwansu yaxo kawai yabamu takaddarta idan an yaye yarinya yaxo ya karbeta yakaiwa yan uwanshi marasa mutunci..... Kuka kawai Amina keyi takasa magana muryarta harta dishe dik wani mai imani a lokacin ya kalli Amina saiya tausaya mata dik ta fita hayyacinta lokaci kankani karamar yarinya tashiga mawuyacin hali babu abinda yafi daga mata hankali irin Kalmar mama jummai da hajiya kakarta akan cewa dole Ahmad yasaketa tashiga uku tayaya xatafara rayuwa babu Ahmad?waye xaixo ya aureta idan Ahmad yasaketa dik Wanda yaji cewa DAGA WANKAN GIDA Ahmad yasaketa bawanda xai aureta shikenan a haka rayuwarta zatakare a cikin kunci da bacin rai shikenan hajiya da yan uwanta sun cuceta sundau hanyar yi mata sanadin aure DAGA WANKAN GIDA....takara rushewa da kuka me ban tausayi da tsuma zuciya yau da mahaifiyarta na nan dataji sanyi a ranta data lallasheta da kalamai masu kwantar da zuciya haka Amina ta cigaba da rusa kuka suko sunfice sunbarta nan itada hajiya rukayya... Itakanta hajiya rukayya tana cikin rudani takasa cewa ko kalma daya sai girgiza kai kawai takeyi tana kallon yadda marainiyar Allah take zubarda hawaye gwanin tausayi ita kanta tasan bakaramun kuncin rayuwa Amina xata shigaba indai tarasa aurenta domin wanan auren shine babban jigo ga yarinyar dakyar ta bude baki tacewa Amina kiyi hakuri komi mukaddarine daga Allah kuma dik abinda yasamu bawa dama Allah ya tsara mishi hakan rubutaccene a wajen ubangijinsa kiyita addua Allah ya zaba miki abinda yafi zama alheri.... ****** Ahmad ne kwance yayi rigingine yana kallon silin din dakinsa tunanin Amina kawai yakeyi tausayinta Dana maraicinsa shiyafi damunsa da irin yadda take sonshi da biyayyar datakeyi mishi anya xai samu macen dayakeso kamar Amina?anya xai iya jure rashin amina? Idan ya rabu da Amina wani hali xata shiga?waye xai kula mishi da tarbiyyar yarsa a matsayinsa na uba?tambayoyin dayakeyiwa kansa kenan ya rasa amsoshinsa...gashi yanxun mahaifiyarsa tayi fushi harta Dora mishi doka da umarni a yadda yakejin mahaifiyarsa a ransa baxai iya tsallake umarninta ba saboda ita kadai tarage mishi dolene yayi abinda ta umarceshi koda hakan na nufin mutuwarsa....amma ya Amina xatayi?tambayar da yayiwa kansa kenan hawaye na zarya a idanunsa... ***** Bangaren Amina itama tana cikin tashin hankali bacci ya kauracewa idanunta kuka kawai takeyi saboda tarigada tasawa ranta Ahmad yasaketa yagama Dan kalaman da hajiya kefada to tabbas dole idan yaxo tasashi yasaketa shikenan tafaru takare sunyi mata sanadiyyar aure sun maidata cikakkiyar marainiya ga maraicin uwa gana miji dama Ahmad shine yaxame mata mijin marainiya to gashi sunaso suyi sanadin auren DAGA WANKAN GIDA....zuciyarta takarye tasan cewa batada Wanda xaiyi mata gata sai Allah....a haka bacci yasaceta ******* Da safe Ahmad jiki ba kwari yatashi yayita shirye shiryensa har karfe Tara ya shirya yafito yashiga mota saida ta tsaya a wani babban shago yasiyawa jaririya pampers yasiyawa Amina kayan tea sanan ya nufi gidansu Amina dik jiki babu kwari... Yanayin parking motarsa yafito yakulle ya dibo abinda yasiya musu sanan yashiga gidan da sallamarsa ya Tarar dasu anty Sahura a tsakar GIDA suna gyara naman da xaa soya na suna ya gaishesu ciki ciki suka amsa ya wuce su ya shiga dakin Amina yayi sallama idanunta ya rufe ya kura mata ido dik ta rame ta fita hayyacinta tausayinta ya kara rufeshi...a hankali ta bude idonta tasaukeshi a kansa Dan muryarsa dataji ta dauka mafarki takeyi murmushin karfin hali yayi mata sanan ya xauna yadauki jaririya ya rungume itakuma ta gaisheshi cikeda ladabi ya amsa.... Be gama amsa gaisuwartaba hajiya ta shigo dakin ta tsaya tace ina Fatan da takkaddar jikata kaxo Dan tagama zama dakai tagama zama da dangin matsiyata dole kabata takkada na fada maka ahmadu... Hajiya niba CeCe kuce yakawoniba sanan dik abinda kikefada na kyaleki darajar Amina kikeci saboda wani yanacin arzikin wani dama dole danaxo dolene takiraki saboda naxone incika umarnin mahaifiyata.....yana fadin haka kirjin Amina ya tsananta da bugawa shikenan ta shiga uku Ahmad yaxone yasaketa""""ya cigaba da cewa naxone infada muku umarni biyu ta bani dolene incike guda daya kodai kubani amina Mu wuce gidanmu ko kuma insaketa inji mahaifiyata ya karashe maganan zuciyarsa nayi masa zafi abinda kuka yanke kufada mun inje infada mata gobe insha allahu xandawo da sakamakon abinda kukacedin.... Amina tafashe da kuka me ban tausayi sosai take kukan...hajiya tace au kuka kikeyi Dan uwarsa tace yasakeki aiba saitace yasakekiba dole yasakeki Dan baxakibishi kutafiba idan kika bishi wallahi sainasa suleman ya tsine miki kuma babuke babushi.... Kuka Amina takara rushewa dashi shikenan tata taxo karshe.. Inajiran comment dinku akan wanan page din馃お馃お馃お馃お _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy Meelah adeel is such an angel DAT I respect and I will always cherished her in my heart ILUSM馃槝馃槝馃槏馃槏 5鈨�1鈨�-5鈨�5鈨� Wanan kukan da kikeyi baxai fissheki ba Amina saboda muyi magana naxo gidan nan banazo bane kitasani a gaba kinayimun kuka ba Ahmad yafada cikeda tausayawa..... Hajiyace ta anshe zancen da baxatayi maganarba kai inda Da kanada kunya ma baxakaxo gidan nan kana wata maganar ta bika ba abinda marasa kunyan kannenka sukayi mana marasa mutunci wadanda basu gaji mutunci ba wlhy jiran zuwanka nakeyi dama ka rubuta takaddar jikata kabamu.... Kalaman hajiya suka kara tunzura Ahmad zuciyarsa zafi takeyi masa besan lokacinda yace idan igiyar sakin a hannunki take saiki saketa tunda dik kawaicin da nakeyi miki a matsayinki na sirikata tunda babu mahaifiyarta bakya gani saikin kureni nayi miki rashin kunya to wlhy nadaina kawaicin kici abinda xakiyi Ahmad yafada cikin fushi da daga murya....anty Sahura CE tashigo dakin a guje daga gyaran naman datakeyi tace lallai Ahmad hajiyar kake fadawa haka saboda bakada kunya bakada mutunci? Nafada mata Sahura kuyi abinda xakuyi kun kaini karshe kuma tunda kun nuna sakinta kukeso inyi baxan saketaba kukaini kotu ina jiran sammaci... Ya juya ya kalli Amina yadda hawaye keyin ambaliya a fuskarta ya kalleta cikeda kunci yace kiyi shawara xuwa gobe xanxo indaukeki kibar musu gidansu mujecan idan kinga xaki Bini idan kuma baxakibiniba xanxo inkarbi yata inbadata inda xaa kula da ita saboda kisani wallahi tallahi daga gobe idan nazo baxan kara zuwa gidan nan ba da sunan wajenki harabada kinji nafada miki.... Girgiza kai Amina takeyi tabafadin Ahmad kada kayimun haka dame zanji da bakin cikin danake ciki kokuwa da fushin da kakeyi sokakeyi in wulakanta kowa ya juyamin baya saboda mahaifiyata Allah yayi mata rasuwa?kalamanta bakaramin karyawa Ahmad zuciya yayiba anya yayiwa amina adalci a rayuwa idan yayi haka?saidai bashida zabi dole yayi haka saboda umarnin mahaifiyarsa ne baxai iya tsallakewa ba kikewa yayi da niyyar tafiya ya kalli Amina yace idan kinga xaki Bini kishirya kayanki gobe da safe xanxo mutafi kinji? Ina zakatafi da ita ahmadu?ko kallon hajiya beyiba ballantana yabata ansa ya ratsa ta gefensu ya wuce abinsa...lallai Ahmad bashida mutunci hajiya Cewar anty Sahura yan uwansa sunxo sunyi mana rashin mutunci kiduba yadda wanan girman kauyen ta hadamu da saudat tayi mana duka kema kanwarsa bata dubi tsufankiba ta ingijeki kikafadi inda da tsautsayi da yanxun ta karyaki shine yanxun shima yaxo yakara akan Wanda sukayi hajiya wlhy Amina ba xata bishiba xamugani idan xata zabeshine akanmu to bismillah.. Hajiya tace kece ma kike bata bakinki ai ba inda Amina xata Allah ya kaimu goben ai suleman yana gidan nan xanga yadda Ahmad Mara kunya xai tasa Amina yace sutafi ...ke kuma xamu gani idan kina kaunarmu idan baki kaunarmu Mara kunya kawai... Suka juya suka fice a dakin...Amina ta runtse idanuwanta hawaye masu zafi sunabin kuncinta yanxun tasan tana cikin tsaka me wuya ya xatayi ta tafi tarabu da danginta komi rashin mutunci su tana kaunarsu saboda sune ita sanan mahaifinta yanada rai haka zata tsallake kenan tabbarsu?meyasa Ahmad xaiyi mata haka?meyasa baxaiyi hakuriba ai komi yayi farko xaiyi karshe"""wata zucuyarce ta tuna mata da cewa idan ta kuskura ta rabu da Ahmad SBD danginta ba xata kara samun miji me hakurinsa ba baxata karasamun dangin mijin da suke kaunartaba inda wasune ma baxasu bashi wanan zabinba saidai Susa yasaketa....innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine kawai take furtawa tana kuka me tsuma zuciya ***** Ahmad be xame ko ina ba sai gidan mahaifiyarsa domin yasanar da ita yadda sukayi a gidansu Amina..da shigarsa ya gaisa da yan uwansu wadanda sukaxo suna ya wuce dakin innah ya tarar da itakadaice a dakin ya gode Allah da mama jummai bata ciki Dan tafi kowa daukar zafi kuma itake tunzura innah....ya xauna gefen gado suka gaisa cikeda kulawa sanan yayi jimmm kadan yace innah daga gidansu Amina nake...ya kwashe dik abinda sukayi a gidan yafadawa innarsa da inda ya tsaya ma Amina akan tayi shawara gobe xaikoma.. Innah tace meyasa baka sakar musu yarsuba Ahmad nema kakeyi mutanen nan sucigaba dayi mana rashin mutunci koh Ahmad nema kakeyi watarana su kira sunana su zageni ko Ahmad karabu musu da yarsu Dan Allah Ahmad kada kaja abinda watarana xaaxo a haifi da Mara ido.... Innah Dan Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki halin da Amina ke ciki idan kikaganta saikin tausaya mata sanan abinda na duba shine idan nasaketa xasu cigaba da gallaza mata da wulakantata innah Amina mutuniyar kirkice a zamana da ita bata tabayimun abinda ya batamun raiba hakurarriya CE innah kuma kunsani Dan Allah innah kiyi hakuri saboda Allah da darajar Mahaifin yarinyar beyi mana komiba bashida yadda zaiyine saboda wanan fitinanniyar tsohuwar"""innah tayi shiru ba tace komiba..... Ganin haka Ahmad ya sauko ya tsugunna a gabanta yace innah Dan Allah kijanye maganar insaketa innah kinji saboda abinda sukeso kenan dama nikuma baxanyi abinda sukesoba innah nabata zabi kota biyoni ko indauki yata inbarota baxan saketaba kuma inkara aure innah.... Ajiyar zuciya innah tayi tadagashi daga tsugunon da yayi a gabanta tace shikenan Ahmad na janye nasan kai me biyayyane a gareni nima kuma dolene inso farin cikinka lallai kin sakin Amina ba karamin jihadi kayiba Allah ya daukaka ka sakamakon yin hakan dakayi xan xaunar da yan uwanka inyi musu bayani insha allahu kaji Allah ya kaimu goben""yace ameen innah bari inkarasa kasuwa innah tace baxakasha kunuba ka karya yace nasha tea a GIDA tace to shikenan Allah ya tsare yace ameen ya fita... Innah ta Tara yan uwansa ta fada musu komi yadda sukayi da Ahmad akan Amina suma sunyi naam da shawarar saboda suna kaunar Matan yayan nasu ***** Daddare bayan Ahmad yadawo gida yayi shirin kwanciya zuciyarsa sai hasko mishi fuskar matarsa takeyi lokacinda take kuka nan da nan yaji hankalinsa yatashi baxai iya bacciba batare dajin muryartaba hannunsa ya mika gefen gado ya dauki wayarsa ya danno kiranta.... Tana kwance taji wayarta na ringin ta dauko taga sunan Ahmad kirjinta ya shiga harbawa sauri da Sauri dakyar ta saita natsuwarta tadauka tare dayin sallama.. Tabangarensa ya amsa sanan yace bakiyi barciba?tace ehh ikram CE keshan nono(sunan da take kiran jaririyar dashi kenan)yace ki lallasheta mana tace ai tayi shiru sanan yakara cewa dama nakirakine inji muryarki tayi murmushi me sauti hade da jin dadin maganarsa sanan yayi mata saida safe yakashe wayar Ajiyar zuciya ko wannensu yayi sbd Kaunar junansu da sukeyi saigashi xaarabasu ta karfin tsiya Wanda hakan xai jefasu a cikin mawiyacin hali yadda suke kaunar juna.... ***** Washe gari tunda Amina ta tashi take kuka saboda batasan yadda zatayiba tabi mijinta kota xauna da danginta tashiga tsaka me wuya gashi tunjiya su hajiya ke zaginta suna mata gori..saboda zuwan Ahmad washe gari yasa anty Sahura da anty saudat suka nemi izinin mazajensu da xasu kara kwana saboda xaayi meeting suka shirya musu karya sukuma suka yadda... Ahmad kuwa yanatashi yayi wanka yadafa ruwan zafi yasha tea sanan ya shirya yadauki makullin motarsa ya rufe gidan yakamo hanyar gidansu Amina kamar yadda yafada musu xai dawo..... Yana isa gidan da sallamarsa ya shiga bakowa tsakar gidan ya wuce dakin da Amina take tana xaune a bakin gado tana shirya ikram ya xauna shima yadan kalleta ta gefen ido yaga yadda ta rame fuskar nan tayi Haske sai hanci...gaisheshi tayi ya amsa cikeda kulawa ..kafin yace wani Abu su hajiya sun dira a cikin dakin suma ya gaishesu ba wadda ta amsa hajiya CE tace kaxomin da takaddarta ko kuwa yace banzo da itaba batare da kallon inda takeba... Juyawa yayi inda Amina take xaune jikinta sai rawa takeyi dik ta tsorata ya kalleta suka hada ido hawaye nabin idonta ya runtse idanuwansa SBD bayason ganinta a haka yace mata Amina meye shawarar da kika yanke zakibini? *Manage this plss banida lfy* _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy 5鈨�6鈨�-6鈨�0鈨� Kuka sosai Amina ta sanyawa Ahmad ganin ya kafeta da idanuwansa yana tambayarta xata bishi ita gaskiya tsakaninta da Allah baxata iya binsaba a matsayinsa na mijinta takoma rayuwa dashi shikadai da dangin mijiba komi lalacewar danginta sune ita komi Daren dadewa tasan cewa xasu shiryu kuma xasu gane gaskiya.. Tana cikin wanan tunanin ne ta tsinkayi muryar hajiya na cewa Amina ba kuka xakiyiba zabi yarage gareki idan kinzabi binsa ya rage gareki kisani idan kinzabi binsa babumu babu ke kuma wallahi tallahi dik abinda ya biyo bayanki nan gaba ki kuka da kanki kuma kada ki nememu saboda wallahi babu wata alaka da xata biyo baya tsakaninmu dake matukar kika bishi sanan matukar kika tsallake umarnin iyayenki to wallahi baxaki taba ganin da kyau ba nan gaba Kalmar baxakiga da kyau ba itace ta harzuka Ahmad zuciyarsa ta hau tafarfasa wato Dan Amina xata bishi ne akeyi mata mugun bakin baxataga da kyauba? Besan lokacinda ya waigo ya kalli hajiya cikeda bacin rai yace idan kece kikesawa aga da kyau din saiki hanata gani da kyau... Zabura Amina tayi ta kalli Ahmad dake yiwa hajiya rashin kunya a gaskiya baxata bari ya wulakanta mata iyayeba komi lalacewarsu koba komi hajiya a matsayin mahaifiyarta take yanxun tunda babu mahaifiyarta aiko darajar tsufanta ya raga mata koba komi tsakaninta dashi ballantana a matsayin sirikinta yake.... Ta kalleshi cikeda bacin rai tace Ahmad gaskiya baxan so ka wulakantamun iyayeba dik son da nakeyi maka kuwa hajiya a matsayin mahaifiyata take be kyautu ka fada mata magana hakaba don ranka ya baci idan rai ya baci kada hankali ya gushe komi rashin kyautawar da akayi maka kuwa baxanji dadiba ka toxartata a gabana... Mamakine ya kashe Ahmad a zaune irin kalaman da Amina kefada masa akan iyayenta wato shine yakejin tausayinta yasa yabijirewa umarnin mahaifiyarsa amma shi yanxun bataga rashin kyautawar da akayi masaba lallai Amina tabashi mamaki.. Zuciyarsa cikeda bacin rai ya kalli Amina baxaki biniba kenan?..ta kallesa tace gaskiya baxan bikaba Ahmad inguji iyayena ba komi lalacewarsu .....cikeda mamaki ya kalli Amina saboda dik a tunaninsa xata bishi..wato dik kukan datakeyi yanajin tausayinta yana ganin kamar tana sonshine Ashe na muna funcine?Ashe baxata iya tsallake umarnin yan uwantaba saboda kada bakinsu ya kamata saishine ya bijirewa tasa uwa?idanuwansa ya kafeta dashi yanayi mata kallon mamaki.. Alhamdulillah hajiya kefadi lallai Amina kin haifu kincika yar halak dik a tunaninmu xakibishine Mu ki gujemu to da gaba Kinyi kuka da idanunki da danasani Mara amfani saboda namiji ba abin yadda bane dik yadda kika kaiga sonshi watarana sai ya juya miki baya... Jiki a sanyaye Ahmad ya mike ya zura takalmansa zuciyarsa na harbawa sauri da sauri ko a mafarki tunaninsa be taba bashi Amina xatayi mishi hakaba amma besan dalilinta nayin hakan ba?amma tunda ta zabi zama da iyayenta to dole shima ya cika umarnin mahaifiyarsa ya sauwake mata ya nemi wata yar ya aura dik da yasan cewa baxai taba iya daina son Amina ba harabada...ya juya xai tafi hajiya tace meye matsayin jikata? Tsayawa yayi batare da ya juyo ya kalli Amina ba yace na saki Amina saki daya.... Dib dakin yayi kamar anyi ruwa andauke juyawa yayi yatafi abinsa baiko waigo ya kallesuba .... Kuka me karfi Amina tasaki shikenan tafaru takare aurenta ya mutu DAGA WANKAN GIDA har ga Allah baxata iya gudun yan uwanta saboda mijiba saboda bakaramin sakaci xatayiba....kuka takeyi numfashinta na sauka a hankali sama sama duhune tafara gani a idanunta take dakin ya gauraye bata ganin komi kara me karfi ta fasa ta sulale a kasa babu numfashi.... Da gudu su hajiya sukayo kanta suna girgizata amma ba alamar numfashi a tare da ita bakaramin tsorata sukayiba saudat CE ta ruga a guje dakin babansu tana ihun yaxo Amina xata mutu...cikin bacin rai ya kalleta yace kije Ku karasata kawai ai dik halin data fada kune sanadi kuma idan ta mutu kun huta hankalinku ya kwanta kun zuge hajiya kunyi sanadiyyar aurenta Ku kuna naku gidan mijin ko waccenku tasa ido tagani itama yadda xata kasance dukanku...niba abinda xanyi muku yanxun tunda saida ta baci kuke nemana aiba amfani gareniba kije kawai kuyi mata abinda xakuyi... A guje saudat ta juya tayi hanyar waje tana kiran umar ta nufi kofarsa turus tayi ganin kofarsa a rufe tasan yatafi kasuwa A guje ta ruga bakin titi ta kira mai napep sukaxo aka kama Amina aka shigar da ita suka nufi Asibiti babu alamar numfashi.. **** Ahmad dakyar yake tuka motarsa saboda halin dayake ciki idanuwansa babu abinda sukeyi sai hawaye dayake xuba ga wani Abu dayaxo ya tokare masa kirji saboda bakin ciki ikon Allah ne kawai yakai Ahmad gidan innah Da sallama ya shiga bakowa saboda dik yan suna sun watse sumayya da Zahra kuma suntafi makaranta dakyar yake taka kafafuwansa ga kansa da yayi masa nauyi yana Sara masa yana shiga dakin innah ya zube a kasa yana kuka mai tsuma zuciya idanunsa sunyi jajir kamar garwashin wuta cikeda tashin hankali innah ketambayarsa lafiya ahmadu?meyafaru ina aminar? Dakyar ya bude bakinsa hawaye na bakin ciki suna zuba yace na saki Amina saki daya innah... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun innah ke maimaitawa tana kallon Ahmad Wanda tunda takedashi bata taba ganinsa yana kuka HK ba tabbas tasan cewa bakaramin tashin hankali yake cikiba rabuwa da iyali babu dadi balle Amina dayake matukar kauna ..meyayi zafi haka Ahmad harkasaki amina?mai yafaru ka saketa Ahmad?ka manta Kaine kake tausayinta ka rokeni akan injanye maganar sakin nan na janye meya janyo maka kasaketa? Ahmad ya kasa magana kansa kawai ya rike dayake Sara masa kamar xai rabe biyu...innah hankalinta bakaramin tashi yayiba ganin Ahmad a wanan halin hannu ta mika inda pilo yake ta dauko ta ajiye mishi tace yadan kwanta ba musu yayi yadda tace ya runtse idanunsa.. ******* Tun a hanya anty saudat ke tunanin idan sunje Asibiti ya xasuyi da kudin da xaa bukata na dubata Dana magani?Dan dole a bukaci kudi kuma su bawani kudine a hannun Suba Dan dik an kwashe anyi hidimar suna dashi...gashi Ahmad ya saki Amina ya xaayi su tunkareshi da xancen kudin magani?kallon Amina takarayi dake kwance a cinyarta babu alamar numfashi ga ikhram nata tsala kuka..a HK suka iso Asibiti.. Inajiran comments dinku..sanan kucigaba da bina Dan jin ya xata kasance domin yanxun ne xaa fara wasan馃お _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy 6鈨�1鈨�-6鈨�5鈨� Da Sauri nurses suka amshi Amina akayi cikin ward da ita wani likitane kwararre a fannin mata ya shiga inda aka shigarda Amina nan da nan ya hau gwaje gwaje aka bata taimakon gaggawa dakyar yasamu ta farfado sanan aka gwada mata BP akaga tanada hawan jini sosai..allurar bacci yayi mata saboda dole sai ya rubuto magungunan da xaaba ya daura mata drip nanda nan bacci ya dauketa yafito hannunsa dauke da files ya nufi office dinsa a guje Sahura da saudat suka bishi sukabar hajiya xaune a reception suna shiga ya xauna yana rubuce rubuce dakin yayi shiru sai karan fanka saudat CE takasa hakuri ta dubeshi tace likita mekedamunta yadago kai yace tana tare da matsananciyar damuwa Wanda ya haddasa mata hawan jini....a gigice saudat ta maimaita hawan jini likita yace ehh hawan jini....innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai take maimaitawa lallai Amina tana cikin wani hali nanda nan idanunta suka kawo hawaye batasan lokacinda hawaye suke zuba a kumatuntaba nanda nan taji tausayin kanwarta ya shigeta ya rinya karama takamu da hawan jini yanxun idan Amina ta mutu sunyi mata adalci kenan?tana cikin wanan tunanim taji muryar likita na miko musu takadda ga magungunan da muke bukata yanxun asiyo kafin ta farka sanan a taho mata da abinci Dan xata bukata....a sanyaye anty saudat takarba ta juya itada anty Sahura suka nufi inda hajiya take.... A reception suka Tarar da ita tana xaune tanaganinsu tace yayadai ta farfado ko?anty Sahura ta yatsina fuska tace hajiya kinji wai hawan jini gareta ga magungunan da aka rubutanan xaa siyo.......hajiya tace ninasan Amina idan bata janyo mana balai ba akan wanan tsinannen yaran hankalinta baxai kwantaba tana Neman mutuwa akansa Shiba ta ita yakeyiba yanxun ya kuke ganin xaayi.....anty saudat wadda jikinta yayi sanyi tace inada wasu kudi Dana kulle bari inruga insiyo mata magani......tabe baki anty Sahura tayi takalli saudat da dik ta tada hankalinta tace ke kuma meye na tada hankalinki ai ita tasawa kanta idan ta mutu ta huta ita tasani.....insha allahu ma baxata mutuba inji anty saudat ta gyra goyon ikram daketa faman bacci a bayanta tayi Sauri ta bar wajen tabarsunan xaune... ****** Ahmad zazzabine me zafi ya rufeshi a dakin innah a HK su Zahra sukadawo makaranta suka tarar dashi dik hankalin innah a tashe yake ta aiki Zahra ta siyo maganin zazzabi ta tasheshi tabashi dakyar ya karba yasha zuciyarsa babu abinda take tuna masa sai abinda yafaru a gidansu Amina shikenan yanxun yarasa abar sonsa matarsa masoyiyarsa wadda yake matukar kauna yau itace ta juya masa baya a sanadiyyar yan uwanta wasu zafafan hawaye ne suka ziyarci kumatunsa innah ta kura masa idanu tana kallonsa cikeda tausayawa dakyar ta mike ta xubo abinci ta bashi cokali uku kawai yaci ya ajiye ta kwanta nan da nan bacci ya daukesa... ******* Su hajiya na xaune sunajiran saudat nurse tafito tace sushiga ta farfado amma kada adameta da surutu saboda halin datake ciki da Sauri suka shige suna bude kofar suka ganta a kwance idanuwanta suna kallon silin hawaye NATA zuba a idanuwanta kamar anbude fanfo dik ta rame idanunta sunyi jajir sun kunbura....hajiyace tace sannu Amina yawwa ta iya CE musu ta fashe da kuka tana kallonsu cikeda kunci jitakeyi kamar ta rufesu da kuka koxataji saukin radadin datakeji a zuciyarta sunyi mata sanadin aurenta DAGA WANKAN GIDA aurenta ya mutu Ahmad yasaketa uban yarta farin cikinta wanan rana tana dagacikin ranakun da baxata mance dasuba a rayuwarta harabada....takara rushewa da kuka Hajiyace ta fusata da irin kukan da Amina take yi saboda bakaramin haushi takebataba a fusace tace ke Amina dik akan ahmadu kike wanan kukan keda xakiyi murna kiyi farin ciki kin rabu da jaraba Dan Ahmad auren sa babu abinda ya haifar mana sai jaraba da tsiya Allah na gode maka daya sakeki muka huta wulakantattun mutane... Anty Sahura tace kedan kinrabu da Ahmad har wani abun bakin ciki ne keda xakiyi murna ki kwantar da hankalinki kitsaya Allah yakawo miki Dan arziki ki aura ba dangin tsiyaba... Kalamansu bakaramin zafi sukeyiwa amina a zuciyartaba ta runtse idanunta hawaye masu zafi suna zuba.....turo kofar akayi da sallama dik suka waiga anty saudat CE ta shigo hannunta rikeda ledar magani ta ajiye da take away a hanunta ta kalli Amina lokaci daya taji zuciyarta ta karye babu Wanda xaiganta a HK beji tausayintaba inhar yanada imani dakyar ta kalli Amina tayi mata sannu ta amsa ta bude take away din ta mika mata tace ci wanan kafin inkira nurse suxo subaki magani ta ansa takai cokali bakinta jitayi kmr tana tauna magani ta ajiye gefe takara fashewa da kuka hajiya tace kinga tafiyata baxaki cikamun kunne ba anty sahura tace nima binki xanyi suka fice suka turo mata kofa kuka sosai take yi me taba zuciya Nurses biyune suka shigo dakin da saudat biyedasu suka bata maganin tasha sanan daya DAGA cikinsu tacewa saudat kiyi kokari kibata abincin taci saboda maganin datasha suka fice suka turo kofar Lallabata sosai anty saudat tayi tabata abinci taci Rabi sanan takalli anty saudat tace taya xanfara rayuwa yanxun shikenan nakara zama marainiya ta rushe da kuka me tsuma zuciya anty saudat ta rungumeta itama tasa kuka lokaci daya taji tausayin yar uwarta ya kamata itama kukan tasa tana rungume da Amina Anya sunyi mata adalci kuwa?su suna xaune da mazajensu lfy amma ita sunyi mata sabadiyyar aurenta yar kanwarsu daya kamata sujida ita shine sukayi mata sanadin aurenta zuface take tsattsafo mata hade da hawaye daya wanke mata fuska nan da nan taji danasanin abubuwan data aikata tausayin kanwarta yakamata dolene ta nemi yafiyar Amina tunkafin hakkinta yakamasu itadai xata hada kai da yar kanwarta su xauna lfy dolene ta nemawa Amina far in ciki a rayuwa koda xata rasa komi dikda tasan bakaramar wuya Amina xatashaba zaman da xasuyi da hajiya tayi nisa cikin tunani ta dago kai takalli Amina taga tayi bacci ta kwantar da kanta a filo ta koma gefe ta xauna a kujera Wata duniyar tunanin takuma fadawa yanxun idan akafada musu kudin gado da kudin sallama ya xasuyi itaba kudi garetaba hawaye ya wanke mata fuska shikenan yanxun ne lokacin da xasu wulakanta saboda inda da auren Amina dole Ahmad ne xaiyi komi yanxun kuwa dolene dik inda kudi yake su Nemo Wata zuciyarce tace kodai takira Ahmad ne tafada masa halin da suke ciki tabashi hakuri dikda ba lallai bane yasauraresu amma xata gwada kiransa tagani da Sauri ta dauki wayar Amina ta kira Ahmad.. **** Kirane ya shiga wayar Ahmad tanata bacci sumayya ne da innah kexaune a dakin sumayya Tamika hannu tadauko wayar taga number aminace da Sauri tacewa inna number aminace innah ranta ya baci wato sunkirane suyi mishi wani rainin wayon kome tadauka takara a kunnenta tace wayene saudat jin innah CE tadauka saida gabanta ya fadi dakyar tace saudat CE yayar Amina.... Innah tace wato kunkirane kuci masa mutunci Wanda kukayi mishi be ishekuba jarababbu marasa mutunci Allah nagode maka da Dana ya sakar muku yarku matsiyata Wanda basu gaji mutunciba kuma indainice na haifi Ahmad babushi babu yarku harabada yagama zama da ita bata jira me xaaceba takatse wayar zuciyarta nayi mata zafi Kuka saudat ta fashe dashi shikenan sun shiga uku dolene taje tafadawa hajiya yadda sukayi da mahaifiyar Ahmad kallon Amina tayi cikeda tausayawa taga tanata bacci sanan ta juya ta fita ta rufe mata kofa Xaune ta tarardasu ta xauna jiki a sanyaye tafara fada musu takira Ahmad ga yadda sukayi da innah bude bakin hajiya sai cewa tayi Allah ya kara ubanwa yace ki kira wanan matsiyacin da garada suka rabu da Amina kowa ya huta waike saudatu mekedamunki?tunda abun nan yafaru naga jikinki yayi sanyi uwar iyayi Anty sahurace tace hajiya kyaleta iyayine kawai kuma baki isa kixubar mana da mutunciba ke ga me tausayi to wlhy itama aminar koxata mutu tabar Ahmad kenan hajiya ta CE kwarai kuwa.... Kuka sosai Anty saudat keyi saboda zafin magan ganun da suka fada mata insha allahu komi runtsi taci alwashin Amina saita koma dakinta komi dadewa ta bude kofar da Amina keciki ta nemi guri ta zauna ta sakko ikram a bayanta dataketa bacci ta kurawa yarinyar ido tana kallonta cikeda tausayawa Kuyi hakuri manage this Faty Dan Maliki CE tadaukemun hankali da surutu馃槣 _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy 6鈨�6鈨�-7鈨�0鈨� Bayan farkawar Amina ne anty saudat ke shaida mata xata nema musu sallama sutafi gida SBD basuda enough din kudin da idan ta kwana xaa cajesu sanan bugu da kari babu Wanda xai kwana da ita a Asibiti....Amina tace badamuwa Anty saudat ta fita tasamu likita ya rubuta musu sallama da sharadin kada a rinka tada matada hankali sanan ta daure ta rinkashan magani anty saudat tace badamuwa data fitone take shaidawasu anty Sahura dake xaune a reception an sallamesu yanxun xasu wuce gida anty Sahura ta tabe baki tace ko baasallamemuba nidama tafiyata xanyi tunda banice nayi mata sanadin ciwon ba taji dashi ni gidama xan wuce daganan......itadai anty saudat ba tace komiba ta juya tashige ta tarar Amina ta shirya takamota suka fito hajiya da sahura Na biye dasu a gida napep daya saudat ta tarar musu itada hajiya da Amina sahura tayi musu sallama ta nufi gidanta.... ******* Ahmad ne xaune gaban inna bayan ya farka take sanar mishida yadda sukayi da yayar Amina xuciyarsa CE ta harzuka yace innah lallai ma mutanen nan to mexanyi musu da suka kirawoni kuma?inna tace ato kaima kafada abinda xangaya maka shine koda wasa banyarda kaje gidansu Amina ba idan kaje gidan ban yafe makaba Ahmad kayi hakuri ka maida hankalinka ga kasuwancinka sanan banaso kadade baka nemi wani auren kayiba kodan wulakancin da sukayi maka kaji nafada maka koh?yace insha allahu innah tace kuma gobe ka tattaro kayanka kadawo dakinka dake gida kuma katurawa amina sako suxo su kwashe kayansu yace to innah bari inje gida yamma tayi insha allahu xankwaso daganan sai in wuce kasuwa tace to shikenan Allah yayi maka albarka yace ameeen Daddare Amina Na xaune a daki dik tunanin Ahmad yahanata sukuni TeX ya shigo wayarta da Sauri ta bude ganin sunan Ahmad jikinta har rawa yakeyi ta karanta nan da nan takarance abinda yace hawaye masu zafine suka fara zarya a kumatunta nikewa tayi a hankali take tafiya saboda rashin kwarin jikinta tashiga dakin hajiya ta sanar mata da cewa Ahmad yace suxo su kwashe kaya SBD dama yanxun ne xai biya kudin gidan to tunda HK yafaru su kwashe kawai hajiya tace kyale matsiyaci xamu kwashe da safe xankira sahura ta nemo dilallai suje a saida kayan tunda bamuda wajen ajewa toh kawai Amina ta iya cewa ta juya ta shige dakinta cikeda kunci..... ****** Washe gari da safe hajiya ta kira sahura ta shaida mata a saida kayan Amina SBD Ahmad yace yasaki dakin su kwashe kayansu da murnarta tacewa hajiya idan ansaida kayan ya xaayi da kudin?Hajiya tace ki ajiye a wajen ki har xuwa lokacinda xatasamu wani mijin cikin tsananin farin ciki ta kashe wayar a fili sahura tace Allah ya kashe ya bani inaxaune nasamu kudi a sama mikewa tayi ta zari hijabi sai wajen dilallai tadaukesu suka wuce gidan Amina Koda sukaje subtarar Ahmad ya kwashe komi nashi kofar dakinma a bude yabari saboda yasan xasuxo kwashe kaya tunda ya anshe mukullin wajen Amina tun lokacinda suka kwashe kayan abinci dayaje ya amsa... Ba bata lokaci akayi cinikin kaya sahura tasaida kaya tas ko gidan hajiya batajeba ta wuce gidanta da kudi cikeda murna ******* Bayan sati uku A haka rayuwa takasancewa Amina yau fari gobe tsumma yan kudaden datasamu dik takarar dasu wajen cefane da siyawa yarinya pampers komi itakeyiwa kanta babu mai taimaka mata mahaifintama tsakaninta dashi sai gaisuwa SBD ya juya mata baya umar ne yakedan bata kudi idan yadawo kasuwa hajiya ko ba ruwanta da ita ko yarta ta bata dauka idan sallah takeyi ko ta shiga bayi HK ikhram xatayita kuka har saita fito ta dauketa ****** Ikhram tayi wayau sosai kama takeyi da ubanta kamar ba yar wata biyuba tana xaune ta tasa ikhram a gaba jikinta yayi zafi zazzabi takeyi batada kudin kaita Asibiti tarasa yadda xatayi saita tuna ai akwai kudin kayanta a wajen sahura bari takira ta tambayeta tabata wani Abu tasamu takai ikhram Asibiti da Sauri ta dauki wayarta ta danna kiran anty sahura Saida wayar takusa tsinkewa sanan tadauka ta gaisheta tana amsawa dakyar Amina tace dama anty cikin kudinane nakeso idan xansamu ko dubu biyu ne xankai ikhram Asibiti....bata karasa maganaba anty sahura ta daka mata tsawa wani kudine naki a wajena naci miki bashine ban biyakiba?baki na rawa Amina tace kudin kayan dakina.....dariya ta fashewa Amina dashi tace Na ranta kuma bandasu yanxun SBD HK kidama mata paracetamol kibata...bata jira me xataceba ta kashe wayarta.... Rushewa Amina tayi da kuka tana cewa tashiga uku.wayyo Allah rayuwa yanxun yaxatayi da ikhram ga jikinta yayi zafi.....Ahmad ne yafado mata a rai tace xata kirashi tafada mishi yarshi ba lfy yaxo ya kaita Asibiti Number Ahmad ta danna takira cikin saa ta shiga lokacin yana xaune shida Aliyu a shago yaga bakuwar number da kamar baxai daukaba ya dauka....yace waye Amina gabanta yafadi wato Ahmad yayi deleting din number ta kuka me karfine yaxo mata ta danne tasaita kanta tace Ahmad ikhram CE batada lfy shine nace bari infada maka... Ahmad yace kifadawa yan uwanki mana daba matsiyataba sukaita kada ki kuskura ki kara kirana a waya idan kika kuma dik abinda nayi miki ke kika siya.... Ahmad yarkacefa batada lfy Ahmad yace yanxun kukasan yatace da bukatar kudi ta taso muku kunkirani Ku cuceni Toni baxanxoba SBD mahaifiyata tace idan nasake xuwa gidanku bata yafeba SBD HK kada kikara kirana a waya... Dib taji ya tsinke wayar kuka sosai tafashe dashi tana rungume da ikram da jikinta yayi zafi sosai Shiko Ahmad yana katse wayar ya kalli Aliyu yace wai meyasa mutane basuda kunya ne?Aliyu yayi dariya yace meyafaru abokina...Ahmad yace Amina CE takirani wai ikhram batada lfy dariya sosai Aliyu yayi yace tun yanxun hartafara laushi?ai tukunna ma badai WANKAN gida ba ga abinda ya janyo mata nan sanan yacewa Ahmad abokina yakamata ka nemi yar budurwa ka aura wadda xata fanshe maka takaici Ahmad yadanyi tsaki yace ni ina naga wata budurwa saidai ka nemomin Aliyu ya sheke da dariya yace akwai Khadija yar makotanmu ka nemeta yarinyace me tarbiyya nasan xakasota bari xanyi mata magana yau daddare idan nakoma fatana kada kabani kunya Ahmad yace bakomi xanyi aure kodan Amina da iyayenta in kunsa mata takaici kuma yanxun tafara wahala...nan suka cigaba da tattaunawa ***** Paracetamol Amina tadama tabawa ikhram ikom Allah zazzabin ya sauka saitayi bacci ta kwantar da ita ta mike ta nufi kitchen Dan ta kwaso sauran abincin jiya datayi tana budewa taga wayam bakomi a tukunyar A sanyaye ta nufi dakin hajiya tace Dan Allah hajiya idan kinada naira hamsin kidan bani da Sauri hajiya ta waigo tace Wanda ubanki yabani?kajimun Mara kunyar yarinya Sana'a nakeyi da xanbaki kudi?ki bacemun daga gani tunkafin in bata miki rai A sanyaye Amina ta juya ta shige dakinta tana xaune a bakin gado babanta ya bude labule yashigo ya mika mata naira Dari SBD dik yadda sukayi da Hajiya yana jinsu....hawayene yafara zuba a idanunta data amshi kudin jikinta a sanyaye tasa hijabi ta fice Dan nemo abinda xataci kafin ikhram ta tashi..... ******* Da yamma ne bayan Ahmad yadawo daga kasuwa suna xaune dukansu a daki hardasu sumayya yakefadawa innah Amina takirasa wai ikhram batada lfy ya kwashe dik yadda sukayi da ita yafada mata.....tace kayimun daidai ahmadu kuma koda wasa kaje gidan banyafe ba Sanan Ahmad kefada mata shawarar da Aliyu yabashi akan yarinyar unguwarsu innah taji dadin zancen tace Allah ya tabbatar mana da alheri dukansu sukace amin ***** Washe gari jikin ikhram yayi zafi numfarfashi kawai takeyi Amina tarasa yadda xatayi Dan ko Sisi bata tashi dashiba Wanda xatakai ikhram asibiti tasata tayi ta zuba mata ido tana kuka zuciyarta nayi mata kunar halin data shiga tana rungume da ita tana faman kuka Kamar daga sama tajiyo muryar anty saudat tana sallama a tsakar gida....shesshekar kukan Amina taji ta shigo dakin da Sauri taganta rungume da ikhram tana famar kuka da Sauri ta karbi yarinyar tana tambayar ko lfy?zafi sosai taji jikinta kmr wuta da Sauri ta cewa Amina muje Asibiti kinji Amina tace cikin kuka anty saudat banida ko Sisi tace sa hijabi muje Allah xai kyauta....da Sauri Amina tasa hijabi suka fice gidan da Sauri suka nufi Asibiti Suna isa Asibiti ba bata lokaci sukayi bangaren yara nan da nan aka amshi ikhram akafara mata taimakon gaggawa allurar zazzabi akayi mata akabasu gado a bangaren yara bacci me nauyi ikhram keyi tana kwance nurse ta shigo ta mika musu takaddar kudin da xasu biya tunda Asibiti kudi sukaje... Turkashi yanxun ya xaayi da wanan kudin wlhy kudin anty saudat ta cewa Amina dubu goma suka cajemu....zabura Amina tayi ta mike tace wlhy anty ko Sisi bantashi dashiba.... Tabdijan anty saudat tace sanan ta cewa Amina ki kira sahura cikin kudin kayanki tabada wani abu... Kuka Amina ta fashe dashi ta kwashe yadda sukayi da sahura ta fada mata..... Ajiyar zuciya saudat tayi sanan tace bari inje gida su Ahmad infada musu halin da ake ciki....Amina takalleta tana hawaye tace kada kije baxasu saurarekiba SBD nakirashi jiya be saurareniba...ta rushe da kuka Anty saudat tace kobaxasu saurareniba xanje komenene suyimun Amina Mu ceci rayuwar jaririyar nan dake kwance batasan komiba bata jira me Amina xataceba ta bude kofa ta fice...gidansu Ahmad ta nufa cikeda fargabar abinda xata tarar..... ***** Innah CE xaune a falo dash sumayya da Zahra sunacin abinci zainab da rabiah ma sunxo wuni gida sunata hira ana raha cikin farin ciki...sallama sukaji suka amsa dukansu a tare sunajiran suga waye tana bude labulen zumbur zainab ta mike tana nuna ta da Dan yatsa meyakawoki gidanmu dangin tsiya? Muje zuwa kubini Dan jin yadda xata kasance..... _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy Wanan page din nakine *Momyn* *sauban* nagode sosai da kaunarki a gareni ina sonki irin sosai din nan馃槏鉂� 7鈨�1鈨�-7鈨�5鈨� Innah ta kalli zainab tace wacece wanan kike CE mata dangin matsiyata zainab?.....da Sauri zainab tacewa innah saudatu CE fa damukayi tsiya da ita ranan suna innah aikinsanta kuwa....saudat Na nan a tsaye tana kallonsu dik jikinta a sanyaye....innah CE ta kalleta tace shigo kinji?zainab tace innah ta shigo fa kikace?innah tace zainab ta shigo bamusan meke tafe da itaba...innah ta kalleta tace shigo mana... A sanyaye anty saudat ta shiga dik sukabita da kallo ta xauna sannan ina tace meke tafe da ke?cikin sanyin murya tace dama ikhram CE batada lfy yanxun HK suna Asibiti anbata gado to.Amina takira Ahmad tafada mishi be saurareta ba shine nace bari inxo ko xansameshi anan in sanar dashi....inna tace meyasami ikhram din?saudat tace zazzabine me tsanani.....innah tace bari in kira Ahmad din be kyautaba ai yakamata ya saurareta tunda yarshice koba komi.akwai hakkinta akanshi....rabiah dake gefe tace gaskiya ne innah Innah takira wayar Ahmad bugu daya yadauka tace Ahmad yanxun yayar Amina taxo.ikhram.batada lfy ance ankiraka baka sauraresuba yace ehh innah gaskiya ban saurareta ba....innah tace yarkace fa akwai hakkinta akanka a matsayinka Na uba dik inda kake kaje Asibiti kasamesu ayi abinda yadace yace to innah xanje da yamma yanxun ina kasuwa tace kayi kokaridai kaje yace shikenan sukayi sallama ta kashe wayar sanan ta kalli saudat tace Yanxun kije asibitin anjima xaixo yasameku insha allahu dik abinda ake bukata xaiyi....a sanyaye ta mike xata tafi rabiah tace tsaya inbaki sako kibawa aminan Jakarta ta bude ta Ciro dubu daya tace gashi kibata asiyi pampers Allah ya bata lfy anty saudat tace ameen... Sauri sauri anty saudat keyi saboda kada Amina taji shiru tana isowa tashiga da sallama Gaban Amina saida ya fadi saboda tana tunanin baxasu saurareta ba....kallo tabi anty saudat dashi tanajiran bayani....murmushi me ciwo anty saudat tayi sanan ta kwashe dik yadda sukayi ta fada mata....hawayene Na farin ciki tafarayi Na murnar xaabiya kudin asibiti....muryar anty saudat taji tana cewa ga wanan Amina tamaxa ta juyo taga dubu dayace anty saudat ta miko mata tabita da kallon mamaki anty saudat tace kanwar Ahmad CE rabiah tace asiyawa ikhram pampers..... Allah sarki kannen mijinta suna kaunarta sanan dama babu wadda sukafi shiri kamar rabiah saboda hakurarriyace...kudin ta amsa tace anty xauna ki huta bari in fita insiyo pampers din insiyo mana abinci muciko anty saudat tace toh Amina ta mike ta fice ******* Karfe shida Ahmad yafara haramar rufe shago aliyune ya shigo rumfar yake CE mishi yakamata muje kaga yarinyar nan fa abokina...Ahmad ya juyo ya kalli Aliyu yace ba yau ba saboda yanxun Asibiti xanje saboda ikhram batada lfy an kwantar xasu....Aliyu yace akan me xakaje ka manta wulakancin da mutanen nan sukayi maka?Ahmad yace ehh xanjene saboda akwai hakkin ikhram akaina yakamata insauke saboda yata xanje.....Aliyu yace to.Allah ya sauwake Ahmad yace ameeen ya juya yatafi shima yakarasa rufe shagonsa... ****** Karfe shida da Rabi Ahmad ya shigo Asibiti besan inda xaibiba dolene saiyakira Amina wayarsa yadauka ya shiga kiranta suna xauna itada anty saudat waya ta shigo da sauri tadauka ganin me kiran ta danna amsawa tambayarta inda suke yayi tace ward din yara ya katse wayar Baafi minti ukuba ya shigo ward din dakin farko yayi sallama SBD yana xaton anan suke...yana budewa suka hada ido da Amina gabantane yafadi ganin yadda Ahmad yayi yar kiba ya canja ta kura mishi ido....dauke kansa yayi yakaraso gefen gadon sannunku kawai ya iya cewa ya duka yana kallon ikhram daketa bacci....Anty saudat tace ina wuni Ahmad ...ko kallonta beyiba ya dago kai yacewa Amina ina takaddar da aka Baku?taciro a jaka ta mika mishi ya fice... Kallon juna sukayi da anty saudat SBD basuyi tunanin Ahmad xaiyi musu HK ba...Amina tasan kowaye akayiwa abinda akawa Ahmad dolene yayi fushi sanan tasan hankalinsa kwance yake tunda taga har kiba Ahmad yayi.....murmushin takaici tayi Turo kofar akayi da sallama dukansu suka amsa anty Sahura CE da hajiya suka shigo....anty Sahura sai yatsina baki takeyi Ku HK akeyi kunxo Asibiti ko Ku kira mutane kuce ga halin da kuke ciki?...dukansu ba Wanda ya kalleta daga Amina har saudat...hajiyace tace Ku kuramene?kafin wani yace wani Abu anturo kofar da sallama... Ahmad ne ya shigo wanan karon da ledoji a hannunsa yashigo be kalli kowaba ya dire ledojin sanan ya mikawa Amina takaddar biyan kudi dakyar yace Allah ya sauwake ya juya ya fice beko kallesuba...... Hajiya tace lallai Amina bakida zuciya yanxun Ahmad kika kira yaxo saboda ke kwadayayya CE ko?baxaki daina bibiyarsaba koh? Kafin Amina tace wani Abu anty saudat da ranta ya baci ta kalli hajiya tace to hajiya waye uban yar?waye xaiyi hidimar inbashiba Dan yayiwa yarsa hidima sai yaxama kwadayi ai akwai hakkin ikhram akansa tafada a fusace..... Hajiya tace rashin kunya xakiyimun kenan saudatu lallai kin isa to bani kikayiwaba ubanki suleman kikayiwa.....anty saudat da ranta yagama baci ta mike ta saba gyalenta ta kalli hajiya tace badai ubanaba tana fadan HK ta fice fuuuuuuuuhhhhh a dakin bako sallama ta rufo kofa Saudatu ai dakin tsaya kin nunamin ke cikakkiyar Mara kunyace kuma xanfadawa ubanki idan nakoma gida hajiya nata masifa ta kalli Amina tace ke kuma komi nacinki baxaki koma gidan Ahmad ba Anty Sahura tace yi hakuri hajjaju mutafi gaisuwa mukaxo taxama tsiya aka miki rashin kunya ai xuwan badole bane muyiwa yar addua a gida baxaki kuma xuwaba ballantana a miki rashin kunya taja hannun hajiya muje muhau napep asaukeki a gida nima in wuce ...Amina kalli tabisu dashi suka fice...hawaye tafarayi ta janyo ledojin da Ahmad ya kawo musu tafara dubawa Madara da Milo ne Na manyan gwangwani sai suga da Lipton dayar ledar kuma lemo ne dash ayaba danginsu fruit...ta ajiye ta bude dayar ledar magunguna ne sai kudi dubu biyu daya saka...murmushi takeyi kawai tana hawayen bakin ciki... ****** Ahmad kuwa yana fitowa Asibiti ya shiga mota yakira number Aliyu yace nagama da wuri kana ina ne xanxo muje wajen yarinyar nan...Aliyu yasaki shewa yace saikaxo mutumina.... _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy Wanan paging nakine antyna *BILKISU BILYAMIN* marubuciyar KASAITATTUN MATA hakika naji dadin kulawarki a gareni Allah yabar zumunci da kauna鉂ゐ煒� 7鈨�6鈨�-8鈨�0鈨� Isowar Ahmad layinsu Aliyu yayi daidai da fitowarsa daga gida,parking motarsa yayi yafito sukasha hannu Aliyu cikin faraa yace"mutumina Ashe xakashigo dai da gaske dama nafito kofar gidane injiraka...murmushi kawai Ahmad yayi yace"muje,suka Dan miko saman Layin a daidai wani kofar gida suka tsaya..almajirai dake gefe Aliyu yakira yatura su cikin gidan suce ana sallama da Khadija... Ba musu almajirin ya shiga gidan..Jim Kadan yafito yace"wai gatanan xuwa mungode koh?ya wuce....bayan minti Biyar Suna tsaye ta fito sanye da hijabi Medan tsawo sallama tayi musu suka amsa aliyune yafara magana da cewa"hajiya Khadija barka da dare?murmushi kawai tayi kanta a kasa tana wasa da yatsunta cikin hijabi...aliyune yace"" abokina ne yazo Neman yardarki da amincewarki kuma ya nemi soyayyarki idan kin amince Ku fahimci juna shi aurenki yakesonyi idan babu wani dayarigamu....dik surutun dayakeyi shidai Ahmad kallonsu kawai yakeyi bece komiba domin gsky tunda Khadija tafito shidai batayi masaba dikda tanada natsuwa da hankali kodaga yanayin daya ganta amma yasan Amina dabance... Aliyu ne ya juyo ya kalli Ahmad adanjin haushin shirun da yayi tunda sukaxo bece komiba yace"malam kabarni inata surutu nine xanyi maka zance?Ahmad murmushi yayi kawai sanan yace"itama gimbiyar batace komiba sai a sannan ne Khadija ta dago suka hada ido ta kara dukar da kanta dakyar ta bude baki tace"bakomi nagode zanshiga gida insha allahu xanyi shawara da mahaifiyata zanfada muku yadda mukayi idan kunsake dawowa.. Aliyu yace"to malama Khadija saida safe,ta shige gida suka juyo suka nufo inda Ahmad yayi parking aliyune yace"gsky ahmad bakayiba muje wajen yarinya kaki magana kabarni inata magana kamar ninajewa kaina?yatsina fuska Ahmad yayi lokacinda sukazo wajen motarsa yace"gaskiya Aliyu batamunba amma zanyi tunani saida safe...Ahmad ya bude motarsa ya tada bejira me Aliyu zaiceba ya ja motarsa yabarshinan tsaye da mamakin Ahmad ****** Gida Ahmad ya isa ko cikin gidan beshigaba dakinsa ya bude dake zauren gidan ya shiga ya rage kayan jikinsa yasa jallabiya yakoma gefen katifa ya zauna...babu abinda idanunsa ke hasko masa sai yadda ya tarar da Amina a Asibiti dik ta lalace ta rame tayi baki saboda wahala yaji tausayinta matuka shiyasama yakasa ko bari su hada idanu saboda yana matukar tausayinta dikda abinda yan uwanta sukayi mishi..... ****** A wajen Amina itama hkn takasance,saboda babu Wanda take tunani sai Ahmad yadda taga yayi kyau yayi kiba shaidar hankalinsa kwance babu wata damuwa a tattare dashi wata wutar sonshi CE take ruruwa a zuciyarta amma ko kallo bata isheshiba tasan tana cikin wahala domin harabada tasan Ahmad yagama zama da ita hawaye ne masu zafi kebin kumatunta... Duba takai inda ikhram ke kwance tanata bacci ta taba jikinta taji babu zazzabin shaidar tafarajin sauki kenan gefen gadon ta raba ta kwanta ta rungume ikhram jikinta saitaji kamar Ahmad ta rungume jikinta hawayene suka cigaba dabin kumatunta.... ****** Washe gari Ahmad natashi yashige cikin gida dakin innah ya shige direct yanemi gefen gado ya zauna innah tana zaune a kan dadduma tanashan kunu da kosai suka gaisa inna tace"Ahmad jiya bakaxo kafadamun ya akayi a asibitinba da jikin ta kwarar tawa,murmushi Ahmad yayi yace"innah wlhy nagajine Dana dawo daki nashiga Na kwanta naje asibitin nan ya kwashe dik yadda sukayi yabata labari da yadda ya tarar da Amina Bakaramin tausayinsu innah tajiba ta gyara zama tace"Ahmad gsky mutanen nan sun cutarda Amina hakika Allah xaisaka mata tunda marainiya CE abinda nakeso dakai shine ka rinka xuwa kana ganin yarka kana sauke hakkinta SBD akan HK sai Allah ya kamaka nayi tunani akan abinda nace kada kasake zuwa ganinsu Na janye dama fushine yasa nace haka idan kasamu abinda zaka kaimusu kaje kayi sallama kofar gidan ta fito kabata kaji?toh Ahmad yace... Sanan idan kayi wanka kafin kashiga kasuwa kabiya asibitin kaga yadda suka kwana idan sunada bukatar wani Abu kayi musu tunda yanxun alhamdulillah kanasamun kudi toka kyautatawa yarka sai Allah yabaka kaima kaji?sosai kalaman innah sukabawa Ahmad mamaki Dan beyi tunanin zata sauko daga fushin datayiba dikda yasan mahaifiyarsa tanada hakuri da kawaici...."shikenan innah zanyi yadda kikace bari inje inyi wanka intafi..."Allah yayi albarka Ahmad.."ameen innah Ahmad ya fice a dakin.. ****** Wajen karfe goma nasafe Amina naxaune rungume da ikhram tanabata nono aka turo kofar dago kai tayi taga waye...da mamakinta Ahmad ne yashigo da sallamarsa yasha blue din shadda yayi kyau sosai kasa amsa sallamarsa tayi sai kallonsa datakeyi a hankali yataso ya duka saitin ikhram dakeshan nono yashafa kanta yaji kaunar yarsa Na shiga zuciyarsa dago kai yayi yana kallon Amina yadda take rungume da ita saiyaga tayi mishi kyau yadda ta rungume yar yabashi shaawa.... Kallon kallo sukeyi shine yakawar da kansa yace"ya me jiki?""da sauki kawai race "Allah ya kara sauki...tace"ameen Wata farar kujera dake gefe ya gyara ya zauna sanan ya Ciro wayarsa a aljuhunsa yafara dannawa itakuwa mamakin Ahmad takeyi dik a tunaninta tafiya zaiyi kamar jiya saitaga ya zauna yana daddana waya... Tanagama ba ikhram nono ta mika mishi ita ba musu ya karbeta itakuma ta juya gefe ta zauna..... Ahmad kuwa dik tunaninsa zaa samu Wanda zai zaunada Amina sukwana tare a taimaka mata da tashi saboda yarinyar amma saibega alamun wani yatayasu kwanaba ido ya zubawa ikhram yana kallonta babu inda tabarshi kamarsu daya hasken fatane ta dauko Na Amina kaunar yarsa nakara shiga ransa...agogon hannunsa ya kalla 11:10 nasafe yakamata ya wuce kasuwa mikewa yayi ya mika mata yar sanan yace" kinada bukatar wani Abu ne?girgiza kai tayi kawai ya juya yace"saina kara dawowa ya fice.. Hawayene yafara gangarowa Amina a fuska tabishi da kallo Wanda batasan dalilinsaba Ya fita badadewa likita yashigo duba ikhram ya tattaba jikinta yaji ba zazzabin sanan ya kara kallon yar ya dubi Amina yace"xaakarashe mata sauran ruwanta Leda daya xaasa da sauran alluranta insha allahu zuwa gobe idan takara samun sauki zaasallameku toh kawai Amina tace "yace zantura nurse tazo ta daura mata ruwan" toh kawai tace ya fice daga dakin... ******* Ahmad Na zaune a shago Aliyu yayi sallama da faraar Ahmad suka gaisa sama sama Aliyu ya amsa sanan yace"Ahmad ka kyauta yadda kayi jiya a wajen yarinya nan?sanan mubar wajenta kawai kanafadamun batayi makaba baka jira mezanceba kaja motarka kabarni ka kyauta...murmushi ahmad yayi yace "" yi hakuri ban kyautaba nasani amma wlhy nikawai batayimunba amma zanyi tunani....au har saikayi tunani?aibadaga ganinta zakaji ta kwanta makaba saikundan saba tukunna aiba haka akeyiba kadaiyi tunani kada kayi wasa da damarka yafada da Dan fushi..""afuwan Ahmad yace insha allahu zanyi yadda kace...""kokaifa inji Aliyu sukayi dariya gaba daya.. ***** Har rana Amina tana zaune babu Wanda yazo daga yan uwanta duba koya suka kwana ga yunwa tanaji sai abincin Asibiti taje ta siya da kudin da Ahmad yabata daganan ne tasiyo kati tasa a wayarta Dan takira anty saudat taji ko lafiya batazo dubasuba.... Wayarta tadauka ta danna kiran anty saudat bugu daya ta dauka da faraarta suka gaisa tayi mata ya me jiki sanan takecewa"anty saudat lafiya bakizo dubamuba ba Wanda yazo?""tace ayya Amina wlhy hanani fita akayi yau ance kullum sainafita shine nahakura gobe zan lallabeshi inzo kinji?kada kiyi fushi...laaa bakomi anty sai goben idan kinzo sukayi sallama ta kashe wayar Wunin ranan babu wanda ya leko dubasu banda Ahmad dayazo tunani takeyi kala kala gameda rayuwarta tasan tanaganin jarabawa iri iri... ***** Karfe shida Ahmad yayi sallama ya shigo kamar yadda yazo jiya tana zaune akan dadduma gefenta take away ne datasiyo abinci tagamaci...kujerar dazun ya janyo ya zauna yadan dubeta ta gefe yace ya me jikin?""da sauki tace gatanan tana bacci ruwan dayarage akasa mata sunce gobe zaa sallamemu...tana magana idonta a kasa shiko bakinta kawai yake kallon yadda take motsa lebenta besan tagama maganarba tanata kallonta.... Itakuma jin bece komiba tadago ta dubeshi karaf suka hada ido...yayi maza ya kauda kai ya mike yace""shikenan zanzo da safe kafin asallameku Allah ya sauwake yace ya juya ya fice bece komiba....kallo kawai tabishi dashi ***** Daddare yana kwance a katifa bacci ya gagareshi babu abinda yake tunani sai Amina yanason matarsa yarasata babu abinda ya janyo musu rabuwa sai WANKAN GIDA bayajin zaikara rayuwar aure da wata inba Amina ba babu abinda idonsa ke hasko masa sai tarar da ita dayayi tanabawa ikhram nono ta matukar bashi shaawa tayi masa kyau jiyayi a lokacin kamar ya rungumesu yaji dadi.... Kirjinsane yake harba masa Sauri da Sauri shifa yanason matarsa anya zai iya jure rashinta koda zaiyi aure dolene yadawo da Amina dikda yasan yana kokwanton yin wani aure Kwancitarsa ya gyara gabansa yafadi daya tuna furucin mahaifiyarsa datace " *wallahi tallahi* *Ahmad kagama* *zama da Amina har* *abada* ya zaiyi da wanan rantsuwar da innarsa tayi gashi tun baayi nisaba wata biyu kawai yana bukatar matarsa ya zaiyi? *Mom farhan* *ina gaisuwa Allah* *yabar kauna* _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy 8鈨�1鈨�-8鈨�5鈨� Washe gari da safe Ahmad ya shiga gida bayan ya kintsa yayi adonsa yayi ras dashi da sallamarsa ya shiga dakin ina,da faraarta ta amsa mishi suka gaisa sanan yace"innah zance Asibiti wajensu ikhram jiya Amina tace da safe zaa sallamesu zanje koda zaa bukaci wani Abu a Asibiti""dakyau Ahmad ka rinka kulawa da lafiyar yarka har zuwa lokacinda zamu amsheta idan uwarta zatayi aure Dan bazamubarta tayi agolanciba,,gaban Ahmad ne ya fadi jin Kalmar da inna tayi wai Amina zatayi aure tabdijan anya zai iya jure wanan bakar ranan?ranan da zai ganta a matsayin matar wani gaskiya bazai iyaba....yana cikin tunanin ne innah tace katashi kaje mana rana tanayi mikewa yayi jiki a sanyaye ya fita... ****** Isar Ahmad kenan yatarar da Amina zaune likita ya shigo dakin yana kara duba jikin ikhram da taji sauki sosai yana yan rubuce rubuce Ahmad Na gefe yana kallonsu.....mika mata takaddar sallama likitan yayi tare da kafeta da wani irin mayen kallon yana murmushi ita kanta Amina saida yabata kunya Dan sassauto da murya yayi yace kinada aure?dammmmm gabanta ya fadi ta daga kai zatabashi amsa suka hada ido da Ahmad ya kafeta da ido.....gabanta yana faduwa ta girgiza kai alamar ah ah ....""good likitan yace sanan yace tabashi number ta zai rinka kira yanajin lfyr ikhram jiki a sanyaye tabashi number "" yace saikinji daga gareni ya fice.... Dik abinda yafaru akan idon Ahmad ne Wanda kirjinsa ke bugu Sauri da Sauri idanuwansa sunyi jajur kishi me tsananine ya taso masa ransa yayi matukar baci takowa yayi inda take a zaune kmr andasata ya dauki ikhram ya kwashi kayan cikin dasasshiyar murya yace "muje" ba musu tabi bayansa Suna isa inda yayi parking ya bude mata gaban mota ya mika mata ikhram yajasu da gudu kamar zai tashi sama tuki yakeyi hankalinsa baya jikinsa lallai ya yarda so masiface yafada tarkon kaunarta fiyeda da gashi ba aure yanzun tsakaninsu ya xaiyi?da wanan tunanin suka iso kofar gida yana gama parking ta bude ta fita ta tsaya ya fito musu da kayansu yace sainazo kara duba jikin Nata tace "toh" kawai ta shige gida ya bita da kallo... ****** Ahmad Na isowa kasuwa ko shago be budeba ya wuce shagon Aliyu da sallamarsa suka gaisa sanan yaja kujera ya zauna huci kawai yakeyi Aliyu yadafashi yana yar dariya yace"mutumina waya tabakane naganka kamar ankoroka yafada yana zolayarsa Ahmad yace"meyema baayiba Nan yakwashe dik abinda yafaru a Asibiti yafadawa Aliyu...dariya sosai Aliyu yakeyi yace"mutumina nan nakaika inda zaafaranta maka rai kuyi soyayya ka mance da Amina kace yarinyar batayi makaba yanzun gashi agabanka tabada number wayarta kuma Na tabbata likitan nan sonta yakeyi bawani saboda ikhram ya amshi number kaika hana kanka sakewa da wata Ita gashinan wani ya kyasa...ya fashe da dariya Haushi Yakama Ahmad wato yafadawa Aliyu damuwarsa yana masa dariya mikewa yayi ya zura takalminshi yace"idan kagama dariyar mayi magana anjima bejira me Aliyu zaiceba ya fice... ***** Karfe hudu Na yamma Ahmad Na zaune a shago babu tunanin dayakeyi saina Amina hoton fuskar likita kawai yake hange lokacin da yakewa Amina murmushi yana magana....nan da nan kishi yakara turnikesa lallai dolene yasan abinyi dole yasan hanyar da zaishawo kan innah ya maida matarsa tunkafin sonta ya haukatashi ******* Amina nazaune a daki da misalin karfe Biyar Na yamma kira ya shigo wayarta bakuwar numberce ta dauka takara a kunnenta batace komiba sallama yayi nan da nan tagane muryarsa ta amsa suka gaisa yayi mata ya jikin ikhram tace da sauki sanan yace"kun mance da maganin sallamarku Baku amsaba inbazaki damuba kiyimun kwatancen gidanku idan natashi karfe shida inzo inkawo muku ba musu tayi mishi kwatance tunda yace magani suka mance sallama yayi mata ta ajiye wayar gabanta Na faduwa ***** Karfe shida Na yamma tanata hidimar Dora abinci tasamu hajiya ta rike mata ikhram suna zaune a tabarma Yaro yayi sallama ta amsa yace"wai ance Maman ikhram tazo inji wani a waje a mota hajiya ta zabura tace uban waye muje ingani ko Mara kunyar nan ne Ahmad tana lekawa taganeshi likitan asibitune hajiya ta washe baki suka gaisa tace bari aturota kasan batagama iddah ba shiyasa Na leko inga waye murmushi yayi ya amshi ikhram ta juya azuciyarsa yace aiko bazan fada mata soyayya takawoniba sai ranan data gama iddah saboda kada inharamtawa kaina wanan tsaleliyar yarinya.... Fitowa tayi sanye da hijabi suka gaisa tace bari inkawo maka ruwa yace toh... ****** Ahmad Na rufe shago Amina tafado masa dolene yaje gidan yafakeda yazo ganin ikhram ne da jiki daganan yaganta koyaji sanyi a ransa da wanan tunanin ya fito kasuwa ya tado mota.... ****** Amina takawo mishi ruwa ya amsa sanan yace muje inbude mota inbaki sakon ba musu suka jero kamar matada miji...daidai nan Ahmad yakaryo kan motarsa cikin layin gabansane ya fadi ganin Amina ta jero da wani yana rungume da ikhram kamar matarsa Parking yayi daga baya yakura musu ido likita ya bude motar ya Ciro katuwar Leda cikeda shopping din baby hardasu pampers ya mika mata ta tsaya kallonsa yace"Dan Allah kada ki maida hannun kyauta baya shedan ne keyin haka jiki a sanyaye ta amsa ya Ciro kudi yabata yace taba hajiya tasiyi goro ta amsa tayi godiya ya shiga ta daga mishi hannu yaja mota ya wuce ...dik abinda sukeyi idon Ahmad nakansu kirjinsane yake bugawa zuciyarsa kamar zata fito daga kirjinsa... Tana waigawa sukayi ido hudu da Ahmad gabanta ya fadi ta nufo hanyar motarsa yanaganin haka yaja a kuje yabada mata kura... Jiki a sanyaye ta shiga gida Niki Niki da Leda hajiya naganin haka tafara washe baki tana kallon Amina kudin dayabata taba hajiya ta mika mata tace yace kisiyi goro jiki Na rawa hajiya ta amshe tace kaga inda ake harkar arziki ba tsiyaba Allah ya rabamu da wanan matsiyacin yaron Mara kunya ahmadu... Itadai Amina jiki a sanyaye ta shige daki tana tunanin Ahmad.. **** Ahmad dakyar yake tukin motarsa saboda jiri dayake dibarsa yau Amina yagani da wani a tsaye tana daga mishi hannu dole ya dauki mataki da wuri tunkafin dama ta kubuce masa....gabansane yafadi lokacinda ya tuna babu Wanda zai fuskanta da zancen Amina a saurareshi *Kuyi maneji* *wallahi a kwance* *nake* _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy Na sadaukar da wanan page din gareki uwar kowa *Anty sis* Allah ya kara miki lfy ILUSM馃槏 8鈨�6鈨�-9鈨�0鈨� Amina bakaramim tashin hankali ta tsinci kantaba SBD ganin da Ahmad yayi musu tasan dole ransa zaibaci yaganta da wani dikda ba aure bane tsakaninsu zuciyarta ta cigaba da azalzalarta akan takirashi a waya.....wayarta ta dauka ta danna kiransa tayita ringing harta katse be dagaba tasan yaji haushine kuma babu Wanda yajawo hakan sai wanan likitan dayazo bata gayyaceshiba...wani irin haushinsane yakamata tayi tsaki tagyara kwanciya cikeda tunanin Ahmad..... ******* Washe gari da safe yatashi da matsanancin ciwon kai sakamakon rashin barcin da beyiba a Daren jiya daya rufe idanunsa hoton Amina yake gani da wanan likitan.....jiki babu kwari ya lallaba ya shiga cikin gidansu.... A daki ya tarar da innahrsa tana karyawa yayi sallama ya shiga suka gaisa....idanunsa ta kalla ganin yadda sukayi jajir dasu tace""Ahmad lafiya?"" Dakyar ya dago.idonsa yana kallonta yace innah babu lfy.... ""Tace meyafaru?" Innah ki gafarceni a gaskiya inacikin matsala Mara misaltuwa innah ina cikin damuwar rashin amin....bekarasaba inna ta zabura ta mike tsaye cikeda fada da kallon mamaki tace "" Ahmad yaushe kazama maraji bansaniba?menafada maka akan Amina?ka mance dik rashin mutunci da tozarcin da iyayenta sukayi maka sukayiwa yan uwanka?saboda bakada zuciya zaka koma mata to wallahi tallahi baka isaba kayi kadan yanxun ne zaka hadu da fushina Wato saboda Na baka damar zuwa wanjentane yasa saboda bakada kunya kake iya fadamun kana cikin matsala akan macen da danginta suka gama tozartamu to kayi kadan ka wulakantani wallahi tallahi.... Ahmad!!!takira sunansa da wata irin murya dabetaba sanin tanada itaba tace magana ta karshe Na haramta maka zuwa gidansu Amina daga yau kome zaakai musu zantura kannenka suje kuma maganar daka fadamun Aliyu yasama maka yarinya me hankali a unguwarsu ya zama dole ka daidaita da ita atura maganar aurenka da ita Dan Na fahimci take takenka Amina kakeso ka maida tobada yawunaba Ahmad.... Zuface kawai take ketowa Ahmad a jikinsa kalaman innah sunyi tsauri dayawa zuciyarsace ke harbawa Sauri da Sauri ya tsugunna a gabanta yace "" innah kiyafemun bata miki rai danayi insha allahu bazan kumaba nayi kuskure...ta kallesa ta gefe tace ya wuce kada insakeji "" kai kawai ya gydamata yace bari inje inyi shirin kasuwa...tace"kacewa Aliyu ina son ganinsa""toh kawai yace mata badan zaifada mishiba Dan yasan mezatayi ya fice a dakin... ***** Misalin karfe uku Na rana Amina ba rikeda waya tana tsammanin kira daga Ahmad amma shiru...ta runtse idanuwanta hawaye masu zafi nabin kuncinta taji ringing firgigit ta bude ido a tsammaninta Ahmad ne saitaga likita a fuskar wayar abinda tayi masa saving dashi kenan SBD batasan sunansaba...kife wayar tayi a gefe SBD wani haushinsa datakeyi...tanata ringing harta katse a karo Na biyu yakuma kira saita danna dauka takara a kunnenta batare da tace komiba... Ranki yadade yace yanadan murmushi me Sauti...dakyar ta gaisheshi ya amsa cikeda kulawa yake tambayarta ikhram tace tana bacci yace dama inaso inzo anjima inganta...haushinsa ta turniketa tace bana bukata...gabansane yafadi yace haba Maman ikhram xanxo induba jikintane takuma cewa Dan Allah likita nagode da zuwan da kayi jiyama kadan nisanceni yanxun Dan Allah tana gama maganr ta katse wayar saboda wani haushinsa datakeji dik wayar datakeyi hajiya Na kofar daki tana jinta da Sauri ta shigo dakin zaninta a hannu... Amina badai mutumin dayaxo jiya kikewa wanan wulakanciba?...Amina ta turo baki tace shine hajiya bana bukatar ziyararsane.... Kajimun yar kwal ubar yarinya mutumin arziki yabiyoki har gida kinemi wulakantasa to baki isaba wallahi kinyi kadan dik abinda kike nufi daidai nake dake.... Amina Allah ya kawo mana mutumin arziki kena nema kiyiwa kanki salalan tsiya to tun wuri kiyiwa kanki fada wallahi.... Amina ta kalli hajiya gabanta nafaduwa bakinta Na rawa tace"ni gaskiya gidan mijina zan koma.... Wani zabura hajiya tayi tayo kanta kamar zata duketa tace"ko suleman be isaba ballantana ke wallahi Amina kisani idan mafarki kikeyi ki farka kingama zama da wanan matsiyacin yaron dangin marasa mutunci.... Kuma kisani yaxo Asibiti wajenki koh?to yagama zuwa gidan nan idan ba hakaba idan yazo dik abinda nayi masa shiya siya sana Tara masa mutane naci masa zarafi Mara zuciya kawai.... Dik wulakanci da tijarar da yan uwansa sukayi baki ganiba saboda bakida zuciya zaki cigaba da bibiyarsa har gida yazo ya sakeki a gabanmu amma da yake bakida zuciya bakida kunya kike fadamun wanan maganar To ki tattara kayanki kibishi idan kincika Mara kunya kikai kanki da kanki daga yau ko kofar gida kin daina fita idan ba hakaba xakiga abinda zansa ummaru yayi miki shashasha....ta fice a dakin tanata sababi..... Kuka sosai Amina takeyi kalaman hajiya sunyi mata zafi ga cinzarafin Ahmad datakeyi dole taji babu dadi koba komi uban yartane bazataso aci zarafinsaba ballantana yadda takejin sonsa a ranta baxata iya rayuwa da wani namijiba... ******* Likita yana zaune a office babu wadda yake tunani sai Amina yasan cewa yakamu da matsananciyar soyayyata amma tunda bata bukatarsa yanxun zai nisanceta zuwa lokacinda zata cika iddarta zaicigaba da zuwa wajen hajiya yana gaisheta yanayi mata alheri yasan ko Amina bataso zaa tursasata dole ta aureshi da wanan tunanin yayi murmushi ya gamsu da shawarar da zuciyarsa tabashi.... ****** Ahmad tunda yaje kasuwa zazzabi me zafi ya rufesa sakamakon damuwar dayake ciki zafi biyu ya hadun masa ga wutar son Amina ga furucin innah a gareshi lokacin tashinsa beyiba yadawo gida yashige dakinsa babu Wanda yasan yadawo sallahr magriba da ishai dik a dakinsa yayisu sanan yasha maganin zazzabi ya kwanta.... ******** Bayan kwana uku da faruwar wanan lamari Amina tana daki babu abinda takeyi sai aikin kuka da tunanin Ahmad gashi ko kiransa tayi baya dauka tarasa inda zatasa rayuwarta saboda bakin ciki gashi tunda tadawo Asibiti anty saudat batazo gidanba ballantana tafada mata abinda kedamunta taji dadi gashi ansa mata dokar fita ko kofar gida yayanta da hajiya ta kwashe komi tafada mishi harda kari ya yadda... Wani tunanine yafado mata kodai zatasamu Ahmad a kasuwane su daidaita Kansu inhar zai maidata tayanke shawarar binsa koda yaddar hajiya da yan uwanta ko babu zatabishi tasan watarana zasu gane gaskiya....sanan bazata bari wanan likitan ya shiga tsakaninta da Ahmad ba... Fargabarta dayace ba lallai bane yanxun iyayen Ahmad su yadda ya maidataba saboda irin rashin mutuncinda yan uwanta sukayi musu ranar Suna...itadai tayi datasanin biyewa yan uwanta da kakarta zuwa WANKAN GIDA gashinan yan uwanta ko wacce tana dakinta a zaune itace tafada matsaloli a sanadin WANKAN GIDA aurenta har mutuwa yayi gaskiya bazata manta da wanan jarabawar datake cikiba..... Hawayene ke zuba a idanuwanta datasani Mara amfani takeyi amma tayi alkawarin komawa mijinta komi runtsi bazata bari a shiga tsakaninta da masoyinta Na gaskiya ba... ******* Ahmad kuwa dakyar yasamu yasamawa zuciyarsa natsuwa dikda cewa bawai yadaina son Amina ba yanasonta kuma be cire raida maidataba....dik hanyar da zaibi yaga ya cika burinsa zaibi..... Matsalarsa dayace mahaifiyarsa da tadau zafi a lamarin amma da sannu zaishawo kanta yasan tanada hakuri kuma zata sauka daga fushin datayi...... ******* Ahmad ne zauneda mahaifiyarsa bayan magriba sunadan taba hira tace Ahmad nace kacewa Aliyu ina nemansa banganshiba nasan bakafada mishiba to wlhy kafada mishi inaso insamu cikakken bayani akan yar daka fadamun yasamar maka Dan aure zakayi nanda wata uku nafada maka....kafada mishi yazo ina nemansa.... Kirjin Ahmad babu abinda yakeyi sai bugawa Sauri da Sauri jin innah tace zatayi mishi aure nanda wata uku...dolene yasamu Mafita tunkafin aukuwar wanan lamari **** A kasuwa Ahmad Na zaune shida Aliyu yake shaida masa innah tana nemansa...amma Dan Allah yayi masa wata alfarma kada yafadawa innah wani Abu akan Khadija danshi be raayin aurenta....murmushin mugunta Aliyu yayi yace bakomi abokina kada kadamu idan antashi kasuwa sai muje gidan inji kiran...Ahmad yace shikenan ******* Bayan magriba Ahmad da Aliyu suka shiga dakin innah ta amshesu da faraa tacewa Aliyu tun kwanaki nake nemanka befada makaba murmushi Aliyu kawai yayi .... Innah ta gyara zamanta tace inaso kafadamun tsakaninka da Allah yarinya da kukaje wajenta ya halayenta suke?gaban Ahmad yafadi ya kurawa Aliyu ido yaji mezaice..... Aliyu ya gyara zama ya kwashe komi yadda sukayi a rana tafarko da sukaje gidan yafadawa innah sanan yafada mata kyawawan halayen yarinyar.... Alhamdulillah innah tace ka shirya zaka rakani gidansu yarinya inganta inganada uwar yarinyar kafin kanin mahaifnsa yaje nema masa aurenta Dan bazan yadda adawo da Amina ba yan uwanta sucigaba dayi mana wulakanciba nagode Aliyu kaji Allah yayi albarka"ameen innah Zuface kawai ke tsattsafowa Ahmad a inda yake zaune gabansa sai faduwa yakeyi jin abinda innah ke shirin aiwatarwa dolene yasan mafita kafin yarasa farin cikinsa zuciyarsa sai harbawa takeyi Sauri da Sauri.. _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy *Anty kk* da *Razan* yan team aliyu馃き馃槣da *Faty* *Dan maliki* ya gode da kaunarku馃槅yana gaisuwa馃槀 9鈨�1鈨�-9鈨�5鈨� Dik maganarda Aliyu da innah ke tattaunawa hankalin Ahmad baya jikinsa Abu dayane ya razanashi cewan datayi zataje Neman mishi aure shiyafi tada mishi hankali SBD yasan tunda innah tafada zata aikata yana cikin wanan tunanin yaji muryar Aliyu yanace mishi zaitafi shi...jiki a sanyaye Ahmad ya mike ya rakashi har kofar gida batareda yace komiba ya juyo yashige dakinsa.. ****** A Daren ranan likita yana kwance a dakinsa yarasa sukuni SBD rashin ganin Amina dabeyiba kwana biyu anya zai iya hakura ya kyaleta kmr yadda ya yanke shawara?zuciyarsa babu abinda take ayyana masa sai yaje gidansu Amina da safe kafin yaje aiki daganan ya ganta koda batace mishi komiba da wanan shawarar ya kwanta bacci yadaukesa.... ******* Washe gari da safe wajen karfe Tara nasafe likita yayi shirinsa tsaf cikin kananun kaya da suka amshi jikinsa ya dauki kayan da zai bukata yasa a mota ya nufi hanyar gidansu Amina.... Hajiyace zaune a daki da yar lelenta anty Sahura datazo gidan da wuri kasancewar ta kwana biyu batazoba hajiya nabata labarin likitan asibitin da yazo wajen Amina ta da hidimar dayayi musu take Neman ta wulakantasa....suna cikin tattaunawane sukaji sallama a kofar gida...da Sauri hajiya ta mike Dan ganin waye tana lekawa taganshi taganeshi ta Washe baki tana sannu da zuwa likita yadan rusuna yace sannu hajiya""shigo daga ciki kaji kaima nan gidankune cewar hajiya...ba musu ya bita dakinta ta nufa dashi fa faraarta sukayi sallama anty Sahura ta amsa cikeda faraa ta shimfida mishi dadduma ya zauna Gaisawa suka karayi yace yazo gaishetane dama zai wuce wajen aiki hajiya ta Dada Washe baki tace nagode likita gashi bamusan sunankaba murmushi yayi ya dukar da Kansa yace sunana ABDUL JABBAR amma mutane nakirana doctor abdul... Hajiya da faraa tace masha allahu sanan tace bari akira aminar Ku gaisa da Sauri yace toh hajiya.... Dakin Amina ta Shiga wadda dik abinda sukeyi tanajinsu haushi kamar ya kasheta saiga hajiya ta shigo ta daure fuska tace kije Ku gaisa da likita zai wuce saura kiyi wanan mugun halin naki inci mutuncinki agabanshi.... Ba musu amina ta dauki ikhram tabiyo hajiya tayi sallama ta tsugunna daga gefe suka gaisa sama sama fuskar Amina a daure ta mika mishi ikhram ta fice ta koma dakinta ranta a bace ... Suna nan zaune bayan minti Biyar ya mike ya Ciro kudi aljihunsa yacewa hajiya ga wanan ba yawa da faraarta ta amshe tana godiya anty Sahura daga gefe ya bata nata sanan yaciro.wasu yabawa ikhram yace a siya mata pampers hajiya tace"haba likita wanan dawainiya haka?mungode Allah yayi albarka yace ameen ya mikawa anty Sahura ikhram ya fice da sanyin jiki SBD beyi tsammanin Amina zatayi masa hakaba amma bakomi.a hankali zai kamata xaiyi hakuri ya jure da wanan tunanin ya fice a gidan... Hajiya kuwa Allah Allah takeyi yatafi taje dakin Amina taci mutuncinta mikewa sukayi anty Sahura na rike da ikhram suka shiga dakin Amina Hajiya tace lallai Amina kincika Mara mutunci wato wanan bawan allahn dayazo rayuwarmu Dan muji dadi kikeso ki rinka wulakantasa SBD tsohon mijinki to kinyi kadan yarinya wlhy ko zaki mutu idan ya nemi aurenki saimunbashi saboda Allah ya kawo mana arziki har gida bazaki koreshiba gashinan harda kudi yabawa yarki idan baki kaunarsa kada ki amshi kudin.... Karaf Amina tace hajiya banrokesaba ya rike kudinsa....anty Sahura tace to hajiya Mu.amsa mukara suka rike kudin da akaba ikhram suka mika mata yarta hajiya tace mugun halinki yakare miki suka fice a dakin..... ****** Ahmad tunda yazo kasuwa be nemi aliyuba saboda haushinsa dayakeji,haushin abinda yayi masa yasa ko hanyar kofar shagonsa beyiba... Shima Aliyu yasan abokinsa na fushi dashi shiyasa yakyalesa be nemeshiba har zuwa lokacinda zai huce su shirya.. ******* Yau takasance jumaa ranan da innah sukayi alkawari da Aliyu zasuje gidansu yarinyar da Aliyu yaraka Ahmad tun safe innah ta shirya itada Zahra tace suje tare tarakata dik sun shirya Aliyu suke jira... Bayan sallahr jumaa Aliyu ya iso gidansu innah da me napep dinsa ya tsaida kofar gida yashiga suka gaisa da innah yace su fito da me napep.suke innah ta Sanya hijabinta dama ta shirya tsab tai kyau abinta Zahra ma HK sukafito suka shiga napep suka tafi Sun iso gidan Aliyu yayi musu jagora har dakin mahaifiyar yarinyar kasancewa Dan gidane shi sunsanshi tunda unguwarsu daya ... Tarba me kyau mahaifiyar Khadija tayi musu dikda batasan meyakawosuba akabasu ruwa me sanyi sukasha sanan Aliyu ya gabatar mata da cewa innah CE mahaifiyar Ahmad da sukazo kwanakin baya wajen Khadija Da faraarta suka kara gaisawa da innah sanan innah tace nice mahaifiyarsa nace bari inzo mugaisa daku insan suwaye mahaifan yarinyar dikda bani yakamata inyiba mahaifinsa ne kuma ya rasu yanada yan uwa amma baanan garin sukeba shine nace bari inzo mugaisa...""Allah sarki mahaifiyar Khadija tace mungode Allah yasaka da alheri Allah ya kara zumunci""ameen" Innah tace inafatan dai babu Wanda ya nemi auran yartawa saboda kinsan yanada kyau musan hakan saboda rashin kyautuwar Neman aure kan aure...mahaifiyar Khadija tace babu""alhamdulillah innah tace insha allahu zanje insamu kanin mahaifinsa suzo a nema masa aure inhar kunbamu izini...munbaku inji mahaifiyar Khadija da faraarta saboda tayaba da innah kwarai daga ganinta dattijuwar kwaraice... Innah da faraarta tace to a kiramun yartawa inganta ba musu mahaifiyar Khadija tashige wani daki a cikin gidan jimmm kadan tafito ta shigo tazauna wajen zamanta tace gatanan zuwa... Tunda Khadija tafito dakinsu sanye da dogon hijabi ta shigo inda su innah suke da sallamarta ta zauna gefen Zahra ta durkusar dakai ta gaida innah cikeda kunya da girmamawa innah ta amsa da faraarta sanan tace"masha allahu ...Allah ya tabbatar mana da alheri insha allahu cikin sati mai zuwa iyayen Ahmad zasuxo kafin nan zaizo sukara ganawa da khadijar Mu zamu tafi...mahaifiyar Khadija tace mungode sosai tayi musu rakiya har zauren gidan ta juya ta koma... A hanyarsu tagida innah ke cewa Aliyu gsky tayabada yarinyar daga ganinta tasamu tarbiya kuma mahaifiyarta Nada mutunci Aliyu yace kwarai dagaske mutanen arzikine Sunata tattaunawa a hanya har suka iso gida akasaukesu ya wuce kasuwa abinsa da faraar abokinsa yasamu matar aure... ***** Ahmad tunda yaga Aliyu be bude shagoba yasan yau sukayi zasuje gidansu Khadija da innah gabansa faduwa ya rinkayi yana tunanin makomarsa idan aka daura mishi aure da wadda ba aminaba wunin ranan jikinsa a sanyaye yayishi ****** Daddare bayan magriba ya shiga cikin gida wajen innah gabansa na faduwa da fargabar abinda zaijiyo suna zaune da faraarta ta kwashe dik abinda yafaru tafadawa Ahmad da shawarar data yanke zatasamu kanin mahaifinsa tafada mishi aje Neman aure... Gaban Ahmad yafadi zufa nata tsattsafo masa dakyar yace toh ya mike ya shige dakinsa jiri na dibarsa gefen katifarsa ya zauna yafara tunani dolene kafin abunan yayi nisa yasan abinyi....take wani tunani yafado masa kafin innah taje wajen kanin mahaifinsa ta bata mishi shiri zai rigata zuwa wajensa ya gabatar masa da yanason maida matarsa kawai inba hakaba idan ta rigashi to dolene yasan ba makawa sai anyi mishi aure da wanan tunanin zuciyarsa ta aminta da safe zai nufi kauyen da kanin babansa yake....kwanciyarsa yayi bacci yadaukesa... ****** Da sassafe Ahmad ya shirya ya nufi kauyensu baba Ibrahim kanin mahaifinsa ya isa da wuri kasancewar da safe ya dau hanya yasamu tarba sosai irinta mutanen kauye yana zaune akan tabarma Baban nasa na fuskantarsa yace ahmadu meke tafe dakai?Ahmad cikeda girmamawa ya kwashe komi dayafaru yafada mishi da hukuncin da innahrsa ta yanke... Baba Ibrahim yace gaskiya baayin haka bekamata Hauwa u ta yanke wanan hukuncinba ka kwantar da hankalinka kada kadamu jibi zanzo garin Ahmad cikeda farin ciki yayi godiya bayan sallah laasar yabaro kanin babansa yayi masa alheri sosai sukayi sallama akan jibi zaizo... **** Ahmad sai karfe Tara nadare ya iso gida directs dakin innah ya Shiga sukagaisa tace yaudasafe bangankaba Ahmad yace yafita wasu harkokinsane innah tace Allah yataimaka abincinsa yadauka ya wuce dakinsa.. ***** Bayan kwana biyu yau takasance baba Ibrahim zaizo Ahmad befadawa innah ba ya shirya yatafi kasuwa Misalin shadayan safe baba Ibrahim ya iso gidan innah da faraarta ta amsheshi tana cewa dama cikin satinan zaatazo wajensa yace to aiganinazo bayan yazauna angabatar masa da abinci Karin kumallo yayi yagama sanan yacewa innah maganace ta kawoshi ta natsu ta fuskancesa Nan yakwashe dik yadda sukayi da Ahmad yafada mata sanan yace ban bukatar wani uzuri tunda ya nuna yanason matarsa abarshi ya maidata... Innah ko mutuwar zaune tayi wato Ahmad abinda zaiyi mata kenan ya watsa mata kasa a idanu to be isaba ko zai maida Amina dolene ya auri Khadija... _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy *Masoyan* *Amina* *da ahmad* *ina gaisuwa* 9鈨�6鈨�-1鈨�0鈨�0鈨� Sosai ran innah yabaci abinda Ahmad yayi mata...gyaran murya baba Ibrahim yayi yace bakice komiba.... Innah tace da gaskiya akwai yarinyar danaje nema masa aurenta yar mutuncice iyayenta sunsan mutunci shine nace na amince yadawo da matarsa amma baxaa fasa wanan aurenba... Bazai yuwuba Hauwah Ahmad bayida karfin da zai rike mata biyu abinda nakeso dake kiyi hakuri kijanye maganar auren zuwa lokacinda karfinsa zaifi haka saiya kara ko ukune a rana daya.... Innah bazata iya musu da kanin mijintaba saboda yanada kima da daraja a idanunta yadda suka rikesu Ahmad amana bayan mutuwar Dan uwansu dolene tayi mishi wanan alfarmar Murmushi tayi tace shikenan Allah yasa haka shiyafi alheri kisawa abun albarka insha allahu bazamuyi danasanin maida auren nan ba... Murmushi innah tayi tace bakomi....baba Ibrahim yace anan zai kwana sai Washe gari zai koma idan sunje gidansu Amina shida Ahmad ya maidata tunda batagama iddah ba... Innah tace shikenan mikewa yayi tayi masa jagora zuwa dakin Ahmad dake zaure ya shiga ya zauna ****** Ahmad yana kasuwa dik hankalinsa yana gida yanata tararrabin abinda innah zatace haka ya wuni jikinsa a sanyaye ******** Da yamma bayan yatashi kasuwa da fargaba ya shiga gida saboda yasan yayiwa innah laifi danyasan bakaramin bacin rai zai tararba Da sallamarsa yashiga gabansa nafaduwa dakyar ta bude baki ta amsa yazauna yace sannu da gida yauwa kawai tace...shiru nawani lokaci..sanan innah tace "" sannu Ahmad me iyaye wato kaje ka hadani da iyayenka ko ka nunamin ban isaba Ahmad ka nunamin bakason farin cikina zuface ke ketowa Ahmad tako ina...tace naji zaka maida Amina amma kasani wallahi tallahi dik abinda iyayenta sukayi kaika siya da kudinka sanan baka isa kazo kacemun ga abinda tayi makaba,kuma kagama sakin Amina ko meye zai faru shashasha tashi kaje kabani wuri..... Hankalin Ahmad a tashe ya fita ya nufi dakinsa jiki a sanyaye...yana shiga ganin baba Ibrahim ya kakalo faraa a fuskarsa gudun kada yagane wani Abu suka gaisa sosai sanan baba Ibrahim yafadawa Ahmad yadda sukayi da innah sanan yace ahmadu wanan abun dakaga nayi maka bashi zaisa idan mahaifiyarka tabaka wani umurnin ka tsallakeba Kayi hakuri Allah ya rabaku lafiya ka rike yan kannenka kaji Allah yayi maka albarka"ameen inji Ahmad Ya mike ya shimfida dadduma ya kwanta a kasa yabarwa babansa saman katifa Daddare abubuwa biyune suka ziyarci zuciyar Ahmad lokaci daya farin ciki da bakin ciki farincikinsa daya zai maida matarsa abar kaunarsa abinda ke haifar masa da bakin ciki idan ya tuna cewa mahaifiyarsa tadau fushi dashi akan lamarin saiyaji babu dadi Babu komi a hankali zata huce yasan mahaifiyarsa macece me hakuri dasanin yakamata fushi tayi amma yasan zai wuce... ****** Da safe bayan sunyi Karin kumallo baba Ibrahim ya bukaci suje gidansu Amina da wuri saboda yasamu mahaifinta su tattaunawa yazo ya shirya kada yayi yamma.... Sun isa gidan gaban Ahmad sai faduwa yakeyi abinda zaifaru number Amina yakira tana zaune a daki taga kiran Ahmad da Sauri ta dauka bejira mezataceba yace kiyi mana sallama da baba toh tace ta mike tafito tashiga dakin Baban da sallama tagaisheshi tace su Ahmad ke sallama a wajen ya mike yasa takaliminsa ya fice itakuma tashige dakinta da fargabar to meyafaru Ahmad yazo wajen babanta? Da faraa Baban Amina ya amshesu suka gaisa a gurguje baba Ibrahim yasanarwa da malam suleman abinda ketafe dasu shikansa Mahaifin Amina yayi mamaki SBD betaba tunanin Ahmad zai maidataba...baba Ibrahim ya katse masa tunanin dayakeyi yace kabawa Ahmad izinin maida Amina dakinta... Gaban Mahaifin Amina ne yafadi daya tuna furucin hajiya akan Amina tagama zama da Ahmad amma yana matukar tausayin Amina SBD dik yayansa babu meyi masa biyayya kamarta dole yayi komi Dan farin cikinta...besan lokacinda ya furta nabaka izini ahmadu.... Da sauri Ahmad ya dago kansa saboda ganin Mahaifin Amina yayi shiru yagama sadakar da cewa bazai aminceba... Da Sauri Ahmad yace ni Ahmad na maida matata Amina na maida aurenmu kasancewar bata gama iddah ba dama shikenan babu wani daura aure... """" alhamdulillah cewar baba Ibrahim dama haka akeso tunda ka maidata shikenan kuma ga mahaifinta agabansa akayi to alhamdulillah Allah ya kyauta gaba sai a cigaba da hakuri Bakin Mahaifin Amina yaki rufuwa saboda farin ciki yasan wanan labarin babu abinda zaikaishi dadi wajen Amina Nandai suka kara tattaunawa Ahmad da baba Ibrahim sukayiwa Mahaifin Amina sallama yace musu zata koma dakinta nanda wata daya idan sun kintsa..baba Ibrahim yace ba matsala sukayi sallama suka tafi... A gurguje suka koma gida baba Ibrahim yafadawa innah yadda akayi sukayi sallama Ahmad yadaukeshi suka nufi tasha yasashi a mota... **** Mahaifin Amina yana shiga gida dakin hajiya ya shiga yace gobe insha allahu zaitara yaransa da ita akwai maganar da zaiyi dasu....... Baki ta tabe ta kallesa a wulakance tace Allah ya kaimu yace ameen ya mike ya shiga dakinsa A ranan yakikkirasu a waya yafada musu yanada bukatar magana dasu Washe gari Dik abinan dayafaru Amina batasan mekefaruwa ba fargabarta daya batasan mesu Ahmad sukazoyiba gidansu hankali ta baa kwance yakeba har dare bacci barawone yadauketa... ***** Washe gari da safe kowacce tazo daga gidan mijinta jin kiran mahaifinsu Anty saudat CE kefadawa Amina ai mahaifinsune yace suzo Amina cikin fargaba tace Allah yasadai lafiya anty saudat tace ameen... Suna zaune anty Sahura ta leko tace suzo suka mike a tare ko wacce gabanta na faduwa suka Shiga dakin hajiya ko wacce ta zauna... Alhamdulillah bawani dalili bane yasa natara kowa a nan sai inshaida muku jiya ahmadu mijin Amina sunzo da kanin mahaifinsa.....gaban Amina ya tsananta faduwa... Yazone akan inyi masa izini ya maida matarsa tunda dama bata fita iddah ba kuma nayi masa izini ya maidata jiya nafada masa zasu tare nanda wata daya.... Zumbur hajiya ta mike cikeda masifa tace wallahi suleman baka isaba kayi kadan ka watsamun kasa a idanuna ka nunamin ban isa inyi iko da yayanka ba wlhy baka isa Amina takoma dakintaba tun wuri ka kirasu ka warware munafunci da kullin daka hada inba hkba zakasha mamakin hukuncin da zan dauka... Anty saudat said faraa takeyi da murnar burinta ya cika yar uwarta zata koma dakin mijinta kamar kowa... Amina hawayene yake zarya a idanunta na farin ciki...ubanta yagamayi mata komi a rayuwa daya dawo mata da farin cikinta Ahmad....Dan tunda tarasa Ahmad tarasa farin cikinta batada Kalmar dazata yabawa mahaifinta dashi saidai tayi mishi addua... Anty Sahura dake gefe cikinta ya duri ruwa saboda tarigada ta cinye kudin kayan dakin Amina batada hanyarsu batasan ina zatasamesuba tana cikin tashin hankali.... _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy 1鈨�0鈨�1鈨�-1鈨�0鈨�5鈨� Hankalin anty Sahura bakaramin tashi yayiba daka kalleta tana cikin tsananin tashin hankali Anty saudat ta kalleta ganin halin datake ciki tace to yakamata nanda sati daya kikawo kudin kayan dakin aminatu a siya mata wasu saboda shirye shiryen komawa da zamu farayi mata basai lokaci yayiba muzo muna zura ido....sarai taga halinda take ciki anty saudat ta saki murmushi Dakyar anty Sahura ta dawo da natsuwarta baki Na rawa tace Allah ya kaimu sati me zuwan...ameen anty saudat tace Babansu ya Mike ya shige daki anty saudat da Amina suke mike suka shiga dakin Amina suka rungume juna anty saudat Na taya Amina murnar komawa dakinta da zatayi nan suka sunata yar hirarsu...anty saudat ke cewa Amina zanfara kawo miki kayan gyara Wanda idan kika koma ahmad zai kara zaucewa akanki....sunkuyar da kai Amina tayi cikeda kunyar anty saudat.... Anty Sahura da hajiya Na zaune a daki Sahura Na famar yiwa hajiya famfo akan kada ta kuskura ta yarda da mgnr komawar Amina dik wulakancinda yan uwan Amina sukayi musu ta karayiwa hajiya famfo Hajiya tace indai da raina zanga yadda zaayi a fitar da ita daga gidan nan zuwa wani gida da sunan Ahmad Da wanan anty Sahura tadanji sanyi a ranta saboda hankalinta ba karamin tashi yayiba ******** Innah tana zaune tare da yayanta duka hardana gidan miji da sukazo gaisheta anata cin abinci ta gyara zama tace akwai maganar datakeson shaida musu ko wacce ta bata hankalinta suka natsu Tace dama zanfada muku yayanku ya maida Amina jiya...ko wacce cikeda mamaki take kallon innah saidai dukansu fuskokinsu dauke da murmushin jin dadi Zainab babbar ciki tace innah alhamdulillah Allah yasa HK shiyafi zama alheri SBD ni wlhy koda mukaje akayi wanan tsiyar ban tsani anty Amina ba SBD ita tanada hali Na gari wlhy naji dadi Innah ta galla mata harara tace Toni bada son rainaba SBD naso ace ya auri yar mutunci ba Amina da danginta marasa mutunci ba Rabiah tace"innah kibar wanan mgnr Dan Allah muyi musu adduar zaman lfy Allah kadai yasan dalilin daya kaddara komawar wanan auren kiyi hakuri koda zakiyi fushi da yaayaah ki sassauta masa Dan Allah Innah batasake cewa komiba ta mike tabarsu falon tashige daki sukabita da kallo dukansu sunsan tayi fushi amma zata huce ******** Ahmad yana kasuwa daka gansa kasan yau yana cikin farin ciki aliyune ya shiga shagon da yar faraarsa yace angon Khadija...da murmushi Ahmad ya dago kai yace angon Amina Baban ikhram dai...da mamaki Aliyu ke kallonsa Ahmad yabashi labarin ai ya maida Amina dik jikin Aliyu a sanyaye yace Allah ya sanya alheri bekara minti biyarba a shagon ya fita ******* Da yamma Amina taji ta tsinci kanta cikin annashuwa kwalliyarta tayi me kyau ta sanya wata atamfa cikin wadda Ahmad ya kawo mata da suna tayi mata kyau tayi simple makeup ta feshe jikinta da turare ikhram ma akayi mata kwalliya sukayi ras dasu... ***** Bayan Ahmad ya tashi kasuwa harya nufi hanyar gida kawai zuciyarsa ta ayyana masa yaje yagasu ikhram ya juya kan motarsa ya nufi gidansu Amina Dan nesa da gidan yayi parking Wayarsa ya dauka yakirata tana zaune rike da ikhram wayarta tayi ringing da Sauri tadauka yace tazo yana kofar gida... Da sauri ta mike ta dauki sabon gyalenta ta yafa ta saba ikhram a kafadarta suka fito batareda sanin wani a cikin gidanba Tun daga nesa ya kura mata ido tayi masa kyau kmr sabuwar amarya tana karasawo ta bude gaban motar ta shige..hannuwansa ya bude alamar ta karaso ba musu ta shige jikinsa ya hadesu ya rungume yana shafa bayanta Hawayen farin ciki Amina takeyi yau gata a jikin mijinta kwance..dago kanta yayi ya share mata hawayen yabata light kiss a goshi馃おdadine ya ratsa jikin Amina dakyar ta bude bakinta ta gaisheshi ya amsa cikeda faraa ikhram ya amsa yanatayi mata wasa tanayi masa dariya kasancewar tafara wayau Hajiya ta fito bayi ta leka dakin Amina bata gantaba hijabinta tadauka ta nufi kofar gida taga ta inda zata bullo tana tsayawa kofar gida ta hangi Amina cikin motar Ahmad da sauri ta nufi motar Suna hangota suna faraarsu nanda nan annurin fuskar Ahmad ya dauke ya daura fuskarsa daidai jikin window ta tsaya tana kallonsu cikeda masifa tace fito Mara zuciya har kinfara kai kanki wajensane Mara zuciya....glass din motar Ahmad ya rufe yabarta tsaye su suke ganinta ita bata ganinsu Ya kara rungume matarsa da yarsa sunadan hirarsu tunda hajiya taga haka ta miki hanyar gida tanata sababin Amina ta wulakantata a gaban Ahmad tana matsar hawaye... Gab da magriba sukayi sallama da Ahmad ya bude mata mota daidai nan motar likita tayi parking a kofar gidansu Amina Ahmad yanaganin HK ya daura fuskarsa ya rike hannun Amina suka nufi kofar gidan Likita yana tsaye sukazo daidai inda yake da sauri likita ya mikawa Ahmad hannu ba musu suka gaisa likita ya kalli inda Amina ke rungume da ikhram yace dama yanzun nazo wajenki Ashe kinatare da bako Amina tayi murmushi tace ba bako bane mijinane uban ikhram halan baka ganeshiba shine yazo fa ya biya mana kudin Asibiti nan da nan likita ya kallo Ahmad yace tabbas naganeshi Ashe ka maida matarka malam Ahmad?murmushi Ahmad yayi ya CE ehh..likita yayi murmushi yace Allah ya sanya alheri"ameen Ahmad yace Jiki a sanyaye likita ya juya yadaga musu hannu yaja motarsa Sallama Ahmad yayiwa Amina yace saisunyi waya ya juya suka rabu cikeda kaunar juna **** Bayan sati daya Yakama yau sati da anty saudat da anty Sahura sunzo gida anty saudat tana dakin Amina suna magana akan kudin da anty Sahura zatabada gashi shiru bata badaba anty saudat tace ki kwantar da hankalinki dole tabada wanan kudin koda tsiya koda arziki...barima kigani insameta inyi mata mgna ta mike ta nufi dakin hajiya.. Da sallamarta ta shiga dik suna zaune ba Wanda ya amsa bata damuba ta zauna ta kalli Sahura da murmushi tace ya maganar kudin kayan Amina munji shiru Anty Sahura ta kalleta a wulakance tace karfi yaci...anty saudat ta saki dariya tace wlhy baki isaba kinyi kadan ki cuci marainiyar Allah nan hayaniya ta kacame sunata zage zage Ummar kaninsu dake kofar gida ya shigo gida da sauri yana tambayar ko lfy?anty saudat ta kwashe dik abinda yafaru tafadawa ummar Cikeda bacin rai ya kalleta a wulakance yace kinyi girman banza kin kashewa kanwarki aure kinciye kudin kayan daki to wlhy baki isaba dik abinda yafaru inasane lokaci nake jira da zan kwatarwa Amina yancinta SBD HK nabaki nanda jibi idan baki kawo kudin nanba wallahi tallahi wajen yan sanda zankaiki idan yaso dik abinda zaifaru yafaru dik abinda kikeyi mijinki besaniba to idan nakaiki wajen yan sanda zaisani kome zaifaru yafaru nafada miki kwana biyu nabaki yanagama fadan HK ya juya ya fice Jikin anty Sahura sai rawa yakeyi kmr tasaki fitsari saboda tsoro tunda ya ambaci police station ta rude inazatasamo kudi nanda kwana biyu? _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* Written by Meenaslimzy Dis page is for u *RUKAYYA* *ABUBAKAR* *KAUGAMA* *REEMAH* my one and only Luv u mean so much to me ILUSM馃槏馃槏 1鈨�0鈨�6鈨�-1鈨�1鈨�0鈨� Ba karamin tsorata Sahura tayiba dajin wanan magana da kaninta yayi hajiya ta kalla tagani ko zata dauki mataki taga hajiya batace komiba cikinta ya kara durar ruwa ba arziki ta shige dakin hajiya tadau mayafinta ta wuce gida cikeda fargabar ina zatasamo wadanan makudan kudade? ****** Washe gari umar ya shiga dakin mahaifinsu yafada mishi ya shirya kayanshi domin zai kaishi tashar mota ya nufi Lagos wajen yayyinsa yusuf da abubakar yadan huta sati daya ba musu yayi shirinsa tsaf ya shiga dakin hajiya yake fada mata zaije Lagos ganin su yusuf sati daya zaiyi....baki ta tabe tace Allah ya kiyaye hanya yace amin dahaka sukayi sallama yafita umar yakaisa tashar mota yasashi ya biya kudi sukayi sallama ******* Amina bakaramin kuka tayiba dataji cewa mahaifinta yatafi Lagos SBD befada musuba hajiya kawai yafadawa saida umar yadawone yake shaida mata dalilinsa Na turashi Lagos SBD yasamu damar yiwa Sahura rashin mutunci akan wadanan kudin SBD matukar mahaifinsu Na nan bazai bariba Lallashin Amina ya rinkayi ganin tanata famar kuka dakyar yasamu tayi shiru ******* Ahmad kuwa shirye shiryen komawar Amina kawai yakeyi SBD hankalinsa ya kwanta yasamu innah tadaina fushi dashi ya lallabi mahaifiyarsa ... ***** Washe gari da safe anty saudat ta iso gidan saboda ranar ne waadin da umar ya dibarwa Sahura yayi datazone Amina ke sanar da ita mahaifinsu yatafi Lagos batayi bakin cikiba murna tayi koba komi zaisamu kwanciyar hankali suna zaune suna breakfast umar yayi sallama ya shiga bayan sun gaisane yake shaida musu yakai report wajen yan sanda zaa kira Sahura akan mgnr kudin nan sanan ya fada musu suyi mata hukunci daidai da abinda tayi kada su Duba cewa yar uwarsace abinda yakeso a amsar ma marainiya hakkinta Murmushi anty saudat tayi tace hakan yayi yanxun yaushe zamuje station din?yace karfe biyu yanzundai sunce zaakai mata takaddar kara....dik yadda akayi zanzo intafi daku kuzama cikin shiri "****** Anty Sahura tunda ta tashi da safe ta shirya yara suka tafi makaranta takasa zaune takasa tsaye saboda tunanin bashin dake kanta Na mutane gashi Dan uwanta Na shirin tona mata asiri akan kudi,saboda kudin anty Kk takasa zaman gidan saboda tasan jarabarta zata yaga mata mutunci anty Kk bata kyale kowaba akan kudi... Tana wanan tunanin ne taji sallama a kofar gida hantar cikinta saida ta tsarga jiki Na rawa ta mike tasa hijabi ta fita...tana fita taci karo da Dan sanda a kofar gidan kafafuwanta kasa daukarta sukayi tsoro ya ziyarci zuciyarta zubewa tayi kasa tace ranka yadade Dan Allah kada katafi dani kayimun rai aurena zai mutu.... Daka mata tsawa Dan sanda yayi yace banzo tafiya dakeba nazone inkawo miki takaddar kara daga wajen yan sanda anason ganinki nanda awa biyu idan bakizoba xamuzo da mota mutafi dake yanagama fadan haka ya wurga mata takadda ya juya yatafi..... Kururuwa tafarayi tanafadin tashiga uku ta lalace ta rushe da kuka ta kwasa da gudu tayi cikin daki kamar zautacciya nanda nan ta shirya ko wanka batayiba ta nufi police station... ******* Umar Na kwance a dakinsa bayan azahar aka kirashi a waya daga wajen yan sanda akan wadda ake tuhuma tazo...ba bata lokaci yace gasunan zuwa ya shiga gida yafadawa anty saudat su shirya sutafi Sahura Na police station ikhram ta Goya Amina tasa hijabi suka fito ko kallon kofar dakin hajiya basuyiba suka fice daga gidan... ******* A police station Sahura Na zaune sai rarraba idanuwa takeyi tana zaune akan benci su ummar suka shigo dasu Amina... Sai kallonsu takeyi da fuskar tausayi ba Wanda yabi takanta office din DPO suka shiga suka zauna aka umurci wani Dan sanda ya shigo da Sahura ba musu aka shigo da ita Nan DPO yafara karanto mata dalilin dayasa aka kawota sanan ya tuhumeta da kudin kanwarta da akace tafito dashi taki hakane?tace ehh yace zasu sami kudin ko yaya tace babu....tanada kaddarar da zata biya?""babu saidai kayan dakina""DPO yayi rubuce rubuce ya bawa wani Dan sanda dokar sujeda Sahura a samu dillalai a siyarda kayanta idan sunyi daidai da kudin Amina shikenan idan basuyiba dole ta nemi ciko awa biyu aka basu... Kuka Sahura ta rushe dashi ganin an tasa keyarta zaaje a saida matada kayan datake takama dasu dik wasu kudi datakesamu a kayan daki yake karewa yau gashi zaarabata dasu kuka takeyi kmr ranta zai fita Dan sanda ya daka mata tsawa suka kama hanya...... Saida suka biya ta kasuwa suka dauki dilallai masu siyan kaya dik inda tabi kallonta akeyi kamar mahaukaciya ga Dan sanda Na biyeda ita dik ta fita hayyacinta...a HK suka so gida duka kayanta akasaida har gado da katifa ba Wanda aka bari siyan wulakanci akayi musu kudin ko Rabin Na kayan Amina basuyiba suka rufe kofa suka nufi police station..... Misalin karfe hudun yamma suka shiga station Amina da anty saudat Na zaune a benci suka shigo dukansu saida suka tausayawa Sahura ganin yadda ta fita hayyacinta tayi bakinkirin.... Suna shiga office umar ya mike ya bisu yabarsu anty saudat zaune Kudin hannun Sahura DPO ya amsa dubu Dari ne basuyi kudin Amina ba ya amsa ya mikawa umar sanan DPO yace yanason ya rokesa alfarmar suyafewa wanan baiwar Allah wanan kudi saboda batada hanyar samun wadanan kudade kuma be kyautu ace matsayinsu Na hausawa su kulle yar uwarsu saboda kudiba suyafe mata nasiha sosai DPO yayiwa umar ba musu yace sunyafe ya amshi wanan ya fito a kofar station yasamu Amina da saudat ya shaida musu yadda sukayi Ba musu Amina tace hkne tayafe tajeda halinta suka kamo hanya sukatafi gida ****** Bayan magriba mijin anty Sahura yadawo yana bude kofa kansa yafara juyawa ganinta zaune a tabarma itada yara dik ta fita hayyacinta da Sauri ya shigo palon yana tambayarta lafy?kuka ta rushe mishi dashi saboda batada amsar da zata bashi.....yana cikin tambayartane suka jiyo hayaniya ana shigowa cikin gidan.... Hantar cikin sahurace takada domin tagane me wanan muryan anty Kk CE tashigo da yaranta samari marasa mutunci jikintane yafara rawa.... Palon suka shigo da tsiya anty Kk tafarada cewa"kudina Nazo Na ritsaki in amsa saboda naji labarin kanwarkima kin cinye mata kudi kunje wajen yan sanda ansaida komi naki anbiyasu to wlhy dik inda kudina yake kifito mundashi ko insa wadanan yaran su nakada miki duka... Kasa magana Sahura tayi jikinta sai rawa yakeyi....mijinta dake tsaye zuface take keto masa ta ko ina dayaji furucinda anty Kk tayi...kallon mamaki da tuhuma yakeyiwa Sahura saboda yakasa magana.... Anty Kk tayi tsalle cikeda rashin mutunci ta cakumo wuyan Sahura kibiyani kudina ko intona muku asiri a cikin unguwa....da sauri mijin anty Sahura ya kalli anty Kk yatambayeta a ina taji cewa ankai matarsa wajen yan sanda Nan ta kwashe dalilin dayasa aka kaita wajen yan sanda da sanadiyyar mutuwar auren yar uwarta datayi tafada mishi karya da gaskiya bakaramin bacin rai yayiba yana huci ya kalleta yace kinci amanata babu abinda Na rageki dashi kwadayi da son abin duniya yasa kin jefa kanki a halaka Toni bazakisa mutuncina ya zubeba zankwashi yayana inkaiwa uwata kije Na sakeki saki uku.......yana gama fadin haka ya tattara yayansa yayi gaba dasu yabartanan tanata kururuwa..... Anty kk tasaki shewa tace burina ya cika mijin naki da kikewa mutanen unguwa iyayi akansa da rashin mutunci da nuna kewatace toya sakeki saura kudina da zaki biyani..... Harara Sahura ta gallawa anty Kk tacigaba da kuka aikuwa bata gama hararataba anty Kk ta rufeta da duka tana cewa baki bani kudinaba kina harata saboda bakida mutunci?umarni anty Kk tabawa yaranta suka nadawa Sahura duka suka fice a gidan sukabarta rai a hannun Allah..... _Meenaslimzy_ [07/08 11:10] pretty: *馃け馃徑馃け馃徑馃け馃徑DAGA WANKAN GIDA馃け馃徑馃け馃徑* *END* Written by Meenaslimzy Dis page is for u my habibty *JAMILA* *YUSUF* *Maman* *hajiya* ILUSM鉂ゐ煒� 1鈨�1鈨�0鈨�-1鈨�1鈨�5鈨� Da safe Sahura ta samu ta tashi dik da ciwon jiki dakyar taja jikinta ta sanya hijabinta ta fito bakin titi fuskarta dik a kumbure kamar tayi hatsari...dakyar tasamu abin hawa ta nufi gidan hajiya... Hajiya Na zaune tanajin yar radiyonta Sahura ta bude labule.... Wani zabura hajiya tayi ta mike tana kallon Sahura, Mezan gani haka yan fashine suka shigo miki gida? Kuka Sahura ta rushe dashi tanafadin hajiya ya sakeni saki uku, Hajiya ta Dada zabura waye ya sakeki?babansu sadik ne ya sakeni hajiya saboda yaga banida komi yanxun ya kwashemun yara yatafi da su nan Sahura ta kwashe dik abinda yafaru tafadawa hajiya harda zuwa police station da sukayi da zuwan anty Kk gidan... Hajiya tace yanxun dama Sahura kincinye kudin yar uwarkine yasa kika kasa zaune kika kasa tsaye?gsky baki kyautaba, Shi kuma ummarun saboda beda mutunci ya daukeki yakaiwa yan sanda meyasa besa sun kashekiba SBD kinci kudi kudin banza kudin wofi ki kwantar da hankalinki kinji muyi zamanmu tare a nan share hawayenki Kuka sosai Sahura takeyi me cikeda nadamar abubuwan data aikata a rayuwarta yau ga yadda takasance da ita.... Kukan da Amina tajiyone dakin hajiya ta fito tashigo tana tambayar lafiya? Turus tayi ganin anty Sahura tanata rusa kuka fuskarta ta kumbura jini dik ya kwanta mata a fuska kamar tayi hatsari da tsananin mamaki take kallonta tace lafiya? Hajiya ta amshe zancen da cewa""munafuka dik bakune kukayi sanadiyyar mutuwar aurentaba kuka hada baki kuka kaita wajen yan sanda to gashinan mijinta yayi mata saki uku saiku zuba ruwa a kasa kusha Bakaramin tausayawa Sahura tayiba ganin yadda lokaci daya takoma kmr almajira dik ta susuce fuska a kumbure kamar tayi hatsari dakyar Amina ta bude baki tace Allah ya kyauta gaba Hajiya tace munafuka yama kyauta, Amina ta juya tashige daki tana shiga Ahmad yakirata suka sha soyayyarsu a waya yana jadadda mata saura kwanaki sucigaba da rayuwa,insha allahu zaizo da gamma ****** Umar ne ya shiga wajen Amina suka gaisa yake fada mata ga kudi yayyinta sun aiko dashi daga Lagos suje suyi siyayya da anty saudat cikeda farin ciki Amina tayita godiya kudine masu yawan gaske yabata yace shi zaitafi kasuwa.... Yana fitowa Amina takira anty saudat a waya tafada mata, Ba bata lokaci ta iso gidan datazone Amina kefada mata ga yadda akayi mijin anty Sahura yasakota tabe baki tayi tace Allah ya kyauta da xasu fita suka leka dakin sukace zasuje kasuwa siyayya ba Wanda ya tanka musu suka tafi ******* Bayan sundawo kasuwa ne akayita shigo da kaya gida hajiyace take mamakin iyayen kaya da suka siyo kasa hakuri tayi tace ina kukasamu kudi HK?anty saudat tace yusuf da abubakar suka aiko da kudi Hajiya tace lallaine kawai ta juya ta shiga daki, ******* Da yamma Ahmad yazo Amina tafita suka sha hirar soyayyarsu shida matarsa yake kara jadda da mata yanda yake kaunarta da yarsa Ahmad yayi kyau yayi kiba sosai SBD samun kudi dayakeyi kasuwa ta bude sosai... ******* Bayan sati daya Yau Yakama Amina zata tare a gidan mijinta ba Wanda yakaita farin ciki Allah ya cika mata burinta tun sassafe suke shiri anty saudat tun safe taxo sun shirya kaya tsab Ahmad suke jira dik abinan da akeyi Sahura da hajiya suna daki sunki fitowa... Karfe sha dayan rana Ahmad yazo da mota shida kannensa sumayya da Zahra da murna suka shigo gidan suna farin cikin ganin anty Amina itama bakinta yaki rufuwa ganin kannen mijinta su suka tayasu fitada kaya suka kwashe tas... Amina ta shiga yiwa hajiya da Sahura sallama ba Wanda ya kulata da kuka ta fito daga dakin Ahmad yace ke kuma kukan me kikeyi? Bakomi tace ta shiga mota suka kama hanya... Unguwarsu ta da suka shiga amma ba bangaren da suka zaunaba GRA din unguwar suka nufa daidai wani gate coffee colour yayi parking Amina cikeda mamaki take kallonsa ganin hadadden gidan da sukazo Cikeda faraa yake kallonta sanan yace"wanan gidan namune halak malak batasan lokacinda ta rungumeshiba ta manta da anty saudat dasu Zahra agurin murna takeyi harda hawayen farin ciki cikeda kunya yasaketa ganin anty saudat a wajen Kallonta yayi yace tun lokacinda kika haihu Allah yabani iko Na siyeshi inata gyara a hankali...dukansu suka shiga cikin gidan.. Suna shiga suka tarar da zainab da rabiah sun shirya komi cikeda farin ciki suka amshesu kmr wani Abu be faruba... Bayan sallahr laasar aka gabatarda walima ta murnar sabon gida da tarewar Amina akayi akasha aka watse kowa Na sanbarka... ******* Sahurace zaune a kofar daki hajiya ta fito da tulin wanki ta ajiye mata... A wulakance ta kalli hajiya dik tarame tayi baki tacewa hajiya mekike nufi da wanan kayan? Hajiya tace wankemun zakiyi, Sahura tace kinbani kudin sabulune da zakice inyi miki wanki to bazanyiba kada kidameni Hajiya ta kalleta tace Sahura kada kimun rashin kunyafa, Idan nayifa mekika isa kiyi tsohuwar banza kawai,""nikike cewa tsohuwar banza to wlhy yau saidai ki nemi me baki abinci dik nagama kashe kudadena a gunki me halin banza kawai... Dariya Sahura tayi tace tare mukeyi, Kuka hajiya ta fashe dashi ta shige dakinta tahau hada kaya zata tafi kauye can ta zauna tunda Sahura babu abinda takeyi mata sai rashin kunya... ******** Kayanta ta hada takoma Zaria can tacigaba da zama babu me kulawa da ita dik ta lalace tafara yawon Neman kwalabe... Garin Neman kwalabene mashin ya bigeta ta karye a kafa akadawo da ita gidanta bame kulawa da ita Makociyarsuce ta shirya tazo ta sanarda Sahura halin da hajiya ke ciki tace itama bashi garetaba yawon wanke wanke takeyi wajen masu abinci HK takoma Zaria jiki a sanyaye hajiya ba kafa komi a zaune takeyi yar makociyarsuce ke shigowa tayi mata shara da Dan wanki saidai hajiya tayita kuka... ******** Babansu Amina kuwa yayi kyau yasamu jin dadi yayansa Na kulawa dashi sosai yankiran Amina da saudat akai akai ******* Amina ta rike dangin mijinta da kyau sun shirya da surukarta suna zaune lafiya**** *ALHAMDULILLAH* Godiya ta musamman gareku: *HAUWAU MUAZU* *BILKISU BILYAMIN* *FATY DAN MALIKI* sanan inawa kowa fatan alheri Allah ubangiji yasadamu da alheri kurakuran danayi cikin labarin nan Allah ya yafemun wassalam Nice taku Amina jibril meenaslimzy 08166177830