[1/9, 2:46 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 HAUSA NOVELS SOKOTO WHATSAPP NO: 07068808039 ABDULMKIBAB.HEXAT.COM BY HAERMEEBRAERH *Assalamu alaikum warahmatullah, 'yan uwana makaranta, ga sabon novel mai suna 'YAR RAWA, zan fara, ina fatan zaku karbe shi, ku bini kamar yanda ko fiye da ku kaima novels dina na baya, ina roqon Allah daya sanya albarka a ciki, ya bani ikon rubuta daidai, duk abinda zan fada in ba zai zama alkairi garemu duka ba Allah ya karkatar dani da barin shi, Allah ya yafen kurakuren da zan yi har i zuwa qarshen kammalawa. HAERMEEN HAERMMAERH NA SON DUKKAB MASOYAN TA DA MASOYAN NOVELS DIN TA DUK INDA KUKE, ME LOVE U XX❤* " Sannu Tabawa, Allah zai baki lfy, da kan ki za ki reni abinda kk haifa, shi ciwo ai ba mutuwa bane" Yana fada yana share kwallar dake maqale a manyan idanun shi, shigowar yar budurwar yarinyar su da bazata wuce shekaru sha 12 ba, ne yasa Tabawa ta daga kai da kyar ta kalle ta, miqa mata hannu tai akan ta isa gareta, da kyar cikin azabar ciwo da kanta yake mata, tare da zafin da take ji a qirjin ta, wanda ji take kamar hucin garwashin wuta take fiddawa, ta fara magana, bayan yarinyar ta bata ruwan da ta debo mata," Ameenee,..... ki ji tsoron Allah a duk inda kk,.... ki ma mahaifin ki biyayya, shida abokiyar zamana,....ki kasance yarinyar kirki da kowa zai sha'awar zaman ki tashi...... ki kiyaye dokokin Allah Ameenee.... Allah zai kiyaye ki da zuri'ar ki har qarshen rayuwar ki,.... Malam ka riqe amanar yarinyar nan,...... kar ka bari a cutar mana ita...... ka saka ta tai ilimi.... domin kai mai ilimi ne....." tari ne mai qarfi ya sarqe ta, yi take ba qaqqautawa, cikin tashin hankali, Malam Muhammad ya miqe ya dakko ruwan zai bata, sai yaji diyar su Ameenee, tana kalmar shahada,mahaifiyar ta na mainaitawa, idon Ameenee na zubar da hawaye, kamar an bude famfo, Malam kasa motsi yar, ganin dagawar da girjin matar shi yai, tare da jan wani nunfashi, ta kwanta, hannun ta Ameenee ta daga, ta ga alamar ya sake, kuka ta fara can qasan maqoshin ta, mara sauti, ta farama mahaifiyar ta addu'a" Ya Rab Ya ilahy, Allah ina roqon ka ka gafarta ma mahaifiyata, ka kai rahama qabarin ta, Allah ka tada ta cikin bayin ka muminai salihai, Allah ka bata ikon amsa tambayoyin qabari," Malam Muhammad da yai mutuwar durqushe ne , kama kanshi yana juya shi, hawaye masu mugun zafi, suke fama kwarara a idon shi, amsa addu'ar diyarshi yai wadda gaba daya bai san me take cewa ba sai daga qarshe ya fahimta, qanqame matar tashi yai kamar zai maida ta cikin shi, hawaye ke zuba, cikin ranshi yana nema mata rahamar Allah, daga baya ya sake ta ya kwantar da ita, ya rufe mata ido, sannan ya lullube ta da abin rufar da ta rufa da shi, tashi yai ya fita tsakar gidan nasu, wata gambasheshiyar mata na gani tana ma yaran ta wanda suke dika maza magana,akan suyi su gama cin abinci su debo mata ruwa, turo baki suke suna su ba inda za su, ganin malam ya fito cikin tashin hankali fuskar shi duk hawaye yasa ta qarasawa wajen shi da gudu2 sauri2, daurin qirjin ta na rai da rai na neman faduwa, ta damqe shi, " Delu, Allah daya ban tabawa ya fini son ta, a yau ya amshi abar shi,ta tafi ta barnu cikin kewar ta, da quncin zuci, wannan qunci daja shiga ban san ranar fita ba Delu" wani tuquqin baqin ciki ne ya tokare mata wuya, jin kalaman shi, amma dake makira ce,sai ta fake da kukan mutuwar da taji ta saka hannu a ka ta kurma ihu ta fadi qasa dabar, tana turje2n kafa da hannaye, tare da cire dankwalin ta kanta da ya cure dan datti ya bayyana," wayyo ni Delu na shiga ukuna, na rasa 'yar uwata, mai sona da qaunata, Tabawa kar ki tafi ki bar mu, muna tsananin son ki, ki yafe mana laifin da mukai maki" Malam ne ya sunkuya ya daga ta, yana qara jin wanu tausayin kansu dika, dan rasa mace kamar Tabawa babban asara sukai,mace ce mai kunya, kawaici, tsafta, rufin asiri, da kuma juriya da hakuri, ga rufa asirin mijin ta, in basu da shi zatai duk qoqarin ta tai providing masi kamar itace mijin, daga mijin har kishiyar tata suna morar ta ba ladan ba, ya fifita ta da kowa a zuciyar shi fiye da kowa, ya bata mazauni mara misalin fada a cikin zuciyar shi da ruhin shi, ta zama wanu bangare na jikin shi, lokacin da sukai aure suka dare basu haihu ba, ita ta matsa mai ya auro Delu, tana zuwa ta fara da haihuwar maza, taso ta fito da iskancin ta fili Malam yai mata barazanar saki, ko nace ya sake ta ma, amma dake Tabawa mutuniyar kirki ce ta bashi hakuri, ta fada mai duk randa ya saki Delu itama ta bar zama da shi kenan, hakuri ya bata suka je ita da shi suka dawo da Delu,kowa na mamakin hali irin nata na kyautayi da kyautatawa, dan haaka sai ita Delu ta fara yi mata kisan mummuqe, a haka har sai da ta haifi yara biyu maza, masu suna Habeebu da Hamza, sannan Allah ya azurta, Tabawa da cikin Ameena, wadda ta sha gata wajen malam, kamar mai sabuwar haihuwa, hakan ne ya qara dasa qiyayyar Tabawa da duk abinda zata haifa a ran Delu,tayi iya qoqarin ta na ganin ta zubda cikin amma Allah bai bata dama ba, ran da kuwa taga mace aka haifa tai rawa tai juyi a daka tana waqoqin samun nasarar kasamcewar yaranta maza kuma sune manya, a haka rayuwa ta ci gaba sai ta dauki Ameenee da niyyae raino da ta kauce tai ta mata azaba, tana kuka, sai tace daga dan matsawa yara suka dake ta, ta hau sababi ma yaran, in Tabawa ta karbe ta tai ta mata fadan dan me zata ma yara fada, suma ai qanana ne,haka dai har Ameenee ta girma ta gane halayen Delu tsaf, mahaifiyar ta bata gano ba, Malam ma haka, ran da ko ta sanar ma da mahaifiyar ta ta sha duka sosai, a haka ta ja bakin ta tai shiru, dan yarinya ce mai biyayya sosai. Daga ta Malam yai ya gyara mata zanin ya miqa mata dankwalin ta yana mai lallashin ta, daki ya kaita, ya miqo mata rigar kayan akan ta saka da hijab, ta saka tana wanai kuka kamar na gaske, can qasan ran ta kalaman da ya fada suna qara yunquro mata kamar kumallo. A haka aka gyara Tabawa akai mata wanka da sallah aka kaita gidan ta na gaskiya, Ameenee ta sha kuka tin tana iyawa har taji ba zata iya ba, daki ta koma ta kwanta inda Innar ta ke kwanciya,ya rungume filo tana hawaye, addu'a take ta mata a ranta ta samun rahamar Allah. Bayan an yi sadakar arba'in ne na rasuwar Tabawa, komai jin shi suke ba dadi, tsakanin Malam kenan da Ameenee, wadda Delu ta mayar baiwa,a bayan idon mahaifin ta, amma in yana nan, har rungumar ta take a jikin nan nata mai dankaren tsami, tana nuna mata kulawa,dan haka suke qara bama Malam tausayi, in ya fita tun safe sai dare, baya jure ganin su cikin quncin da shima ya addabe shi, hakan ne ya ba Delu da yaran ta damar musgunawa marainiyar Allah, ga horon yunwa, da ya dawo sai kuji tana" zaki qara abincin ne Ameeneenaa, na kula ba ki son cin abinci, ki taimake ni kina ci, dubi yanda kk rame? Mutuwar nan duk muma a cikin dacin ta muke...." sai ta kasa qarasawa ta hau kuka, Malam ne zai rarrashe ta, ya karbi dan abincin ya ba yar tashi, ta wuni da yunwa amma gudun kar ya gane komai, dam an mata warning mai girma akan kae ta bari ya gane daidai da rana daya kashin ta ya bushe, daki take komawa ta hau ci kamar mahaukaciyar data shekara ba abincin, tana ci tana hawaye. Mai gari ne yace a kira Malam Muhammad, sabida ya ga tunda akai rasuwar ya daina hada2r shi na Islamiyyun da ya taimaka aka bude a qarin nasu na Rimin Gata, hakuri ya ba mai garin, ya kuma tabbatar mai zai koma normal, daga wannan satin. El- mustapha Sadauki, wani shahararren mutumi ne wanda yake da arziqi da taimakon gidan marayu,da islamiyyoyi, yau qungiyar su ta baro qasar su dake Niger, ta taho Nigeria, domin taimakawa, islamiyyar da malam Muhammad ke jagoranci, ya samu labarin qoqarin shi ne, ta bakin wani mai masa hidima, a nan Nigeria, dan yana da masu nemo masa rahotanni a qasashe don ya samu damar taimakawa. El-mustapha yana da nasaba da kuma jinin larabawan Dake da mazauni a Dubai, garin tainakon shi ne yasa ya baro qasar shi ya kafa gidauniya anan Niger, wanda da dawowar shi da komai bai fi shekara biyar ba kenan, ya samu tsananin qiyayya daga 'yan uwan shi na can, wadan da ba su qaunar shi ko kadan sakamakon son talakawa da yake da, rayuwar shi daban da tasu, ta dalilin haka ne ya tattaro ya dawo, iyayen sun rasu. Dawowar shi nan bai sa ya yanke alaqar shi da su ba, yana zuwa a kai akai, dan sada zumunci, gaba daya hakan da yake yi ji suke kamar su kashe shi su gaje dukiyar shi, tinda yaqi auren 'yayan kowa a qasar yace bai ga wadda ta mai ba, yana son yarinyar da zai aura ta kasance daga gidan tarbiyya, da mutunci, amma fa talaka, wannan kalmar qarshen ta baqanta ma yan uwan shi ba kadan ba, a haka suke har yau da yashirya zasu so Nigeria, sannan Unguwar Rimin Gata, kuna gidan Malam Muhammad mai Islamiyya...... *Hello guys, can u pls do me a favor? Ku dan aje wannan page a wani wajen, yanda koda nai nisa kunji sha'awar bi na sai ku lalubo ku karanta,ba sai nai nisa kuna tambaya ba, wayata yar qwaya ce,lols😉 ta yi nauyi da yawa, saboda abubuwan da take dauke da shi, ba zai yu na dinga sendin abu mai yawa ba ba tare da tana riqewa ba, so pls ku na adanawa, Thank u* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH page 2: Sun iso a gajiye, inda suka fara isa gidan mai garin, suka gabatar da kansu da dikkan bayanan abinda ya kawo su, nan take mai gari ya aika a kira Malam Muhammad, domin bangaren shi ne, isowar shi keda wuya, suka gaisa sannan aka qara kora mai jawabin komai, godiya ya musi mai tarin yawa, sannan ya nemi izinin tafiya da su masauqin da yakan aje baqi in sun zo, tashi sukai suka isa gidan Malam din, daidai lokacin Ameenee ta fito wanka tana shiryawa, kiran ta Malam yai ta je tare da durqusawa, " Abba gani" " Ameenee je ki dauko mazubin ruwa mai kyau da tsafta ki debo ruwan sha mai sanyi na randar gefen madafi ki kai wa baqi a dakin baqi, sai ki dawo a kai masu abinci kinji?" Amsawa tai da " To Abba" sannan ta miqe ta tafi ta qarasa saka riga da skirt din ta na atampa, ta dora hijab din ta akai, saboda Allah ya mata halitta mai kyau da diri, wannan dalilin ne yasa bata ta'ammili da mayafi. Sallama tai cikin muryar ta mai sanyi, kanshi a duqe yake a hankali ya dago dan ganin mamallakiyar wannan daddadar muryar, kallon ta ya tsaya yana yi kawai yana mamakin samun yarinya mai kyau a cikin Africa kuma a Nigeria, Nigerian ma a kano, lumshe idanun shi yai da suke madaidaita da cikar kyau ya amsa sallamar ta, ruwan ta miqa mai ya karba ta gaida su, cikin hausar shi da ba wani ji yake ba sosai, ya amsa, miqewa tai ta tafi ciki ta qara dawowa dauke da abincin da ita ta dafa, taliya ce mai mai da yaji, sai maggi da aka bada mata? Irin taliyar murjinnan ce, amma tai wara2 kamar ba ta murji ba, sannan Malam ya siyo kifi manya aka dora musu akai, a da da aka kai El-mustapha sadauki ya fara ganin anya zai iya ci? Kawai a dakko mai abincin shi a mota ya ci, sai kuma zuciyar shi ta raya mai ya tambaye ta. " Yaya sunan ki?" Murmushi tai dan jin hausar shi, ta amsa mai da" Suna na Ameenaa" " Malama Ameena ana zuwa makaranta kuwa?" " Eh ina zuwa, dan na sauke alqu'ani da shekara goma, da sauran littafan addini, yanzu ma ina taya Abbana koyar wa a wasu daga cikin ajujuwan da suka rage ba malamai" " Masha Allah" shine abinda ya fada cike da jin dadin tabbas abinda yake ayyanawa zai tabbata da yardar Allah, " Malama Ameenaa kin iya girki ne?" Ya tambaye ta da alamar zolaya, amma ti be honest yana son jin wa yai girkin ne, cikin jin kunya da. Sadda kanta qasa ta amsa mai da" Eh, ni nake girki dama" godiya ya mata yace ta je, miqewa tai ta fita, ya hango yanda jikin ya ke ta cikin hijab, ya tabbatar an yi halitta a wajen, dakko kwanon yau ya fara ci ba sai ga El-mustapha ya tashi da taliya da manja ba😂fadi yake lallai, Bahaushe akwai hikima...... ( Ana kiran shi da Sadauki ne saboda jajrcewar shi wajen taimakon al'umma duk rintsi duk wuya, sannan duk nisan gari da surquqin qauye zai shige shi, amma asalin sunan shi shine El-mustapha Ahmad Nabeel.) Sun kammala dukkan abinda ya kawo su, a cikin kwanakin nan ba qaramin shaquwa da sabo ne ya shiga tsakanin shi da Ameenee ba, duk da cewar, bqi taba furta mata kalmar so ba, amma soyayyar ta ta gama da dukkan jiki da ruhin shi, ita kuma a nata bangaren bata san me ne ne take ji game da shi ba, all she know is that in ya tafi she will miss him alot, and she don't even want him to go. Samun kan ta tai da shiga damuwa a duk sanda ta tina sallamar da sukai daran jiya, Delu kuwa hankalin ta ya fara kwanciya dan jin za su tafi, dan ta kula da take2n El-mustapha, wanda taci alwashin ko zata mutu bazata bari ya aure ta ba. Shi da malam ne suke ban kwana a dakin da aka sauke su, anan yake shaida ma Malam manufar shi, Malam yayi farin ciki sosai, inda yace ai wannan magana ya kamata mai gari ya jita, dunguma sukai can wajen mai garin, a gaban su ya rabbatar ko bayan ran shi suka dawo batun auren Ameenee a aura mai ita, godiya yai mai yawa suka wuce Nijer. Tafiyar shi da kwanaki ne malam ya hau rashin lafiya a tsattsaye, wata rana ya tashi ya tafi fadar mai gari ya same shi daga shi sai mai garin yace mai " ranka ya dade ina neman wata alfarma, ina son ko bayan raina in yaron nan ya dawo ku taimaka, ku bashi auren Ameenee, dan na yi alqawari bana son na mutu ban cika ba kuma ba a cika min ba, na sanar da Abubakar amini na shima hakan," " Hab Malam Muhammadu, ai ciwo ba mutuwa bne, in Allah ya so da kan ka zaka aurar da Ameenatou" kada kai malam yai yace " Kayya ranka shi dade ni na san me nake ji kawai a zuciyar nan tawa, na kasa cire tinanin margayiya a raina, da zan iya da nayi na huta, amma zuciyata kamar ta rabe gida biyu nake ji" ya qatasa yayin da wata qwalla ke bin fuskar shi, gogewa yai, a lokacin da mai gari ke ta kwantar mai da hankali tare da mata addua, godiya yai ya tafi gida, ba ai sati ba Allab yai ma Malam Muhammad cikawa, sakamakon ciwon zuciyar da ke damun shi, Ameenee tai kuka sosai kamar ranta zai fita, in da Delu kam da yaran ta sun yi kuka na ranar daga baya suka shiga harkokin su, jira kawai take ai arba'in a raba gado. Bayan an dan kwan biyu ne ya tattara ya tafi Dubai don sanar da 'yan uwan shi batun auren shi, sannan da gayyatar su zuwa auren nashi,fafir suka mai rashin mutunci,suka nuna su fa ba zasu tako qafafun su garin takakawa ba, masu qaramin qarfi, ya buga ya raya, amma fir suka qi aminta, yai kuka yai kuka har yaji ba dadi, take kewar mahaifan shi ta addabe shi, tabbas da suna da rai da hakan bata kasance ba, ya sani ko mahaukaciya ya nuna zai aura ba zasu qi ba,balle mahaddciyar qur'anul kareem, share hawayen shi yai ya aje masi doguwar takadda da wasu daga dukiyar da Allah ya bashi, yai umarnin su raba a tsakanin si, sannan ya tafi ya koma Niger, bayan ya iso ne ya samu wani daga abokin shi, da suka zama kamar yan uwa, wani hamshaqin mai kudi ne shima a nan qasar, ya roqi arziqin zuwa ya zama waliyyin shi, a haka suka iso Nigeria. Tana gaban murhu tai budu2 da hayaqi ne taji Sallamar shi, tabbas ba zata taba rasa gane muryar shi ba, hijab din ta ta dauka ta fita da sauri, tana ganin shine, ta durqusa a wajen tana kuka, ita kanta bazata ce kukan meye ba ne, kukan maraicin daya mamaye ta ne da shekaru qananan da ba zata wuce sha uku sha hudu ba a yanzu? Aa ko kukan murnar ganin shi ne? Itama ba zata tantance ba, durqusawa yai gaban ta shima, ya qurawa zara2n gashin idon ta da suke a lumshe idoj na zubar da hawaye ido, " Meenaa, me ya faru, ko baki son ganina ne na koma" da sauri ta daga kai ta girgiza kanta, " Abbana ya rasu bayan tafiyat ka" cike da tashin hankali ya miqe yana baya, idon shi nan da nan suka kada sukai jawur, " Ameenee saboda tsabat iskanci da tsagwaron tijara na saki aiki ki aje ki tafi yawon iskanci, dan najiyo muryar maza, wane ne yazo?" Tana tozali da shi tashin hankali qarara a fuskar ta, to in ma ta bar wannan ya zo ya dauke mata Ameenee gadon ta da ta lissafa za ta sake kayan daki da sho uban wa zai bata? Sannan wa zai ci gaba da mata ayyukan gidan? " ke dawo baya wannan dan rainin ne yazo, ba sallama da manya kawai sai kazo ka tasa yarinya qarama a gaba da zance? Kai kuma na gefe waye kai, ka tsaya ka tsare ni da ido?" Duqawa El-mustapha yai har qasa idon shi na hawaye, dan tunawa da nagartar Malam Muhammad da yai, ya gaida ta ya mata ta'aziyya, shima haka abokin shi mus'ab yai, a kaikaice ta amsa tana kada qafa, " ke ! Wuce ciki ki qarasan abinda kk yi tin fari" miqewa tai tana waiwayen shi, kada mata kai yai alamar karta damu yana nan ba inda zai je, wani dadi ne ya lullube ta tai ciki da gudu, ta je nan da nan ta hau girkin ta gama, tai wanka ta shirya cikin doguwar rigar atampa, bunjimemiya, ta dora hijab, ta zauna tana bitar katatun ta, ita kuma iya masifa ta kasa zaune ta kasa tsaye, sawa tai yaran ta suka kira bappanin su, tace tana son magana da su, nan da nan ko suka taru. Shi ko yana tashi wajen mai gari ya nufa,ya sanar da shi ya dawo kuma a yau da yamman yake son a daura masu aure gobe ya wuce da matat shi, dan yanda ya tadda ita ya tabbatar tana cikn wahalar matar uban ta, mai gari bayan ya amsa gaisuwar da ya masa ya tabbatar masa da cewar za ai yanda yake so din da zarar an dawo daga sallar la'asar dan sauran mintina kadan a yi ta, aikawa yai yace a gaya ma bappanin ta in an yi sallah su hallara auren Ameenee....... *To pah makaranta, anya kuwa auren nan zai yu kuwa,tinda Delu ta murza kanbun mugunta tace ayi mu gani🤔* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Page 3: Dakin Delu suka shiga suka zazzauna, ta je ta debo masu abincin da Ameenee ta dafa, da ruwa mai sanyi, rabon su da cin abincin gidan dan uwan nasu tun zamanin Tabawa, shekaru biyu kenan, amma yau har da ruwan randar sanyi, tasa daga yaranta suka siyo mata balangu ta watsa masu akai, aiko kamar mayu haka suka hau abincin da ci, ga shi dama Ameenee a yan shekarun ta ba dai iya girki ba, tunda kullum ita takeyi, na safe , na rana, na dare, duk itace dole ta kware. Bayan sun kammala ne ta daya daga cikin su mai suna Bappa Lado wanda yafi kowa baqar zuciya yace, "Delu kin aika a kira mu ina fatan kiran mai amfani ne, dan ni kan na fito aike ya iskeni daga mai gari gaba dayan mu da yan uwana mu je fada akwai mahimmin abu daya taso, dan haka ina ganin ku da baku sani ba yanzu na isar muku, sai mu qoqarta mui hanzari mu kammala na nan mu je can muji me ya taso haka na gaggawa?" Gara zama tai ta ce " ba komai ne yasa na kira ku ba Lado face maganar auren yaeinyar nan da mai gari keson yi, ni fa ba na son marainiyar Allah ta bar gabana, ta bar garinnan kwata2,..... sai ta fara kukan munafurci harda fyace majina.... in ta tafi Lado ban san halin da take ciki ba akwai damuwa da zata sarqen, ina tsoron nima na rasa raina saboda rashin Malam da diyar shi, sannan mutumin nan da gani ba dan Nigeria bane, wa yasan sana'ar shi, kuma malam bai da rai bare ace ya tabbatar zai bada ita a yanzu, babban kuma wani abun dubawar yarinyar nan bata son shi, tana ganin shi ma kuka ta saka" tsagaitawa tai tana kuka sosai kamar na gaske, tausayin ta ne ya kama wasu daga cikin su, wasu kuma suna ganin anya??? Lado shi anashi bangaren ba ruwan shi da koma me zai sami yarinyar tinda Delu bata son auren to fa ba wanda ya isa daura shi, " kiran mai gari na da nasaba da zuwan yaron ya kamata ku hanzarta kar mai afkuwa ta afku, ku tai maken da yar ku da dan uwan ku" kuka ta qara sakawa mai cin rai ita a dole kar a cutar da marainiya, miqewa suka suka kama hanyar gidan mai gari suna tattauna yanda zasu bullowa lamarin. A fada waje ya cika ba laifi dan sanar da jama'a me za ai da me gari ya saka a yi, suna isa mai gari ya shigar da su wani daki, harda Aminin Malam wato Malam Abubakar, sai kuma su El-mustapha da Mus'ab abokin shi, zama sukai mai gari yai addu'a suka shafa sannan yace" Malam Lado na sa an kira ku ne da yan uwan ka akan batun auren Ameeaatou, meye ra'ayin ku akan wasiyyar dan uwan ku na a a aura ma wannan bawan Allah ita ko bayan ran shi?" " Ranka ya dade ni na ke bin tsohon wannan yarinya, nasan abinda yake so da wanda baya so, dan haka gaba daya wancan karon wannan bawan Allah tilasta mai yai akan ya aura mai ita,ba dan ya so ba ya amince, kan ya mutu ni da shi munyi wannan maganar," cikin kidima El-mustapha ya ja baya yana zare ido da dafe qirji kamar wata budurwar da ta shiga damuwa, yace" Malam Ka ji tsoron Allah, kaji tsoron ranar da Allah zai tsaidaka ka maimaita abinda kace, kaji kunyar ranar da zaka maimaita wannan qaryar gaban dan uwan ka, wannan abun da ka fada bai faru ba, ba a taba yin shi ba, yarinya bata taba cewa tana sona ba ni na ce ina son ta,amma da dikkan alamu itama tana sona, ni ban taba furta mata kalmar so ba, na kula qarama ce tai qanqanta da hakan, dalilina na zuwa nansamu mahaifinta kenan, dan hakan shine mafi dacewa, uba na da damar zabawa yarinyar shi mai auren fari miji, musamman wannan da bata san komai ba" sunkuyar da kan shi yai yana hawaye,badan komai ba ganin yau ba Malam Muhammad ana neman shiga tsakanin shi da abar son shi , baida kowa a duniya, ita yake saka ran ta zama mai komai, ta maye mai gurbin rashin iyaye da yan uwan kirki da yai, amma gashi komai na neman zama mai ba daidai ba, kafadar shi yaji an dafa da sigar lallashi, " ka kwakntar da hankalin ka, wannan aure kamar anyi an gama ne, ba wanda ya isa ya daga shi, domin kuwa ni ne aminin mahaifin ta.ni da shi ya tabbatar min ya baka ko bayan ranshi ka dawo ai wannan aure naku ga mai gari shaida n3 shima"mai gari ne ya qara tabbatar ma shi hakan shima,nan take kwanciyar hankalin shi ta bayyana " ammmm bayin Allah ban katse maku hanzari ba, amma in dai za ai auren nan ba yawun mu, ko shekara dari zamu sake.a duniya in dai akai auren nan ba mu ba Ameenaa ba zuri'ar ta, tinda mu yan uwan mahaifin ta an mai damu bamu da amfani," inji na Duduwalle kenan daya daga Bappanin ta, me gari ko sauraran su bai sake yi ba ya baza babbar rigar shi ua fito suma si malam Abubakar suka bi shi, nan take aka daura auren su, akan sadaki dubu 20k, cikin farin ciki, Malam Abubakar ne ya wakilce ta shi kuma Mus'ab shine ya wakilce shi, haka akai auren cikin saka albarkar mutane da yawa,kamar sun san za ai auren dama can yanda aka taru a wajen, fakam fakam fakam suka zo suka wuce suna huci, bayan an dunqula masu goro da alawa a ledoji, ba kunya suka amshe sukai gidan Delu, suna zuwa daga yanayin su ta gane an gama komai, hannu ta dora aka ta rusa kuka, " shikenan sun cuce ni sun cuci marainiyar Allah, in dai ina nunfashi yarin yar nan ba za ta bar gidannan ba, sun ganta marainiya za su cutar da ita?" Daidai nan su Malam Abubakar suka iso, " zamu cutar da ita ko kk cutar da ita kuma kk shirin qara cutar ta? Dwlu duk makircin ku akan idona kk aikata shi, tin fil azal, ki kiyayeni dan wannan karon ba auren aminina akan ki ba zan dau iskancin ki ba," " Malam Abu ka duba fa ka gani auren dole kuke son yi wa marainiya ko nace kukao ma marainiya"ta fashe da kukan baqin cikin halin hutun da ya zo wa Ameenee, ki ra Malam din yai ta banka mata, nan da nan ta iso da hanzari ta duqa kan ta a qasa, ta gaida su ta dada takurewa gefe, dan a yanzu duk ta fuskanci inda zantukan su suka saka gaba, " Ameenaatou, kina son wannan bawan Allah ko baki son shi, ki fadan gaskiya kamar yanda zaki fafa ma marigayi, ni ubane a wajen ki , ko da wadannan ubannin naki sun juya maki baya ni ina nan tare da ke har qarshen nunfashina" hawaye take sosai, na fahimtar kenan su Bappanin ta sun qi ta ne, gefen da gogan nata yake ta kalla qasa qasa, cikin sa'a idon su ya hadu, wani marairaice mata yai akan ta amince da shi, murmushi ne ya subuce mata shima hakan, ta qara sunkui da kai tana rufe fuska, malam ne ya ce" to Alhamdu lilLAAH ina ganin wannan kadai ya baku amsa dan haka Ameenee debo kayan ki mu wuce gidana da ke da mijin ki cam zaku kwana kafin tafiyar ku jibi, domin ni ba kowa garen ba kun sani iyalina ta mutu kuma Allah bai bamu haihuwa ba, akwai wajen da zai ishe ku ku kwana kai da abokin ka da iyalin ka, mu tashi mu wuce, ke kuma Allah ya shirye ki da ku baki daya ku gane meye ma'anar zumunci" Bappa Lado ne ya karkata baki yace" Ameeeen da bamu san akan me kk wannan rawar jikin bane da sai mu zaci kai ma dan zumuncin kayi" Malam bai kula shi ba, haka suka jira ta ta debo kayan ta suka wuce gidan malam din, daki daya aka ware masu mai katifa da ledar daki, shikenan sai dan bargo da zanin gado, anan aka sauke su, Mus'ab ma dakin nashi haka ne, bayan sun isa ne, El-mustapha ya sanar da malam gobe zasu wuce, malam ya musu fatan alkairi da addu'o'i Ameenee ta sha kuka sosai, inda tin yana lallashin ta shima ya saka mata kukan,tin da shima yau ce rana abar baqin ciki a tare da shi, yayi auren fari ba kowa na shi, ga matar da yake so itama tana cikin damuwar, rungume ta yai suka sha kukan su a hakan,. Washe gari su Ameenee an dau hanyar tafiya Niger, a hanya ta sha bacci sosai, suna isa gidan su kuwa Mus'ab ya musu sallama ya tafi gidan shi, shima, nan take ya aika da driver aka kai ma su abinci da abubuwan dai da zasu buqata a ranar, sannan ya aika wata daga cikin masu aikin shi, yar dattijuwa yace taje ta kula da Ameenee, ta kuma koya mata abubuwan da duk ya kamata ta iya, dan shi mai suna, Ameenullahi ne ke ta kuka, sai ya bi Iya gidan da zata dan sun shaqu sosai, hakuri ta bashi tace zata dawo nan da kwana biyar su tafi, Ameenullahi mai shekaru 6 a duniya ga wayo, yasan ba ta mai qarya sai ya hakura amma hawaye bai bar zuba mai ba, tafiya tai, aka kaita tana zuwa,ta isa inda Ameenee take ta kwashi gaisuwa, nan da nan Ameenee ta zube a qasa itama, ganin babbar mata da ta kusa sa'ar Innar ta tana duqawa tana gaida ta, gaisawa sukai a haka, El-mustapha da ya shigo ya gansu dariya ta kama shi, yai tayi kuwa, isa yai gabam Ameenee ya dago ta ta dan jamye kadan ganin wannan dattijuwa na wajen, sannan ya umarci Iyan da ta tashi, tashi tai ta zauna akan kujera kamar yanda ya umarta " da farko dai Iya wannan iyalina ce, sunan ta Ameenaatou, Ameenee wannan ita ce zata na zama dake musamman in bana nan, kuma kina buqayar wani abu duk zata maki, zata na taya ki ayyukan gida, ta koya maki abubuwan da baki iya ba, ina fatan ba matsala, ke kuma Iya daga yau kina dauki Ameenee kamar 'ya, sai dai kawai ba zan lamunci muzguna mata ko bata ranta ba a wajen kowa, dan wannan girman da kk bata ita ta taso gian tarbiyya ba zata so shi ba ina fatan kin gane" kada kai tai tare da godiya, ya nuna mata bangaren da zata zauna ya ja hanun iyalin shu suka tafi, a yau din komai ya wakana tsakanin shi da iyalin shi, wanda ya danganci amarci da raya sunnar ma'aiki, su Ameenee an sha fama da maza😱🙊 tayi kuka hr ta gode Allah sai da yace mat " in kina kuka Iya zata gane me mukai, ki shiru kae kowa ya ji, a maki dariya ke raguwa ce, in miji na ma matar shi haka lada suke samu, amma in wanda ba miji da mata bane zunubi suke samu, na san a karatun ki kin san hakan ai ko? Daga mai kai tai yace yauwa Habibaty, ku daina kuka, daga yau ba zan qara maki wanda zai saki kukan wahala ba kinji" daga mai kai tai, nan take suka tashi suka tsarkake jikin su kafin suka koma bacci,( ana son mutum bayan ya kusanci iyalin shi sui wanka ba a son kwana da janaba) bacci mai dadi sukai. Washe gari ta tashi da tsamin jiki,musamman cinyoyin ta, ruwan zafi sosai mai hadin kayan qamshi na musk, da magarya,sai yar bagaruwa kadan, da kaninfari iya ta kawo mata tace ta shiga ta zauna zata daina jin ciwon jiki, nan da nan ta zaro ido😳😳😳😳ko dai iya tasan me akai jiya ne,wata kunya ce ta kama ta ta daqe bakin ta ta kama tafiya a tsaye da sauri tana son ta gudu daki, yana hango su ta parlo dariya ta gama cika mai ciki,tashi yai ya amsa yai mata godiya ya kai mata ruwan, samun ta yai bakin gado tana hawaye " Ya salam me ya same ki Ameenee na? Wa ya bata ran sahiba ta,? Ko dan iya ta baki wannan ne baki so, bata gane komai ba fa, kawai tasan kin gaji tafiyar hanya ne yasa ta miki wannan hadin, da kin shiga robar kk zauna zakiji dadi a jikin ki," kallon shi tai da idanun ta masu kyau da sukai ja, kada mata kai yai alamar da gaske bata gane komai ba, cikin ran shi kam dariya ce cike, tqna shiga ko ya fashe da dariyar, yace " ikon Allah, ashe haka auren yara yake?" ......... *Ni ko Haermeebraerh nace ya ma fi haka wallah* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Page 4: Kwana biyu na cika kamar yanda Iya taima Ameenullah alqawari, haka taje ta roqi El-mustapha da in ba damuwa zata dakko Ameenullah, dan ta mai alqawari, nan take ya yarda, domin shima yana son yaron akwai wayo da tarbiyya, sannan kuma in an kawo shi zai debe ma Ameenee kewa da zaman kadaicin da zata shiga in tafiya ta kama shi, nan take ya saka driver da Iya suka tafi dakko shi, ba wani jinkiri mahaifiyar Aminullah Aishaa ta amince, tare da bada saqon gaisuwa mai yawa a kaiwa amarya, da kayayyakin su na Niger,😉 Aminullah ya yi murna sosai da farin ciki dan zai koma kusa da mai renon shi, yana son kulawa sosai, domin ita mahaifiyar shi akwai son yara, amma ba ta son dawainiyar su, son jiki ne da ita sosai, in tana zune bata qaunar abinda zai daga ta, in ba ita tai ra'ayi ba ko mijin ta ne wato Mus'ab sai dai yai komai da kan shi, tin yana fada har ya hakura, sai ya auna abubuwan alkhairin da take mai , yaga sun fi wannan din yawa sai ya mai da shi a matsayin ajizancin ta, haka suke rayuwar su kamar ba wata matsala. Kafin su zo ta gyara wa Aminullah daki babba mai kalar green da white, dakin ya yi kyau sosai, ko wanne daki a gidan akwai combination din kalar shi kuma kaloline masu matuqar kyau, gidane babba mai ban sha'awa ga kowa, suna isowa, da fari ya dan mata baqunta, amma yana ganin Uncle Musty,ya ware, wasan shi ya shiga yi sosai, in da da dare, El-mustapha yace suje shooping don a siyo mai kayayyakin wasa, da kuma wasu littafan makarantar kamar yanda yake da su a gida suna debe mai kewa, itama cewa tai a sai mata littatafan, tana son koyon bokon, amma bangaren turanci, tinda da shi ake amfani duk duniya, sai mata yai cikin zuciyar shi yaji dadi, dan matar shi na son koyon ilimi, ba qaramin dadi yake ji ba, idan ya ji ta tana karatu da asubah, ko kuma in tana zaune ita kadai yaji tana bitar wasu daga ayoyin qur'ani ko kuma wasu littafan addinin. Sun sai kaya sosai in da Ameenullah yai ta murna, ga ice cream da chocolate nan kala2 an sai mai, bayan sun kammala ya biya ne suka dawo gida, kafin ya shigo yai ma driver magana akan da safe zai na kai Ameenullah makaranta, amsawa yai cike da girmama wa da son ubangidan nashi, miqa mai wata leda El-mustapha yai shima yai kwalamar kar a varshi a baya, wajen mai gadi ya nufa suka bude suka hau cin gara suma, Ameenullah yai bacci a hannun ta tini, karbar shi yai, dan gani yai kamar ya mata nauyi, dan irin yaran nan ne masu jiki bulbul barakallah,ga hasken shi mai matuqar kyau da daukan ido, in ta qura mai ido gani take anya jinin Niger ne yaronnan??? Washe gari da kanta ta shirya shi ta hada mai abun karyawa da taimakon Iya, tinda ta iya girki na zamani ne dai bata iya ba, shima ta daura damban iyawa. A hankali kulawar Ameenullah ta dawo hannun ta, ita ta take mai komai, tare suke kwana in tafiya ta kama El-mustapha, a hankali ya maida mata sunan ta Ammii, yana kiran El-mustapha Abee, iyayen shi suna matuqar jin dadin hakan ba kadan ba, kusan a duk bayan kwana biyu uku sai sun je, zasu yini ma Aishaa sosai, sai dare su koma, yana kiran Aishaa da Momma, Mus'ab kuma Baaba, ba qaramin gata Ameenullah ke samu daga iyayen nashi hudu ba, sai ga shi a shekara daya da yai da Ameenee ya kusa yin Hizif 30, wanda tana kyautata zaton yana shekara 8 zai sauke alqur'ani, mahaifan uku sunji dadin hakan, kuma sun jinjina ma Ameenee. A kwana a tashi, yau shekarar Ameenullah uku a hannun su, Ameenee na hango kwance jikin mijin ta,Ameenullah na wajen qafar ta yana matsa mata, yana ta zubo haddar shi, Abee din shi na ta saurara yana lumshe ido, Ameenee na cin yalon da ta sa aka nemo da kyar, sakamakon tulelen cikin dake gaban ta, haihuwa ko wanne lokaci zata iya sallama, tana daga kwance ta miqe da sauri kamar an mintsineta, har tana buge Ameenullah, duk da bakin shi daya dan fashe bai damu ba, hankalin shi ya tashi ganin yanayin da Ammin shi ta shiga lokaci kadan, abu kamar wasa, sai ga Ammin shi na kuka, dan wata irin shagwaba take bugawa El-mustapha, riqe mai wuya tai ta qanqame shi, fuskar ta a girjin shi tana murza kanta dan azaba, " Haerbeebee je ka kirawo Iya da sauri," yana kuka ya fita tare da waigen ta, haka yaje ya kira Iyan, da hanzarin su suka shigo inda ta umarci El-mustapha da fuskar shi ta jiqe da gumi da hawaye da ya kai ta dakin da suka tanadi komai na haihuwa, zuwa yai ya aje ta agaban kujera ta durqusa tadan buda qafa kadan, Ameenullah ya je ya ba hakuri " Haerbeebee ka zauna anan kaji, kai tai ma Ammin ka addu'a Allah ya sa ta haifa maka qanwa ko qani lafiya kaji, kar kai kuka, ka zama namiji, " haka ya dan bubbuga fuskar shi, " To Abii kaima ka daina kukan, inshaa Allah zata haihu lafiya," rungume shi yai, ya dan yi kukan kadan, sannan yai kissing goshim shi ya shige dakin, Iya ta saka komai a qasan ta na tarba jariri, ta dafe kujera yaje ta gefen damar ta ya tsugunna, ya riqe hannun ta daya, dayan ta dafe kujera da shi, yana shafa bayan ta da daya, addu'a kawai take, tana yi ma iyayen ta da suka rasu addu'a, ko tai da qarfi ko tai a zuci, ganin wahalar da take sha ba kadan ba yace "ko asibiti zamu kaita Iya" " karka damu da ikon Allah zata haihu lfy, ni na karbi haihuwar Ameenullah, duk jikokina ni nake karbar haihuwar su," gyada mata kai yai, zai magana kenan yaji Ameenee tayi wani nishi mai qarfi, ta damqe shi kamar zata karya, sai da yai wata 'yar qara, Iya na qara mata gwarin guiwa, akan ta ci gaba da nishin, qoqarin zama take, ta ware qafa iya ta hana, a haka take son ta haihu( in mace ta haihu ta haka ba ta da matsalar samun qari wajen haihuwa, inshaa Allah) wani kyakkyawan nishi da tai sai ga Baby ta fado, ta saka kuka, cikin farin ciki iya ta duqa ta janye yarinyar, sannan ta umarci El-mustapha daya girgiza ta mahaifa ta fado, haka yayi ko, ta nuna mai yanda zai ya kwaso jini daya kwanta mata, cikin nutsuwa da tausayawa,yai hakan, nan da nan ya daga ta ya shiga da ita toilet, ya fara wanke ta da gasa ta, tin a ciki ta fara gyangyadi, suna fitowa waje yai qal, Iya ta gyara har Baby, ta mata wanka,ga qamshi da ke tashi a wajen, bayan ya shirya tane, suka bude wa Ameenullah qofa, fuskar shi tayi jawur, ga hawaye ga dariya, ya rasa wanne zai yi, yana shiga ya fada jikin Abiin shi ya fashe da kukan murna, da sauri ya qarasa jikin Ammin shi ya kwanta a jikin ta yana mata sannu, shafa kan shi tai tana murmushi, ta daga kan shi ta kada mai nata, alamar ya bar kuka, Iya ce ta miqa mai qanwar shi a hannu, kasa tsaida hawayen shi yai, wata irin soyayyar ta ce ta dira a zuciyar shi lokaci daya, ya qara qanqame ta, yana kissing din ta, " Ammii ina son bbyn nan, tana da kyau, Ammii Allah ya sa tai halin ki, itama ta zama bata duka ko fada" dariya suka saka sosai, " Inshaa Allah ba zata zama me fada ba Yaya Ameenullah, dan kai zaka na koya mata komai" murna ce fal cikin shi har ya zama Yaya ," Abii yau she zata fara ce min Yayan?" Cikin murya ta dariya Iya ta amsa da" In dai ba ta da yanga gobe ma sai ta fara, amma in zata maka yanga sai ta kai shekara biyu zuwa uku" kallon yarin yar dake ta bacci a hannun shi tana tsotsar yatsa yai yace," dan Allah kar ki min yanga kinji qanwata?" Dariya suke tayi dika," zo nan haerbeebee, ba zata maka yanga ba, dan ko Ammii ba zan bari ta fara kira ba Yaya zamu koya mata, kaji yaro na" dadi ne ya kama shi sosai, ya kwantar da kanshi jikin Ammin nashi. Ameenee ta yi kukan rashin dangi, ita daya a daki, dan ba zata so ya ga ni ba, gudun shigar shi damuwa shima, tinanin ta yanzu haka zata fara tara zuri'a da qanan shekaru, sannan ba ta da kowa, sai mijin ta, murmushi tai dan tina waye mijin nata, ya kasance namiji daya tamkar da ba iyaka, tasan yana maye mata gurbin yan uwa da ta rasa, amma gaba wa zata nuna ma yaran ta a matsayin dangin ta, Ameenullah ne ya shigo, ganin ta na kuka kan ya qaraso wajen ta idon shi ya cika da hawaye, zauna wa yai a kusan rabin jikin ta, yana tambayar ta meya same ta, cikin qarasa gangarowar hawayen shi," Haerbeebee, ka kula da qanwar ka, har girman ku kaji, kar ka bar qanwar ka ta shiga halin maraici, ko da yaushe ka zama kana tare da ita, ina nufin ka maida ta rabin jikin ka, ta zama ba inda zaka iya shiga ba da ita ba, har qarshen nunfashin ku, ka min al'qawari Ameenuna, duk da na san kana da qarancin shekaru amma na san kana da kaifin hankali, da kuma riqe abu,na san ka fahimce ni, kuma ka riqe abinda nake fada maka," gyada mata kai yai yana kuka, yace" Ammii na na miki alqawari zan kula da ita, har qarshen nunfahin mu, ki daina kuka," share hawayen ta tai ta dakko mai ita ta miqa mai, dai dai nan Abii n shi ya qaraso" ashe nan ka gudo ka barni da ball a hannu, " dariya ya mai yana mai gwalo,.... [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Hey guys, ina roqon duk wanda suka tambayen novel dinnan ta pc da su min hakuri sakamakon rashin tura shi ta pc da bana samun damar yi, i am truelly sorry, ku dinga adanawa a wani wajen saboda daga baya in kunji ya maku ku karanta, na gode. ME LOVE U XX❤ Page 5: Ran suna an sama yarinya Aishaa domin yi wa matar mus'ab takwara, amma shi Ameenullah na kiran ta da Lamyah, ( macen da take baqa kuma siririya) dan gaba daya Aishaa kamar ta daban ba baqa ba kuma ba fara ba kuma bata da wani girma, abu kamar wasa suna ya bita da wuya wani yace mata Aishaa in ba Ameenee ba. A kwana a tashi har ta kai shekara hudu sai kuma kamanannin ta suka canja, ta fara qiba da haske, kyaun ta ba qaramin ban mamaki yake ba mutane ba, hakane yasa Ameenee bata wasa da mata azkar din safe da yamma, ba qaramin son juna suke ba ita da Yah Amee din ta, haka take kiran shi, duk da baya so amma baya nuna wa sai bata kusa yake ma Ammiin shi magana, " ni Ammii bana son wani Yah Amee, yarinyar nan da akama ramawa tai, dan na bata sunan yar baqa sai ta rama, ai naga tayi haske ta tashi daga baqa yanzu" dariya Ammiin shi da Abii suke mai suce " to ai sau ka canja mata da sunan masu haske maybe ta canja maka kaima," " A'a wannan zai fi mata dadi in ta girma, kuma ma naga ba kowa ne yake da wannan sunan ba ai, zata zama daban a cikin mata kamar yanda take daban itama," sukan kalle shi da so da qauna a cikin ran su su rungume shi. Wayar shi ce take ringing a gefen shi, suna parlo suna kallo, miqa hannu yai yace " wake kira da darennan?" Yana dubawa sai yaga no qasar su ce, ea mammaki yake nunawa Ameenee har ta katse, aka sake bugowa, nuna mai tai ya daga yaji waye? Daga wa yai ya amsa, yayan shi ne, da suke uba daya, yake wanar da shi cewar Bappan su ba lafiya kamar zai mutu, yana ta tambayar shi, akwai abinda yake son ya bashi, nan take zuciyar shi tai rauni, dan Allah ya saka mai son yan uwan shi, ba kadan ba, hankalin shi ya tashi matuqa, miqewa yai ya shiga daki ya zauna bakin gado, zuciyar shi ta kasu kashi biyu, wani bangaren ana fada mai ya qi zuwa, dan suma sun yada shi, wani bangaren na ce mai yaje ba komai, yaje domin zumunci kuma domin Allah, beside baida kowa nan , can ne tushen shi, yaje ko yar shi ma ta san iyayen ta da suka guje ta, wata qila ma su daidaita, su so Ameenee, kodan hai fa masu kyakkawar diya da tai, a haka ta isko shi, bata tambaye shi ba, saboda ta kula, gaba daya hankalin shi a tashe yake, zama tai dab da shi ta kwantar da jikin ta a bayan shi, ta jingina da jikin gado, ta kwantar da jikin shi a nata, tana ta shafa qirjin shi da hannun ta daya, dayan kuma tana shafa sumar kanshi, a hankali take kissing din wuyan shi, tana hura ma kunnen shi iska, runtse idon shi yai, tin yana jin zafi a zuciyar shi har yaji ba komai, a hankali ta rada mai kalmar" I love u" da murmushi ya janyo ta ta koma saman shi ya ce " iiyeee ashe dai da gaske ake koyon turancin nan" dariya tai tace" ai dole na koyi duk yaren duniyar nan just to tell u how much i lobe u" daga ta yai sama kamar bbyn roba yana dubawa anya da gaske ita ce, na farko ta samu wani courage, hqr tana iya fadan tana son shi, wanda kullum sai dai shi ya fada, in ya matsa ta fada mai sai dai tace itama haka, sannan ga mamakin yanda har wani slanks take a turancin, " tsaya a ina kk koyi wannan turancin ne" dariya tai kan tai fari tace mai " a wajen Haerbeebee" gyada kai yai yana murmushi, can ya tuno da maganar da akai mai a waya, sai yace mata, " Habibty, ina son in kin aminve zamu tafi Dubai nan da kwana biyar, Bappana ba lafiya, da ni da ke bamu da kowa a Nigeria, domin kowan ki ya kuje ki, ni kuma ina son mu je ko shekara mu samu, saboda yarinyar mu ta san yan uwana duk da rashin son da suke mata, ba a san gawar fari ba, a qalla dai ta je" " Zaujee kar ka damu kan ka da neman yarda ta, ni mallakin ka ce, a qarqashin ikon ka nake, ko me kk so, ni zan kasance mai biyayya da mana fatan alkairi" kissing din ta ya shiga yi dan bai zaci zata yarda ba. A gidan Mus'ab kuwa duk jikin Aishaa da mus'ab din kanshi yayi sanyi, Ameenullah kam har zazzabi yai saboda jin wannan mummunan labarin, sosai labarin ya rikita shi, hakuri suka bashi, da alkawarin in ya gama secondary zai koma can in har basu dawo ba ya qarasa karatun shi, da kyar suka samu ya daina kuka,ranar da zasu tafi kam, kamar Ameenullah ba zai kai ba, sun so matuqa su tafi da shi, amma suna ganin ba zasui ma Aishaa daidai ba, tinda shi kadai gare ta, haka suka tafi kowa na cike da qunar rabuwa da dan uwan shi. Sun isa dubai lafiya inda suka nufi gidan shi na asali da yake can, an gyara shi kamar wani babban mai muqami na zuwa, haka Ameenee tai ta mamaki dama mijin da take tare da shi kenan? Yaran shi na dane ta kalla ko wanne fuakar shi cike da annuri, cikin harahen larabci daya daga cikin su yace, bai zaci zasu sake ganin shi ba, ba dan aiken da yake masu ba akai akai sai suce ko ya manta da qasae gaba daya, murmushi kawai yai yace, komai lokaci ne ai, gashi da lokaci yai na dawo, maraba suka qara mai suka bat shi da iyalan shi, kowa kallon Lamyah yake cike da so da qauna, dan ganin kyakkyawar yarinya, mai cike da kuzari. Bayan sun huta ne sun ci abinci sunyi wanka, sika shirya sai asibitin da aka mashi kwatancen a can aka kwantar da Uncle din nashi, isar su ke da wuya, ya hango yan uwan shi uku maza, kowannen su fuskar nan ba alamar walwala, iya abinda ya zata shine jikin uncle din su ne yai tsanani, abinda bai sani ba shine, baqar fatar matar shi ce basu so gani ba, ga tsarabar yarinya da suka gani, isa yai ya miqa masu hannu dan ya kula ko dan rungumar larabawan nan ma ba samu zai ba a wajen su, da kyar suka bashi hannu, da yatsa dayan su ya nuna mai dakin kama Ameenee yai ta qugu sannan ya karbi Lamyah suka shiga, a kwance suka tadda Uncle din nashi, kamar baya nunfashi,yana jin muryar shi ya bude ido a hankali, miqa mai hannu yai da nufin ya isa gare shi, kama hannun na shi yai, yai kissing, a hankali, a hankali ya mai nunu da qasan pillo din da yake kai, daga shi yai a hankali, ya ya dakko wasu takardu, yana ganin ya karba yai murmushi ya koma ya kwanta, shikenan rai yayi halin shi, cikin kidima ya leqa ya kira Doctor da yan uwan shi kowa ya shiga damuwa da tashin hankalin. Bayan an kai shi komai ya lafa ne yana zaune a daki shi kadai, Ameenee tana can dakin Lamyah tana mata wanka, ita kuma sai rashin ji take, tana tsalle2, dan Lamya ba dai son RAWA ba , gata qarama, amma yanda take son rawa abun na ba iyayen ta mamaki, dan dai in ba a TV ba ba ganin Ameenee tai tana rawa ba, dubawa yai yaga wasu takardu ne na dukiya mai tarin yawa, da wasiqa a ciki,wadda Uncle din shi ke neman gafarar shi akan tauye mai hakkin sa da yai, tin mutuwar iyayen shi, yayi kuka sosai shi daya inda nan take ya tina wata magana da daya daga cikin yan uwan shi ya fada mai, kan cewar, ko yaqi ko yaso sai dukiyar nan ta dawo wajen su, mamakin su yake sosai, amma ya yanke shawarar miqa masu dika, dan a yanzu ma yana da ninkin ta, dan haka ba komai dan ya mallaka masu, da gudu suka shigo Ameenee da Lamyah, in da ta biyo ta da rigar ta a hannu suna ta dariya, sai tayi nesa da ita sai ta tsaya tana rawa tana karya qugu, tana daga hannu sama, in taga Ammiin nata ta kusa amata sai ta diba da gudu, wajen Abiin ta taje ta kwanta tana daria, wurga masu rigar tai ita kuma ta kwanta tana haki, " ga shi nan ku qarata, wannan yarinyar sai an mata addu'a ita kenan rawa, na rasa in da ta ke gani, ina jin zamu daina kallon tashoshin rawa a gidannan," dariya tai tace " A'a. Ammii ina so plsssss" Abiin ta ce yace " Baza a canja maki, tasha ba, duk san da kk kallo kinji, abun da nake son da ke shine, ki zama mai yawan karatu da neman ilimi, kinji, in kina qoqari kika zama yarinyar kirki, to har wajen koyon rawa zan kai ki" Ameenee ce ta kama baki tana girgiza nai kai, dan gaba daya ba ta son wannan bangaren na shi na ba wa yarinyar su duk wani abu da take so mai kyau ko mara kyau, amma tai shiru dan ganin bai dace ta mai magana a gaban yar ta su ba. Bayan shekara 11 a Dubai da sukai, kullum suna waya da ita da Yah Amee din ta da Momma Aishaa, sai Baaba Mus'ab din ta, cikin da Ameenee ke dauke da shi ya girma sosai, in da yanzu Lamyah mai shekara 16, kowa ya ganta sau daya sai yai saurin sake juyawa dan kallon ta a karo na ba iyaka, tsabar kyau, da shape din da take dauke da shi, ga gashin ta mai tsaho da cika, santsi da baqi, Lamyah ta zama yarinya mai matuqar kyau son kowa qaunar wanda ya rasa, ga ilimi dan tinj ta sauke qur'ani da sauran littafan da mahaifiyar ta ta koya mata, bangaren boko ba a magana, yare uku take ji, Turanci, Larabci, sai hausa, tana son koyon Frence amma Yah Amee yace sai ta koma Niger zai koya mata. A kullum Ameenee na bata labarin dangin ta,kuma tana fada mata babban burin ta bai wuce ta haihu su je wajen dangin ta ta ga iyayen ta maza ba, dan duk da sun yada ta suna da haqqin ta sada zumunta da su, kusan kullum sai ta fadi hakan, hakan ne ya sa Lamyah take matuqar son zuwa Nijeria taje itama taga dangin mahaifiyar ta, taga ya qasar take. Ameenee ce ke naquda ba kowa a gidan lokacin,gaba daya ta galabaita, kafin mai masu wanki ta zo daukan wanki taji nishin ta, da sauri ta isa, Ameenee ko hanun ta bata iya dagawa, bakin ta ya bushe qaf...........😱 [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAN RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *Hey guys, i am so sory for the late update, i have been busy ne wallahi this days, kuma ban jin dadi, amma in komai yai normal zan dawo kamar kullum, ina godiya da damuwa da kuka nuna akan jina shiru da kukai, hakan ya tabbatar man kuna biye dani, and masu tambaya daga farko ina qara baku hakuri dan Allah ku tambaya a group.nasan ko daya ne baza a rasa mai shi dika ba,thank you so very much for the love and care. Me love u xx* Page: 6 Waya ta dauka ta kira El-mustapha daga yanayin maganar ta, hankalin shi ya gama tashi, ko qarasa sanar da shi.batai ba ya kashe ya taho, da hanzari yaje ya kamota, a take Iya ta fado mai arai, yai tinanin ko gwadawa zai ya karbi haihuwae shima, can kuma da yaji tana jan wani nunfashi, bai san sanda ya dauke ta ba sai asibiti, a hanyar fita suka ci karo ra Lamyah tana dawowa daga makaranta, itama komawa tai tabi bayan shi ta rungume Ammiin ta ya ja su, yana yi yana waigowa yana mata sannu, bata san ina kanta yake ba sam, Lamyah kam tai kuka ta gode Allah, fatan ta bai wuce na Allah ya tashi kafadar Ammiin su ba, a haka suka isa, nan da nan Doctors suka taru akan ta aka fara bata taimakon gaggawa, kiran shi sukai akan ya saka hannu su mata aiki, da hanzari ya saka hannun, bayan sun shiga da iya ne, cikin ikon Allah da taimakon addu'ar da su Lamyah suke ta mata, Allah ya bata iko ta haihu da kanta, amma jini ya tsaya yaqi tsayawa,sai da tai awa daya da wasu mintunan tana zubda jini, da kyar suka tsaida shi, ta haifi yaron ta qato tubarkallah kyakkawa sosai, mai matuqar kama da mahaifin shi, take wata iriyar soyayyae shi ta kama zuciyar Lamyah, tana hawayen murnar samun qani ta rungume shi tana kissing din shi, Ammii da Abii suna murmushin kallon soyayyar data bayyana a fuskar Lamyah, a haka Ameenee ta kwana uku suka sallamo.ta. A ranar da yaro ya cika kwana bakwai a ranar Lamyah ta dau hotunaj shi ta turawa Yah Amee din ta, ta rubuta mai " Yah Amee ga Mubarak qanin ka, na turo don ka gan shi," Yana gama gani ya bata amsa da, " Woooowww masha Allah, wannan kyakkyawan yaro haka? Allah ya raya mana shi da imani, amma ina fushi dake fa" " Yah Amee me nai" ta fada tana turo baki kamar yana ganin ta, " laifin da kk saba yi ne yau ma kk qara," Murmushi tai dan tasan me yake nifi " laifin me?" " hmmm Lamyahhhh kina son bam wahala, wannan ai abun kunya ne ace ban san fuskar ki ba bayan kin girma, kina nufin dole wai sai kun zo na ganki, ni ina matuqar son ganin yanda qanwata ta koma," " ni dai na baka hakuri nafi son na baka mamakin sunan daka saka min na baqaqen mata sirara, kai dai kawai ka sa a idon ka zaka ga macen da baka taba tsammani ba, kuma nasan su Abii bazasu karya promise din da sukai min na hanaka hotuna na ba" ta fada tana mashi gwalo, da dariya irin mai hawayen nan, kawai" Hmmm" ya rubuta mata, sai ya sauka online, kiran shi tai tana bashi hakuri, yace ya haqura, hirar su suka ci gaba, mai qunshe da ma'anonij da su suka barwa kan su sani. " My queen ni me kedamun ki ne, gaba daya wani irin fari kk kamar mara jini a jiki, ko dai qarin jinin da akai maki bai ba ne?" " Hum Abiin Ameenullah, lfy ta qalaou, ka daina sa ka damuwa aranka, rayuwa da mutuwa na wajen Allah, kuma duk abinda yai farko zai qarshe, fatana kawai shine ka daure ka ci gaba da mu'amala da mutane yanda kk yi, 'yan uwanka ka ci gaba da kyautata masu, na san ka sune sama da dukiyar ka dan haka koda ka ga zasu so salwantar da ranka akan dukiyar ka ka miqa masu ita dan a Niger da Nigeria ka na da mafiyan su, kullum kasuwancin ka habaka yake, ka kula da yaran nan kamar ina kusa daku, ka......" " Dakata wai me kk fada ne hak?" Ya fada cikin tashin hankali, da ganin kamar bankwana suke, take ya janyo ta ya rungume ta cikin wani irin runguma mai tsanani, da nuna bege da shauqi, hawayen da suke riqewa ne ya zubo masu kusan a tare, shessheqar kukan ta ne ya qara daga hankalin shi, haka sukai ta kuka ba mai rarrashin wani acikin su, sallamar Lamya ce ta katse masu kukan su, " Assalamu alaikum, na shigo?" Ta fada tana neman izini daga iyayen nata, Ammiii ce tace mata ta shiga, sannan ta shiga, kallon su tai taga gaba daya idon su alamun sunyi kuka, mamaki da tsoro ne ya mamaye ta da hanzari ta isa gare su ta zauna a tsakiyar su ta dora kanta a kafadar Ammii tace" Ammii na me ya same ku? Me akai maku idon ku dika alamar kun yi kuka? Ko baki da lafiya ne har yanz? Dan na kula gaba daya kin yi fari , kuma kin fada?" Kamo ta ta qarayi ta rungume sannan ta manna mata kiss a goshin ta, " Lamyah Haerbeebty, ba abinda ke man ciwo, kawai ina tinanin rayuwa ne, in yau mune wataran ba mune ba, ina roqon ki da ki ji tsoron Allah, ki kare mutuncin ki, kar ki sadaukar da darajar ki ta 'ya mace a banza, ki kamilantar da kan ki ga mijin da zai aure ki, ki kula da dan uwan ki, Allah zai kula da ke kema" cikib kuka sosai Lamya ta qanqame Ammiin ta, Abii ya qara rungume su dika " Ammii me ke damun ki, dan Allah ki fada mana matsalar ki, mu kadai kk da, bakinda wanda ya fimu, wannan maganganun naki na tsorata ni sosai" tashi suka ga tayi zata toilet,cikin kidima Abii yabi bayan ta ya juyo da ita, " Ameenatou me yasa baki fadan jinin nan na zuba haka ba? Me yasa baki sanar dani ba? Ameenatou in wani abu ya same ki bazan yafewa kaina ba, ina tare da ke am......" zamewa tai qasa zata fadi ya riqo ta, Lamyah ko kuka kawai take tana riqe da yar binjilallayir rigat ta da hannu daya dayan ta toshe bakin ta, ta sunkuya hawaye na zuba da gudu, Abii ne ya ce ta bude qofar suje asibiti, kafin ya taka qafar shi sai yaga....... *dan Allah ku min hakuri da wannan* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *BANI NAI KAINA BA FANS❤ this page is for u guys, i love ur comments, u guys ar awsome, and i love u XX, especially Ramlat Sani, Fateema Abubakar, Haleema Sahad, ina jin dadin comment din ku, dan ku na miqe yanzu na fara wannan page❤* Page 7: Har ta zube a wajen, da gudu ya ida taro ta suka fadi qasa, rungume ta yai tsam a jikin shi yana wani irin marayan kuka, sakamakon tabbatar da cewa ba nunfashi a jikin ta, Lamyah ko mutuwar tsaye tai nunfashin ta na fita da sauri da sauri, hawayen ta kamar na yi ruwa an dauke, daga baya ne Abii ya kula da halin da Lamyah take, nan take ya miqe ya daga Ameenee ya kwantar da ita a gadon, ya rufe ta, ya koma jikin Lamyah dan kar ai biyu, jijjigata yai nan danan ta zube a jikin shi, hakuri ya fara bata, yana ta taimake shi kar wani abu ya same ta, bai san ya zai da ran shi ba " Lamyah Haerbeebty pls say something, ki magana kinji, ki koka Ammiin ku ta tafi ta bar ni, ta barku, ta bar Yah Amee din ki, ki koka dan Allah Lamyah" wani kuka ne ya kwace mai mara sauti sai qunar rai, nan take hawaye masu zafi suka fara bin kuncin ta, ta fara kuka, da rarrafe taje ta kwantar da kanta jikin Ammiin ta " Ammii ina son ki, na so ace kin rayu damu, kin kula da Abii da Ni da Mubarak, ga Yah Amee na ya dade bai gan ki ba, a wannan lokacin da muka saka ran Zuwa Nigeria ki hadani da 'yan uwan ki ko bazasu karbe mu ba a wannan lokacin kk tafi kk barmu, Ammii Allah ya fimu son ki,Allah ka gafartawa Ammii na,ka kai rahama da salama kabarinta, Allah kasa ta tashi tana mai makwaftar Rasulullah, Allah ka sauqaqa mata kwanciyar qabari," kukan ta ne ya fara raguwa domin addu'ar da tai ma mahaifiyar ta sai take jin a ranta ta gama nuna mata soyayya, abinda ya rage ta ci gaba da nema mata Rahamar Allah, gefe ta koma ta takure ta hada guiwar ta da kanta tai shiru, Abii n ta na gefe yana matse kwallah, yana ma matat shi addu'a, sai daga baya yai tinanin yi mata duk abinda ya dace, miqewa yai ya fita kamar wanda ya sha abin maye, a haka yai waya ma abokan shi 'yan uwa da duk wanda ya dace sai dai ya ce kar a fadawa Ameenullah, ya fi son ya sanar da shi ga shi shima kuma ga shi, a haka Aishaa da Mus'ab suka fara shirin tahowa, Aisha tai kuka har taji ba dadi, Mus'ab tun yana rarrashin ta shima ya bige da kuka, Ameenullah na Nigeria wajen kasuwancin Abii da yake yi yakan dawo Nijer duk qarshen wata, sai kuma Baban shi ya tafi shima yai wata, wataran kuma suna tafiya tare, in suka je sukan sauka a hotel, har su gama abinda zasui su dawo. Mubarak ne ke ta tsala kuka, a lokacin har an kai Ammii makwamcin ta na gaskiya,wajen qarfe biyun dare, daga Lamyah har Abii sun rasa yanda zasui, yaqi shiru, Lamyah ce ta koma qasan qado tai ta kuka, yi take tana kumawa, shima Abii sharcr kwalla kawai yake, kukan Mubarak ba qaramin taba zuciyar Lamyah yake ba, wata irin zuciya ce ta shige ta nan take taji wani qwarin guiwar, cewa zata iya kula da qanin ta kamar ita ta haife shi, she is 15 going on 16,kuma Ammii tace a Nigeria ana ma yara 'yan 14 ma su haihu su raini baby so why can't she do it? Fita tai ta damo madara a fida ta karbe shi, ta miqa wa Abii hannu ya bata shi, miqa mata yai yana kallon fuskar ta cike da tausayawa,tina wa yai yanda Aishaa tai tai tai akan su koma Nijer ta kafe ita bazata ba, a bar su anan, har suka koma, duk qiwar Aisha a qalla yasan zata na koyawa Lamyah yanda za ta na kula da qanin ta, bari ya sawa sarautar Allah ido yaga ya zasu qare, Gani yai ta mai rungumar shan nono,ta saka mai fidar aiko kamar mai jira, nan da nan ya kama,ya dinga tsotsa ba jira, sai da ya shanye tass, sannan ta dora shi a kafadar ta yanda taga Ammii nayi, gyatsa yai sannan ya fara qoqarin bacci, sai me? Ji tai yana wata irin tusa mai qarfi, sai da ta tsorata, daga baya ita da Abii suka bushe da dariya, hannu ta saka a leben ta tace ma Abii " Shhhhhhhssshhh" shima yanda tai yayi, basu ankara ba suka ji Mubarak na kashi, aiko miqawa Abii shi tai, tana riqe hanci, dan dama ita a komai na reno bata son aikin kashi, hannu ya dage yana nuna kan shi, " Me me zan yi?" " wanke mai zakai Abii" ta fada tana daga gira, " Noooo pls u know i can't?" " Yes u can,me zai hana ka ma in the first place? Bayan kai ne Abii ni yayar shi ce kowa yasan ba zan iya ba i am just 15"ta fada tana daga kafada, kada idon shi yai sama yace," Fine" ya karbe shi ya daga shi sama, yai toilet da shi tana gimtsr dariya, juyo wa yai ya kalle ta yana hararar ta ta kama bakin ta tai dif, zuwa yai ya cire mai ya gyara shi,kan ya gama jariri yai baccin shi, rungumo shi yai ya dawo ua kwantar da shi a gadon nan suka kwanta dikan su da asuba ya tashe ta tai sallah ta koma, nan ma Mubarak ya tashi,kan ya shigo dakin ta hada mai madara ta bashi ta jijjiga shi sun koma bacci. Yau Ameenee ke cika kwana 60 cif da rasuwa, El-mustapha yai niyyar dakko mai reno amma Lamyah ta qi sam, tace in dan gyara kashin da yake ne ya koya mata zata na yi, da wannan zancen ya hakura, dan kuka tai tayi sosai, a haka yai ta bata hakuri sannan tai shiru aka bar zancen, Mubarak yana samun kulawa sosai, wajen Lamyah, dan komai take mai sai taga kamar bata yi, in da Ammii na da rai da zai fi samun kula, ko makaranta ta aje gefe, fatan ta kar qanin ta yai maraici. Watarana El-mustapha ya fita yaga wata mota na bin shi a baya, yai iya qoqarin shi ya bace ma motar, mamaki ne fal cikin shi, waye kenan? Me ake nema a wajen shi kuma? Take wani tinani ya ziyarce shi, na wayar da daya daga cikin 'yan uwan shi sukai mashi, sun tabbatar mashi da cewar, sun gano dukiyar da Uncle din su ya bashi ba ita kadai bace, ya boye wasu, saboda ko gezau arziqin shi bai ba, ya yi iya bakin qoqarin shi, na yaga ya fahimtar da su cewar shi fa dama wannan kudin baya gaban shi na gado, sannan dukiyar shi ta kasuwancin zannuwa da kayayyakin yadikan da yake siyarwa qasa2 ne ya tara sudan ba qanan kasuwanci yake ba manyan kasuwanci yake, amma inaaa sun tabbatar mai da in bai mallaka masu komai a hannun su ba zai fuskanci hukuncin da bai zata ba daga wajen su, yai rantsuwa ya kuma amma sam sun qi aminta da shi. Yau suna zaune da Lamyah da ta dan fada sakamakon rashin bacci da kuma gajiyawa na reno, tausayin gudan jinin shi ne ya kama shi, dan ko RAWAR ta ta da ta zama mata farillah bai kuma ganin ta yi ba, abun na matuqar damun shi canjin nata, a qanan shekarun ta, " Lamyah Haerbeebty fadan ina kk son zuwa in in Mubarak ya cika shekara?" Murmushi tai tace " Abii nafi son sai ya cika shekara biyar muje Nijeria, dan in cika burin Ammii na kaimu wajen 'Yan uwan ta" murmushin takaici yai, sakamakon tina yanda suka rabu da 'yan uwan mahaifiyar ta ta, amma nan da nan ya kauda tinanin saboda bai son dasa ma Lamyah tsanar su, " kar ki damu zamu je in dai shine burin ki," miqewa yai ya dakko mata wata jaka, ya bata a hannun ta, "ki ajen wannan jakar, duk rintsi duk wuya kar ki rabu da ita, sai kin sada ta ga Mus'ab, (mahaifin Ameenullah)" kallo ta bishi da shi, nan danan ya dauke damuwar fuskar shi da ce mata" zaki sha ice cream na dakko mana, kwadayin shi nake ji yau tin safe" " yippyyyy zan sha Abii dakko mana pls" tashi yai yana rangwada kai irin na murna na yara dinnan tana mai dariya, amma da zata juya ta ga fusjar shi da dariyar ta ta bace, ya san halin 'yan uwan shi akan kudi, basu da mutunci ko qanqani, tinani yake na ya tura ta Nijeria din da isassun kudin da zata iya kula da su na tsahon shekaru ya sai masu gida, in yaso hankalin shi zai fi kwanciya, domin ba zai so hukuncin 'yan uwan shk ya shafe su ba, tinda shi a yanzu ya gane raina masa hankali kawai suke son yi, dan cin dukiyar shi, duk da irin kyautatawar da yake masu, da wannan tinanin ya dakko ya kawo masu. Waya ya buga Nigeria ma wani dillalin sai da gidaje, ya siya mai dauke da daki biyu da babban parlor daya, sai kitchen, kowanne daki da toilet, kayan more rayuwa ya sa aka zuba masu ya kuma saya masu mota, unguwar a cikin mutane take, dan yana tsoron zaman su a waje mai shiru, kuma ko ba komai Lamyah zata ga Nigeria sosai yanda take so, dan ba qaramin buri ne da ita na ganin ta zagaya Nigeria don ganin labaran da Ammiin ta take bata, musamman garin kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa kano ko da mai kazo an fika💃🏻❤. *BAYAN SHEKRA DAYA* Yau bakin Lamyah kamar zai tsage dan farin ciki, waya rake da Yah Amee din ta " Abii ya gama komai zamu tafi an jima," " Yanzu Lamyah ba zaki zo Nijer ba na gan ki? Ki duba shekarun fa da mukai bamu ga juna ba, ga rowar kan mu da muka qaqabawa kan mu, haba Lamyah? Pls kizo mu hadu, ko zuciyata ta daina raya min kalar ki da yanayin ki, da da yanda zan na aje aikin nan na zo danayi, kin san dana bar nan aiki yawa zai wa Baba, pls ki zo Nijer" ya qarasa da karyewar murya,tausayin kansu ne ya kamata, tabbas tana tsananin son ganin shi, amma dole ta cika wa Ammii burin ta na zuwa ganin 'yan uwan ta, " Kayi hakuri Yah Amee, kai ma kasan yanda nake da burin zuwa Nijeria, ka bari dana je naga yanayin wajen , na gana da 'yan uwan Ammii zan zo Nijer kaji," da kyar ta shawo kanshi ya hakura, bayan ta kammala shirin ta ta gyara Mubarak ne, Abii ya shigo, kallon shi tai ta ga kamar baya cikin hayyacin shi " Maza maza, Lamyah ku fita a gidan ku tafi ta qofar baya, dirver zai dauke ki" " Abii me ke faruwa ne, me yake dmaun ka ka rame kana cikin tashin hankali da damuwa" " Lamyah wannan lokacin bana dogon bayani bane, muje ki tafi," kamk su yai duka ya rungume ya manna masu kisses ya tura su cikin mota, daga masu hannu yai tana daga mashi har motar ta bace ma ganin shi, wani abu yaji an buga mai ta baya wanda ya sa bai qara sanin ina kanshu yake ba...... [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH This page is for u Sweet Shaerreefaerht, Allah ya biya maki dukkan buqatun ki na alkairi. Love u XX❤ Page 8: Jan shi sukai su dika ukun a qasa, har cikin parlor n, duk inda suka ja shi jini ne ke zuba ya gogu a qasa, idon shi kawai yake budewa yana lumshe su, cikin zuciyar shi yana mai tsanan ta mamakin 'yan uwan nashi, ashe zasu iya aikata mai haka? Gaba daya bai kawo abun nasu ya kai har haka ba, duk a tinanin shi zasu so quntata ma yaran shi ta bangaren gaya ma Lamyah baqaqen maganganu, misali akan mahaifiyar ta, wanda shi baya son koda quda ya hau kan ta in dai da nufin cutarwa ne, ashe gwanda da ya nesanta su da shi, da har su zasu azabtar, daga sama yaji dayan.na tambayar shi cikin fushi " ina sauran kadarorin naka ka aje su" murmushin ganin qarfin halin su yake kawai, naushi mai qarfi dayan su ya sakar mashi a fuska, nan da nan bakin shi ya fara zubda jini tare da hancin shi, daga ido yai da kuma yatsan shi yai alamar kira a gare shi, da hanzari jiki na rawa ya matsa ya zaci fada mai zai kawai sai ji yai Abii ya tattaro yawun bakin shi mai jinin ya tofa a fuskar shi, cikin tsananin bacin rai ya tattare hannun shi zai daki Abii amma sauran suka riqe shi, suna fada mai ya bari su samu abinda suke so, in yaso koma me zai faru daga baya bai dame su ba, don jinin dake zuba a kan Abii ba kadan bane, kan shi kawai yake jin yana juya mashi, da kyar ya budi baki ya fara magana, " Al-Hassan, ban taba zatan ku 'yan uwana zaku min haka ba, ban san cewa kudi yafi zumunci da dan uwa ba, na mallaka maku dukiya ta ta gado duk da dimbin yawan da take da ita, amma bai ishe ku ba, shine sai kun hada da komai dana mallaka saboda tsabar mugunta? To ku sani , ba ku kuka nemar min ba, sannan ban nema domin ku ba, na nema domin iyalina, da al'ummar Rasulullah, dan haka ku min duk abinda zaku min ba samu zakui ba, dan na kula a yanda kuke ko na baku, ko ban baku ba, bazaku bar ni da raina ba" haushi ne ya qara kama Al-Hussain yace " Al-Hassan shiyasa nace maku mu kashe shi kawai, daga baya sai mu nemi dukiyar, mu hada auren 'yar shi da dan gidan Yaya, amma kace ba haka ba, ga shinan yana son bata mana komai" miqewa babban su yai, ya tako gaban Abii, " El-mustapha ka sani tun fil azal bana qaunar ka, bana qaunar komai na ka, tin mahaifan mu na da rayuwa, saboda fifikon da mahaifin mu yake nunawa akan ka, tin da kai dukiya nake son na samu damar mallakar ta, dan haka yanzu ma ba zan fasa ida nufina na kauda kai da abinda ka mallaka ba, ina Lamya" dariyar qarfin hali Abii yayi, " Yah Muhammad, ba zaka taba ganin Lamyah ba har abada, dan ko Nigeria kaje baza ka gan ta ba, Nigeria ba qaramar qasa bace, yanzu haka Lamyah da Mubarak suna hanyar Nigeria, in dukiya ta ce kuma nan ma ba abinda zaku samu banda wanda na baku a baya, wannan gidan ma danake ciki na sai da shi, hatta sauran gidaje na da kamfanoni na na sayar da su, na tattara komai na bayar ma yarinya ta ta kai ma wanda ban hada komai da shi ba, kuma ya ke kula da zuri'a ta da dukiya ta, ina maku nasiha da ku riqe zumunci tsakanin ku da Allah, ku guji son zuciya ko...." kan ya qarasa babban su ya kai mai wani wawan naushi, a tare da yin wata qara, ta bacin rai, bakin shi har kumfa yake dan jin ba abinda zasu samu, " El-mustapha ko ta halin qaqa sai dukiyar ka ta dawo hannun mu, sai na ka salwantar da rayuwar yaran da kk taqama da su, kake tinanin zaka iya katange su daga sharri na," fita sukai suka bar shi awajen bayan sun kwantar da shi a qasa, sun saka bawon ayaba, suka rufe qofar parlorn ta ciki dika biyun, sannan suka bar dayar da ba ma a bude ta sosai a bude, bayan sun kai kujera da table da cup dauke da ruwa a ciki, sannan suka tafi, tafiyar su ke da wuya El-mustapha ya fara ganin duhu gaba daya, baya jin komai kuma baya ganin komai, sannan ya kasa motsa komai na jikin shi, ba kadan ba jini ke zuba a kan shi, kalmar shahada kawai yake maimaitawa cikin ranshi, dan ko lips din shi ba si buduwa, a haka rai yai halin shi, in da daidai lokacin Lamyah ta farka daga baccin da take, Mubarak ya tsanyara kuka mai qarfi, lallashin shi ta hau yi,nan take taji idon ta na fidda kwalla, zuciyar ta ta tsinke sosai, karanta duk adduar da tazo mata take dan samun nutsuwar ta, a haka har suka isa Nigeria, duk doki da murnar ta sai taji komai na sauya mata,tana tsananin kewar Abiin ta da Ammii, bayan sun gama komai ta hada kan kayan ta ne, ta dakko littafin da Abii ya bata na address din inda zata nema, da kuma address din unguwar su Ammiin ta, tinani tai ta fara zuwa gidan su da Abii ya sai mata, in ta huta, ta kwana biyu, sai ta je. Tana isa gidan duk da bai kai kwatan kwatan na su ba amma ta yaba sosai, ta yaba da yanda gidan yake cikin mutane, taga yanda kowa ke harkokin shi, amma wasu na ta kallon ta kan ta shiga gidan, murmushi ta musu suma suka mayar mata ta shige, mai gadin gidan ne ya taso da gudu yana mata sannu da zuwa Nigeria, cikin hausar ta da bata wani fita sosai ta amsa mai cikin sakewar fuska, dakko mata kayan ta a motar da ta kawo ta yai ya shige da su, ya miqa mata keys din gidan, ya koma cike da qaunar ta a ranshi, dan bai zaci zai gan ta da fara'a haka ba, shiga tai cike da adduoi a bakin ta, na neman samun alkairan dake cikin sabon wajen ya kare ta daga sharrin dake ciki sabon wajen, kwantar da Mubarak tai ta nufi dakunan ta leqa,murmushi tai tace " Abii" wayar ta ta zaro ta hau kiran shi taji shiru ta qi shiga, tai ta qoqarin gwadawa amma bata shiga ba, hakura tai tace wataqila ya kashe yana hutawa ne, da wannan tinanin ta fara cire doguwar rigar ta ta zauna daga ita sai gajeran wandon ta da vest ta dauki Mubarak tai daki dashi dan watsa ruwa. Washe gari da wuri ta tashi, ta ma Mubarak wanka tayi ta saka dogoj wando da riga sannan ta dora boyfreind jarket mai matuqar kyau da ta kusa guiwar ta, ta zira takalmi ta dora mayafi akan ta, tulin gashin kanta data daure ya bayyana ta qasan qaramin mayafin nata, a haka ta tako ta kulle qofa,mai gadin na hango ta ya taso da gudu ya duqa ya gaida ta, amsawa tai cikin sakewar fuska, " Bala" wani saurayi ne ko nace matashi da ba zai wuce 27 ba ya taho da gudu ya duqa gaban Baba mai gadi " gani Baba" " ranki ya dade ga wanda zai na kai ki duk inda kk so," godiya tai tace mai tana son ya kaita wani kamar wajen cin abici da zata ci ta dan shaqata haka, amsa mata yai da to, ya karbi jakar hannun ta, ya bude mata mota, ta shiga sannan ta mai godiya, mamakin. Ta yake in tana masu godiya, wani qayataccan Hotel ya kai ta, a cikin garin kano, iya haduwa wajen ya hadu, kallon wajen take da sha'awa duk da cewa wajen ba za a kwatanta da ire-iren wuraren da ta saba gani ba, amma ya mata kyau sosai, shiga tai ta ci abinci mai rai da lfy ta tasa aka bawa driver ma dan qin shiga yai ta matsa suka shiga tare, yaci yai qat, yana fadi a ranshi " da haka masu kudi ke kula da masu aikin su ba za a samu masu masu mugunta ba daga masu aikin sun" bayan sun gama ne tai umarnin a hada mata take away, suna gamawa ta miqe ta fara tattakawa, tana ganin yanayin wajen, a yawon da take ne ta hanqo wani waje da mutane suka taru mata na ta rawa, ana kallo, ana tafa masu, abun ba qaramin burge ta yai ba, tana murmushi, taji wani ya mata magana a gefe... . [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH This page is for u dear as promised Hafsat Bello ( Maman Afaf) ki huta ❤ Page 9: Juyawa tai, wani saurayi ta gani, tare da shi akwai wata budurwa, siririya sosai fara mai kyau, ga hushirya, sai dai ko kadan ba ta kama qafar Lamyah a kyau ba, dan kuwa ban bancin dake tsakanin su kamar na Cute one( Hussy)😝 ne da Queen( Hassy)❤murmushi sukai wa juna, daidai nan driver n ta ya iso dauke da take away din su, yana kallon ta gefen saurayin nan sai ya fadada murmushin shi, yace " Aaa manyan gari ana ganin ku dama? Ko dake dama wane mu direbobi da irin ku matan manya? " dariya budurwar tai tai fari da ido, tace " Bala Driver kenan, ai kai na ce maka ina son ka, kai ne dai kk ja baya, ni dai rawa ce ba fasawa zan ba, koma me mutane zasu ce sai dai su fada, amma ni da ka ganni nan ba na yawon banza, rawa a jikina take, dana ji kida zan taka kuwa, so ni ban damu da surutun 'yan unguwa ba" ta fada tare da daga kafada, mamakin irin wannan surutu na wannan budurwa take, daga magana biyu zuwa uku tai goma ita, budurqar ce ta miqawa Lamyah hannu, tace " ni suna na Farha, kuma ina zaune a unguwar su Bala amma unguwar da yake aiki nake nifi" murmushi lamya tai bayan ta miqa mata hannun ta daya da wanda bai dauke da mubarak tace " ni suna na Aishaa amma ana kirana da Lamyah" daga hausar ta ta gane ko wace ce Lamyah, cikin zumudi ta ke magana, " Laaaahhh ke ce wadda aka ce zaki dawo unguwar mu daga dubai? Woww, i mean woww sai gani ga ki, u have no idea yanda na matsu na ga wace ce ke, dan labarin ya karade ko ina a unguwar mu, mahaifin ki ya kyautata ma 'yan unguwar mu ba kadan ba, ya mana alkairi mai yawa, duk da bamu taba ganin shi ba, ta hannun mai unguwar mu ya isar da dikkan saqon da ya ke son isarwa ga wadan da ke buqatar taimako," Lamyah ce cikin dariya sosai tace " do u really talk like this all the time?, " itama dariya tai ta kada ido tace " yeh haka nake, dan ma kin samu yau bana jin surutu, raina bace yake ban samu shiga rawa ba" ta qarasa cikin jimantawa kanta, kiran sallar azahar ne ya katse su, inda sukai sallama, farha tace ma Bala sai sun hadu a gida, in ba damuwa zata kawi wa Lamyah ziyara, Lamyah ta tabbatar mata ba damuwa, zata so hakan. Da yamma kuwa sai ga Farha ta iso cikin shigar ta kamar kullum doguwar riga da mayafin ta, wanda cikin kayan qananan kaya ne, sallama tai Baba Mai Gadi ya bude mata, duqawa tai har qasa ta gaida shi, tace mai ina Bala, yace yaje makaranta, dake yana BUK ne , yana a 200 level ne, sallama tai wa baban.ta shiga ciki, knocking tai a qofar inda Lamyah ta bude mata, tayi zufa.sakamakon rawar da ta tiqa, dan da suka dawo tai wanka tai sallah, ta zauna bayan ta sallami Mubarak ta bashi abinci ta hada shi da abin wasannin shi, stumin rawar ta ya motsa, daga nan tai ta rawa, data gaji ta ci abinci tai brush, sannan ta dawo ta dora daga inda ta tsaya, tana kan rawar ne Farha ta katse ta, dan gajeren tsaki tai, tana budewa da ta ga ita ce, cikin sakewa ta bude mata ta mata izinin shiga, dan sai take jin ita kam tayi qawa, dan runguma ta mata irin ta larabawa, ita ko Farha bata saba ba sai taji daban, wajen zama ta nuna mata ta wuce kitchen, kan ta dawo sai ganin Farha tai tana ta tiqar rawa, abun ya burge ta, aje ruwan tau sukai ta rawar sai da suka gaji suka zube kan kujera suna dariya tare da maida nunfashi, " gaskiya yau naji dadi sosai, ashe kema haka kk iya rawa?" " Hmmmm ai in kk ce rawa daya kenan, duk qawaye na na fisu iyawa, dan kuwa ko a makaranta in ana yi na fi kowa, dana fara kowa komawa gefe yake ya hau kallona, amma kuma ke taki salon rawar daban yake, BELLY DANCE kk yi," " eh haka ne, don mu ta can ita ake yi, rawar Larabawa kenan ai, shiyasa na keyin ta nima, in ina yi Abii yana cewa i am the best dancer ever" tinawa da Abii n ta ya sa kwalla ta kawo mata, tashi tai ta dakko wayar ta ta sake gwada layin shi, amma yanzu ma a kashe, kuka ne ya kwace mata, hankalin Farha ba qaramin tashi yai ba, nan take ta matsa kusa da ita, tana son dora hannun ta a bayan ta ta lallashe ta, tana tantama,janye hannun tai, daga baya kuma ta qara dorawa cikin inda inda, ta fara magana " me.... ya faru... kk kuka?" " Farha Abii na tin da nazo bai kira mu ba yaji, ya muke, sannan ina son naji ko yana lfy, gabana na mugun faduwa inna tina shi, hankali na na tashi kwarai" bubbuga bayan ta Farha tai itama ta share hawayen ta da suka fara ambaliya, tace" kiyi hakuri Lamyah kinga gwanda ke, kina da uban da zaki kalla ko mai daren dadewa ki tabbatar da cewa naki.ne, ni kuwa da dama tin kan a haifen nawa ya rasu, tawa uwar ta baro dangin miji da suka takura mata, ta zo nan ta rayu dani, har Allah yai cikawar ta, yanzu shekara biyu kenan, wannan rawar da kk gani dazu, ita ke riqe ni, banda kowa, ba wani nawa dan ban san dangina ba," kuka ne yaci qarfin ta, wanda ya bawa Lamyah tausayi matuqa, lallashin ta tai, ta labarta mata itama labarin rayuwar ta, gaba daya, da iya wanda ta sani da wanda taji labari, Farha ta matuqar tausaya ma Lamyah, " Lallau bahaushe yai gaskiya, in kaga jarabawar wani, naka sau ya zama nafila, sai dai ke da gatan ku ,ni kuma banda kowa," " Farha kin yi kowa, dan zan so ki dawo nan da zama mu zama kamar sisters, kinga Mubarak yanada yayu uku kenan, duk sanda mukai waya da Yah Amee na zan bashi labarin ki, dan shima tin da nazo bai kira ni ba , bari dai na duba me ke damun wayata ne, dan gaba daya kamar an canjan komai haka take, ita din ce dai amma is like komai ya sauya, No Abii kawai nake iya gani," dubawa tai sosai sai taga wani sabon layi ne na Nigeria aka saka mata, kuma ba Number din kowa, sai na Abii, itama sai yanzu ta kula sam no kamar ba daidai bace, wani irin tashin hankali ta shiga, meke faruwa ne, ta sunkui da kanta qasa tana nazari, ga zufa dake karyo mata, wani tinani ne ya shige ta, ta miqe kamar an mintsine ta, fadi take" Noooo Noooo pls this is not happining again pls" sai ta rushe da wani marayan kuka, ta durqusa ganin kukan ta ne yasa Mubarak rarrafawa ya rungume ta, yana kuka, lallashin shi Farha tai dan ita Lamyah gaba daya bata hayyacin ta, kuka kawai take" Farha sun kashen Abii na, tabbas shima yasan zasu kashe shi, na rasa shi kamar Ammii na, yasan zasu rava mu da shi, shiyasa ya turo mu nan, Abii meyasa kai haka, baka bari mun kaisu qara kotu ta bi mana haqqin mu ba? Abii me yasa ka basu dama, akan dukiyar ka? Daka sani ka basu, komai ko zamui yawo tsirara, zamu haqura da juna, Abii.." nunfashin ta ne ya fara sarqewa, ruwa Farha tai saurin bata, da kyar ta shq kuka kawai take ba qaqqautawa, " Abii hannun wa ka bar mu? Ina zan samu Yah Amee na ? Ya zan na samu Baaba Mus'ab ? Ban da tabbacin dangin Ammii zasu karbe mu, na fi son sai Mubarak ya kai matakin Secondary,a qallah dai da wayon shi, sai mu je, don ko sun koren ba zan ji kadaici ya min yawa na rashin Ammii ba" kuka suke dikan su su ukun, kwankwasa qofar akai, da kyar Farha ta tashi ta miqawa Lamyah Hijab din da ta gani a ninke a gefen kujera, ita kuma ta maida rigar ta, sannan ta je ta bude qofar, Bala ta gani, murmushin qarfin hali tai masa, izini Lamyah ta bashi ya shiga, ya zauna a gefe, " Farha na sha gaya maki ki daina kuka, kowa da kk gani a duniya akwai rayuwar da Allah ya tsara masa, taki jarabawar kenan, dan haka ki ragewa kan ki damuwa, ko kin daina ramar nan da bana so" ya qarasa cikin fara'a, murmushi tai, cike da shagwaba tace" Allah Bala in ka qarasa abunda ke zuciyar ka zamui fada" " Habaaa ni.na isa nace maki qugu kamar an daurawa tabarya zani? Wane ni?" Ya fada yana kama baki, murmushi sukai, in da Farha ta nemi izinin sanar da Bala komai, dan Farha ta dauke shi aboki, shine dai ke baya2 da ita, dan a unguwar sun dauke ta a ' Yar mace, kuma karuwa, Farha batai ilimin boko mai zurfi ba, dan mahaifiyar ta ta rasu tana SS1 so yanz haka shekarar ta 16, wajen karatun islama kuwa, itan A ce ba B ba, dan akwai shi sosai, wannan dalili ne yasa Bala ke koya mata karatun bokon sosai, bayan Bala yaji labarin dika, ya matuqar tausaya ma wadannan bayin Allah, da kan shi..... dan shi ta shi uwar rabuwa sukai da Baba mai gadi wai ba zata iya rayuwa da miji mai gadi ba duk kyaun ta, haka dai ya sallame ta, shi ko Bala yaqi binta dan bata da dalili mai kyau. A haka Bala, Lamyah, da Farha suka zama abokai, qoqari Lamyah tai ta koma makarantar boko, inda Baba Mai gadi ya shige masu gaba a matsayin uba, ita da Farha, suka koma, suka fara daga SS1 , dan su samu su shiga University, su samu damar yun ilimi, dan sun kula ba zasu samu rayuwa mai kyau ba ba ilimi. Mubarak kuwa mai aiki Lamyah ta dakko, take kula da shi ta musamman, wata dattijuwa ce sa bazata wuce 45 ba, mai suna Tani, waiiii Tani ba dai magana ba,ita da Farha Lamyah na rasa wa ya fi surutu, in suka fara wataran tashi take ta bar masu wajen. *Bayan shekara uku da wata biyu* Result din su Lamyah ya fito,kuma yai matuqar kyau, inda suka samu duk abinda suke da buqata. Mubarak ya iya magana, yai wayo, kamannin shi da Abiii na qara fitowa, sau da damar lokuta, Lamyah kan sashi gaba tai ta kuka, yai ta tambayar ta Mummy mene? Dan sunan da yake kuran ta kenan, a zaton shi ita ce mahaifiyar shi, san da ya fara kiran Lamyah da wannan suna ta sha kuka, dan ba qaramin tausaya ma kansu tai ba, bata hana shi ba, sannan bata bari kowa ya hana shi ba....... *to makaranta ga dai lamyah an gama secondary, kun san dai yanzu kyau ba a magana, ko yaushe zata fara rawar? Ni na matsu ta fara🙄* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Me koko kawas, this page is for u dear, ai sana'a lfy, sana'a goma maganin mai zaman banza😂 ME LOVE U XX❤ Page 10: Lamyah ce zaune tana ta danna waya , tayi sabbin qawaye, ta whatsapp, ta sanadin Farha, wadan da da damar su masoya rawa ne, hirar wata waqa suke da tanda ake stapes din rawar waqar, yanda Lamyah take bayani ba qaramin burge su tai ba, dan ta nuna masu ita fa gwana ce wajen rawa, ji tai an zauna a gefen.ta, " kaiii kaiii waye wannan dan Allah ni duk zaki soke ni da qashi🙄" ai ko Farha ta ji haushi dan ba ta so ana zancen ramar ta, qara zaune Lamyah tau tana dada sossoke ta da guiwar hannun ta, ita kuma Lamyah tana ta dariya dan abun kamar cakulkuli yake mata, Tani ce ta shigo, riqe da hannun Mubarak, yana ganin su haka da gudu shima ya taho ya haye" Mama Tani kina gani sun min taron dangi ko?" Dariya Tani tai tace" Hmmm yanzu na topa nawa ku juya ni kumin taron gari ba, ba ruwana haka na ganku, in kun gama ku taso ku ci abinci," miqewa sukai suna murna, dan dama yunwa suke ji, abinci suka.ci suka zauna suna hira," Lamyah yaushe zamu je wajen Faisal ne, kema a saka ki a wannan harka, ki fara, shiga taro kina bada mamaki? Dan na kula burin ki kenan, ki rawa a kalla a yaba maki, dan na san za sui matuqar son ganin taki salon rawar," kaiiii Farha wannan dogon sharhi haka, ni ko yau da yamma muje Bala ya kaimu," "yippyyyy, ba ri naje na dau wankan sikari, yau sai mun ba ma yara mamaki, dan kaf stapes din ki ba wanda ban dauke ba, yai sai....." " My goodness Farha, do u really need to talk much all the time?" 🙄 " yeh right, ya kamata na nutsu kar a raina mu, dan kin san akwai ni da maqiya a wajen nan basu son a ce yau ni zan rawa , dan ba qaramin kudi nake samu ba, sun san bana bin ko wanne qato daki, so kudin dana ke samu na daban ne" " mu ai ba ruwan mu da kowacce qatuwa kawai burina bai wuce nai rawa a min tafi ba na burge kowa sai naji nishadi a zuciya ta," haka sukai ta tattaunawa, har biyar na yamma, Lamyah ce ta fara tashi ta shige dakin su, dan tare suke kwana, yanzu mubarak ya zama yana kwana shi daya, wannan dalilin ne yasa suka ware mai daya dakin shi daya, Tani da sassafe take zuwa sai takwas na dare take tafiya. Bayan sunyi saallar isha'i ne suka yi ma Bala magana, ya fiddi mota, kowaccen su ta sha baqar abaya, tai rolling kanta, cikin ko kayane qanana, inda Lamyah ta saka skirt tsukakke ta qugu, qasan shi kuma mai fadi sosai, ga wasu yan stones masu gyalli da shegi daga qadan, haka akai wa ta saman ma ado, sai rigar ra dingilalliya, data kama jikin ta, tsam, ta gyara gashin ta , ta daure ta sake shi bayan ta tsaga gefen shi.ta kwantar da shi, avun dai ba a cewa komai sai wanda ya gani, Lamyah ba qaramin kyau tai ba, Farha sake baki tai.tana kallon ta kawai, " Farha kallon yao yawa tun muna shiri kk kallo na har yanzu, sai munje kin ja an raina mu," Farha ce ta gyara zama ta juyo gaba dayan ta ta fuskanci Lamyah zata fara zuba danneman surutun nata, Lamyah ta katse ta da" Farha na roqe ki da Allah ki hakuri, kar ki zuqen energy kan rawar," murguda baki tai ta juya ta ce " Fine"🙄 dariya Lamyah tai qasa2, dan tai imanin ta bar Farha ta bude baki, har su isa ba zatai shiru ba. Sun isa suka tadda Faisal a gofar shiga wajen rawar yana ta jiran su " Haba dan Allah sai kace wadan da ba zaku zo ba, kun shanya ni malamai," hakuri Farha ta fara bashi tana fari tana son zuba mai zancen nata yace" dakata kanya, dan in kk fara zuba sai an rasa mai kwashe ki yanzu, muje ciki a rubuta sunan ta ai komai a gama ta fara gudanar wa yau mu gani," ran farha ya baci sosai " Eh ai ko yau ko kun qi Allah sai nai surutu, dan kuwa ina cikin farin ciki, ba wanda ya isa ya hana ni magana ehe tin da ba d leben kowa nake zancen ba," ta qarashe cikin hawayen shagwaba, ita a dole yau an qi sauraren ta, Lamyah ce ta kamo ta tana lallashi, sannan ta hakura ta gyara tsaiwa zatai qala'in maganar da. Batai ba dazun aiko suna kula da hakan basui.magana.ba bare tace anqi ji suka sa kai ciki, bata gane ba, bin.su tai tana ta zuba , ko A ba mai gane wa, Bala dake gefe sai dariya yake, kama hannun Mubarak.yai suka tafi shan ice cream, dan da shi suka.taho, Lamyah ta ce suna tahowa da shi.tinda.ba kowa gida, Tani ta tafi. Wani waje suka je aka gama komai na tabbatar da Lamyah a cikin masu rawa, zuwa sukai wani daki dan yin kwalliya, sai Faisal ya dakko wasu kaya ya bata akan ta saka, qanana ne sosai, tace " A'a wannan ma sun yi qanqanta in gaskiya ne, balle ka ban wannan, barni da wadannan, tinda ni.ba wai wani abu ya kawoni ba bayan rawa, and wannan sune perfect kayan da zan yi rawar da nake son yi d su, cire doguwar rigar tai, ta baza gashin ta, sai da faisak ya kusa suma dan ganin kyau tsabar shi, ga wani gashi da tin da take sai dai a TV yake ganin irin shi,magana take mai ta shirya bai ji ba, sai d ta bugi kafadar shi sannan cikin in ina ya amsa ta da su je, yana tafe yana juyowa baya, sai tuntube yake, dariya kawai suke ta mashi, har suka isa, wani irin kishi ne mai tsanani ya kama yammatan wajen da ganin fitowar Lamyah............. *nima dai kishi ya kama ni na ganin Lamyah zata danse ba ni a ciki* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *Alhamdu lilLAAH for another blessed and healthy year, Ya Allah increase me in Eeman, health, wealth, and taqawa, ya Allah make me among the Salihun. HAPPY BIRTH DAY TO ME🎉🎉🎉🎉🎉🎉* ❤ Page 11: Tana hawa wajen da zata gudanar da rawar kuwa gaba daya hankulan mazajen wajen ya dawo kanta, wasu daga cikin matan dake wajen kansu sai da suka razana da ganin ta," wannan daga ina?" Waqa ce ta Arabs aka kunna mai matuqar dadi , a hankali ta fara takawa, dan sai taji gaba daya idon mutane ya mata yawa, amma da ta ci gaba da yanayin yanda aka fara tafa mata sai ta ware, daga nesa Farha ta kwada mata kira " Go Lamyah, show them what u got" kaii rawa fa tai rawa, kudi ne kawai on air, sai watsa mata su ake, qugun nan kamar zai karye saboda juya shi da take, amma ko a jikin ta, Farha ce ta zabura ta haye itama, rigar ta ta wurgowa Faisal, dan ko ankarewa bai ba, kan ya miqa hannu ya cafo ta har ta zille, tana " inaaaa wannan casu ba zan taba bari ya wuce ni ba, in na bari ya wuce ni sai kunyi jinya ta" gaba daya stapes din Lamyah kusan ba wanda bata dauke b a zman su, nan fa suka ci gaba da bada mamaki, haba mana, wasu maza ne daga gefe suka taso su biyu, suka iso gaban su suka balle farare bugun ABUJA, zuba su suke kamar ba sa so, tun faisal na kwasa shi daya sai da wasu ma'aikatan cikin wajen suka fara taya su, as promised, suna cikin rawae 10 na dare tayi, Faisal ne ya matsa kusa da Lamyah ya rada mata, ai ko tai wani irin juyi da qugun ta, tai baya da kanta sannan a hankali, cikin kwarewa ta dago, wani ihu.aka saka a cikin wajen, cikin nishadi da jin dadi ta jawo hannun Farha da ba ta san me ke faruwa ba kawai tiqar rawa take, masifa ta juyo tayi sai taga Lamyah," My goodness ni fa ban dade da fara wa ba , haba ki bari nima.na maida kwadayin rawata mana," Lamyah bata kula ta ba, Faisal ya wurga mata rigar ta, Lamyah ta nuna mata agogon jikin wayar ta da ta karba hannun Faisal, kame baki Farha tai, ta bi bayan Lamyah, suka shiga wajen kwalliya, ta dau kayan ta, bayan sun kimtsa ne, Faisal ya shigo, riqe da kudi masu yawa a hannun shi, wanda a qalla zasui dubu 70k hankalin farha ba qaramin tashi yai ba data ga yawan su, ita da sai dai a bata irin 30k 20k dinnan, tana ganin ta sha kwana da yawa, yau ga kudi masu yawa a gabanta, gyara tsaiwa tai tana son magana, sai ta bude baki ta yarfa hannu.sai kuma.tai shiru ta hadiyi yawu, data kasa magana kawai sai ta doka tsalle ta dane Lamyah, Lamyah dariya tai ta karbi kudin sukai godiya suka tafi, a mota suka tarda Bala daga shi har Mubarak sun fara bacci, shiga sukai, suka zauna inda Lamyah ta mannawa Mubarak kiss a goshi, tana shafa kanshi, nan take ta sa hannu a jaka ta zaro kudin rawar da suka samo, dubu goma ta miqawa Bala, sannan sauran gaba daya ta miqawa Lamyah, sannan ta dora mata gannu akan lips din ta alamar bata son godiya ko wani surutu, Farha kasa magana tai, ta qame qam, toshe bakin ta tai tana hawayen farin ciki, Lamyah zamewa tai kadan ta jingina da bayan kujerar ta lumshe ido, tunani kala2 ne cikin zuciyar ta, tinanin Abii, Ammiii, Yah Amee din ta, da kuma rayuwar kadaici ta rashin 'Yan uwa da iyaye da take ciki, kiss taji an mata a kumatu, ta bude ido tace " WTF Farha, do u have to do that? Ni nace maki na yafe komai kin tsorata ni gaba daya hankali na baya nan," rungume ta Farha ta qara yi, tana kukan murna," you have no idea how this mean to me, ba wan da ya taba ban dubu biyar ba tare da ya nemi wani abu daga wajena ba, na shiga qunci da matsin rayuwa, ba mai taimakona, a kullum inna tashi kk ga na samu kudi to naje nai rawa ne, dan ita kadai ce abinda na iya nake mora a rayuwata, mutanen duniya basu da kirki Lamyah, ki gode Allah baki san babu ba, baki san halayyar mutane ba, wanda sai sun ga kina cikin matsi zasu so kassara rayuwar ki" ta qarashe cikin kuka sosai, sakamakon tina baya da tai lokacin tana ita daya, ba mataimaki sai Allah, Lamyah qara rungume ta tai," its k dear, everything s ganna be just fine inshaa Allah, nothing will ever disturbe u i promise,"Lamyah na shafa bayan ta sai ji tai Farha na munshari, to an gaji, ga uwar rawar da ba a sa ta ba ta tiqa, dariya ce ta kwacewa Bala da Lamyah, aiki suka hau darawa, Bala ne yace" shi yasa nake son ta she is so innocent, ba ruwan ta da shirme, amma gaba daya a unguwa sun qi gane hakan, ka dan ne suka fahimce ta, akwai lokacin da aka ce za a kore fa a unguwa kar ta bata tarbiyyan yaran wajen, Farha ta musu hauka, tace nan nan wakilin mai unguwa da ta taba kai mai koken ya taimaka mata kwanan ta biyu ba abincin kirki neman ya keta mata mutunci yai, da ita din yar iska ce yan da take a yunwace ai da ta yarda, ke na taqaice maki a haka dai magana ta mutu, sai ga 'yar da suke cewa tafi kowa hankali a unguwar 'yar wani kamilin mutum Malam Sule, ta yi ciki, kaiiii ranar sun ga tijara wajen Farha" ya qarasa yana dariya sakamakon tina me ya faru ranar da yai, isar su gida ne ya katse shi, su kai ta dariyar rikici irin na Farha, har yanzu da suka girma suke jin suma manya ne tin da sun cika 20 da yan kai Farha bata barin shiririta, sai son girma, in Mubarak yace ma Lamyah mummy, ita kuma Farha yanzu zata kamo shi tace," to mara ta ido, in ka qara ce man Farha ba Aunty ba , ko Adda, ko Yayah zaka ga ya zan da kai sai na balle maka haqori daya," tin Mubarak na kuka har ya koma mata dariya, data sake shi zace Farha ya kwasa da gudu, ba ko zata tsaya bata lokaci wajen bin bayan shi ba. *NIJER REPOBLIC* Yau shekara hudu da watanni kenan da Baaba Mus'ab ya san mutuwar Amini kuma aboki sannan dan uwan shi El-mustapha, ran da suka sani dan qaramin hauka ya masu, Ameenullah kuwa, ya suma yafi a qirga, sai da ta kai an mai qarin ruwa tare sa allurar bacci, dan gudun kar wani abu ya same shi, satin shi biyu cif aka sallamo shi, ya rame yai baqi, baya umm baya umm umm, tinanin dake daga mai hankali, da ganin gawar yasan kashe mai Abiii akai, amma an hana su yarda da hakan, domin duk wani shaidar mutuwa yai sakamakon taka bawon Ayaba, da yai an gabatar, in ya mutu ne haka kawai ina Lamyan shi? Ina Mubarak? Sannan ya akai ba a ga komai na dukiyar shi ba? Dakko wayar shi yai ya bude, yana duba messages nan ya ga saqon , da Abiin shi ya turo mai, jiki na rawa yana hawaye ya ke qoqarin bude saqon, Sallama ce sai gaisuwa, sannan ya fada mai yana cikin hadari, game da 'yan uwan shi, amma kar ya samu koma mene ne Lamyah da mubarak will be safe inshaa Allah, wasu hawaye ne masu zafi sosai suka zubo mai, "to ina take? Ina zan gan su? Me yasami qanwa ta, amana ta? Wace irin rayuwa suke? Ta ina zan fara neman su?" Tari ne ya sarqe shi, ya fara yi ba tsayawa, Mommaa Aisha ce ta shigo cikin hanzari, fridge din cikin parlorn shi ta bude ta dakko ruwa ta kamo shi jikin ta tana hawaye ta bashi , tare sa shafa bayan shi, a hankali ya samu nutsuwa, " ka yi hakuri Haerbeebee, ka kwantar da hankalin ka, ka ma Abiin ka addu'a shi da Ammiin ka, ita suke buqata a wajen ka ba kuka da damuwa ba, ba za su so ganin ka a haka ba, sannan ina son ka sa 'yar uwar ka a addu'ae itama Allah ya bayyana mana ita," kuka yake sosai kamar qaramin yaro, yana qara mannewa a jikin Momman shi, a hankali tana shafa bayan shi da kan shi yai bacci, gyara mai kwanciya tai cikin tausaya wa dan nata, dan ta san shaquwar dake tsakanij su, haka ta fita tana share kwalla.......... *celebrate with me Roumie na and Aisha Bixxisiou, kuna raina always, ku din daban ne, love u da yawa* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *WOW ! i must say thanks to this wonderful and amazing people, u guys ar awsome, and i love u so so so very much u made my day so beautiful* *My family i love u all❤ My friends ku daban ne na zama ku kun zama ni, Widad Ummu Hafeeza❤ My family freind, and so many others sunayen ku ba zai fadu a dan wannan page ba, amma ina mai tabbatar maku da naji dadin addu'oin ku jiya, Allah ya bar mu tare ya saka maku da alkairi mara yankewa❤* *Mamu Novella* *Bani nayi kaina ba G* *Matsalolin Mata A yau G* *Safaa & Marwaa Fans* *Tabital fulaku G* *Zahrah Surbajo G* *Ummyn Yusrah G* *Al'ummata G* *Sophy And Vc novels* *Sawwama Novel G* *Matan Gidan Daraja G* *Qasaitattun Mata G* *Na gode da addu'oin kukuma, sosai naji dadi, Allah ya saka maku da alkairi mara yankewa❤* Page 12: Sai da Baabaa Mus'ab da Momma Aisha suka sha fama sosai, kafin Ameenullah ya daidaita, ya koma normal, amma ya rage yawan fara'a sosai, sannan ya rage magana, komai akai sai dai yai murmushi, ko ya bada amsa da kai, qasan zuciyar shi cike yake da soj ganin qanwar shi, da yanzu ta tabbatar wa kan shi son ta yake matuqa, so irin na aure ba soyayyar wa da qanwa ba, zuciyar shi na azabtuwa in ya tina har wannaj lokacin ba zai ce ga kamannin ta ba, muryar ta sai ta waya yake ji, abun na matuqar damun shi ba kadan ba, sannan ya zatai ta kula da Mubarak, iya wannan tswon shekarun, yakan yi kuka sosai, ya gode Allah, domin ya san tabbas suma suna cikin kadaicin rashin kowa nasu, cigiya kam a gidan redio da TV tare da jaridu duk sun.bayar, amma shiru kk ji. Yau ne Baaba ya samu Ameenullah, ya ke mai maganar komawar shi Nigeria aiki, don zaman ya isa haka, yana da kyau a ci gaba da kulawa da dukiyar da El-mustapha ya bari ko dan yaran shi, da ci gaba da yin sadaka da kyautukan da ya saba, ba dan Ameenullah yaso ba ya gyada mai kai, bayan ya fita ne ya kwanta yana kallon sama, sai tinani yale kala2, har aka kira sallar magrib, tashi yai yaje yai alwala ya tafi masjid, bayan ya dawo ne, ya fara shirya kayan shi kamar yanda ya saba, kiran abokin shi yai, Faisal, " Yah Man ya akayi ne? Ina fatan dai gobe zaka zauna gida ba zaka wajen shegiyar rawar nan ta ku da kuka dorawa kan ku ba?" " yessss gobe zaka zo? Alhamdu lilLAAH, dama ina son ka zo akwai wata haja dana aje maka, wannan karon ko min qin kusantar mace da kk akan dalilin wata da ba ta san kana ma son ta ba, wannan karon sai ka dana, wannan kalar kuce, ta hadu iya haduwa, bata da makusa ko ta ina, matsala daya da za a samu shine, bata kula kowa, sannan bata cika magana ba, dan ina jin tin da muke bai fi sau uku na taba jin maganar ta ba, ita dai kawai ta zo tai rawa ta tafi kuma......." "Ya Allah, Faisal, me yasa kk min wannan dogon sharhi haka ne? Ni fa ban ce maka ina son kowa ba,hasalima kai kasan bana son hulda da mata, dan Allah ka aje surutun ka a wata ma'adana wataqila zai ma amfani, wanni karon" kit ya kashe wayar ta dayan bangaren Faisal ko da yake shirin shiga hotel din yai dariya kawai dan yasan halin abokin nashi. Washegari da sassafe ya nufi Nigeria, bayan nasiha da Baaba ya saba mai wannan karon sai da ya qara akan na da, Momma ma haka tai ta mai nasiha tare da kwantar mai da hankali, cikin so da qaunar dan nata tare da kewar shi da ta fara tin kan ya tafi ta kai bakin ta goshin shi ta manna mai kiss, bayan ya tafi ne Baaba mus'ab yace " To sauran ni, dan na kula gaba daya hankalin ki ya tattara akan dan ki, tin da ya zo kk manta dani" ya qarasa cikin shagwaba kamar wani yaro, kwallar dake idon ta ta mayar nan da nan ta maye gurbin damuwar ta da farin ciki," Habaa Baaban Lamyah, da girman ka kk shagwaba, to matso ka gani," matsawa yai ya miqa mata fuskar shi, lips din shi ta kaiwa soft kiss, nan take ya lumshe ido, kan ya bude ta shige bedroom tana dariya, dariya yai shima ya bita yana," ai sai ki saya ki karbi tukuicin ki kema ko," " A'a ni kam na yafe Allah," dariya sukai cikin nishadi da nunawa junan su so. Da magrib Lamyah na gani da guntun wando iya cinyar ta, kalar bby pink, sai riga da ta daga hannun ha ana ganin cikin ta, da cibiyar ta, ta daure gashin ta, hannun ta ya sha lalle da qafarta, an mata baqi da ja, sai naga ta dakko tirarukan ta tananta barin su sannan ta shafa powder, tana gamawa ta dora baqar abaya, kusan shigar da Farha tai kenan, Mubarak kuwa manyan kaya suka saka mai, dan shi wataran har kuka yake in an saka mai qananan kaya, sam.basa burge shi,in ba bacci zai ba ya saka na bacci, Farha kan kira shi saurayin qauye kawai, shi kuma ya murguda baki kamar budurwa harda fari da ido, in ta biyo shi ya gudu wajen Mummyn shi, yana mata gwalo," Lamyah yau gaskiya sai mun fi ruda duk wanda Allah ya sa yai tozali da mu, ni har na fara jin kunya, anya bamui shigar tsiraici da yawa ba?" " ke malama in zaki gama ki zo mu tafi ki taso, ai dai naga ba sai da jikin namu zamu ba ko, zamu ne dan nishadin mu kawai mu komo," " haka ne, to ni dai yanzu gaskiya jibi sai naje kasuwa, dan siyo pant da Bra na acuci maza, qawata Cutie kullum shi take sawa, kan na gano ta ba mai cewa ba nata ba, ni nqi ta tafiya zalau2 ba nama ke kuwa ko ina sai san barka," maganar ta ba qaramin ba Lamyah dariya tai ba, har tana kama ciki, "kin ga matakar ki dariyar tsiya dilla ni tashi mu tafi, nimq zan qibar ne ai, sai na baki mamaki, har sai kin nema min abun rage ta, kai kuma da kk guntse dariya ka sake kayi ta sai na zaune ka, ta shi kaje kace ma Bala mun gama," ta fada tana kunburi ita an mata dariyar bata da qiba, aiko sai da mubarak ya kai qofa ya juyo yace " Farha ni dai kk zaune ni sai na mutu, qashi zaki soka min," da gudu ya fita yana dariya zata bishi Lamyah ta riqe ta," haba princess din Bala, ina zaki da gudu haka ai sai Bala yace baki da aji," " to laifij waye in an ganni ban da ajin ? Ba ke kk fadan haka a gaban shi ba gashi nan yai hadda, ko batan wasali baya yi? Ni dai gaskiya asan ya za ai dani, ko kuma kema ki fara slimming cinyoyin da qirjin ki su dawo kamar nawa," ta qarashe maganar cike da shagwaba, Lamyah ce ta shanye dariyar ta ta kamo ta tana buga bayan ta," kar ki damu yanda kk so haka za ai, tashi mu tafi," miqewa tai cikin yanga, kamar zata balle, Lamyah ce ta saki tari, mqi hade da.dariya, aiko cikin fushi fuuuuu tai waje, zama tai gefen kujera tana ta tiqar dariyar ta, sai da tai ta qoshi ta gyara fuskar ta suka fita, lokacin tara ta kusa, a hanya ba mai kula kowa, Bala yayi iya qoqarin shi darling din shi tai magana taqi sam,Lamyah ya zabgawa harara ta madubi, daidai sun hada ido," Whatttt???? Me nai kk hararata," " nasan laifin ki ne koma me yasa Farha fushi, ga shi nan kin ja min," dariya take son yi amma bata son ta bata ma farha rai again,dan yanzu kam tasan tana gab da kuka, kuma tana son ba Bala amsa, haka ta shanye dariyar ta kawai ta koma gefe tana kallon titi, hannu ya sa ya riqo hannun Farha wadda ta zame da sauri, ta na kallon shi, da ma'anoni masu yawa, tsayawar motar a filin da suke parking ne ya janye hankalin ta daga kan shi, da sauri ta kama murfin ta fice, Faisal da Ameenullah su kuma sun fito, suna hira, kawai sai Lamyah ta tsinci kanta da faduwar gaba, like wise Ameenullah, shi ko harda dafe qirjin shi yai, "Man lfy?" " ba komai haka nan naji qirjina na bugawa da sauri, kuma zuciyata ta tsinke sosai Allah ka jiyar da mu alkairi," amsawa faisal yai yana kallon gefen su, inda suke takowa cikin yanga da qasaita irin na hadaddun mata........ [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA. 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH page 13: Tunda suka qaraso da Ameenullah ya hada ido da Lamyah, gaban shi yai wani irin bugawa, wani irin abu yake ji daha qafar shi zuwa kan shi, itan ma hakan take a wajen ta, kallon kallo sukai, kafin su dauke kai ga barin kallon juna, Farha ce tai fari tace," Hey handsome, ya kk?," banza yai da ita bayan ya mata kallon tara saura kwata, wayar shi ya zaro yana daddanawa, yana kallon tsohuwar Numbern Lamyah, dan guntun tsaki Farha tai wanda ya sa Ameenullah ya kalle ta da wani irin kallon da yasa ta ja hannun Lamyah tai gaba, tace ma Faisal," ka same mu a ciki in wannan dan rainin ya barka, ni kwata, bana son yana dawowa gaba daya baida sabo, dan ma ya samu mace kamar ni tana kula shi yake wani basar wa, dadin abun ina da saurayi, ba a kasuwa nake ba ehe," ta fada lokacin da take kada yan qananun duwais din ta, Lamyah kam yau tana cikin dariya ne sosai, amma wannan karon duk da dariyar da take ji, gaba daya ta kasa yi, saboda yanda take jin mutuwar jiki, bayan sun shiga ne Farha ta kamo hannin ta ta fara cire mata Abayar ta, ," Gurl me ke damun ki ne? Gaba daya naga jikin ki yai sanyi, ko dai wani abi na miki?" " A'a ni kam baki man komai ba haka nan naji jikina ya mutu, amma ba komai da naji taken mu zan ware na san," ta qarasa cikin murmushi, Farha ce ta qarasa mata make up, zata ce Lamyah kenan Faisal ya leqo, sai ta sauya da sunan da tai register da shi wato, Laila, ," lokaci yayi me kuke yi ne har yanzu?" " gamu nan zuwa" miqewa sukai a tare suka fito, kida aka baza masu nan da nan Lamyah ta ware, rawa take kamar ba qashi a jikin ta, juyi take kamar wata tarwada, guqun nan kamar zai karye saboda girgiza shi da take, haka ma qirjin ta, ga gashin ta da ta baza in tana rawa yana gaba yana baya, ko ta maoda kai gefe, abun sai wanda ya gani, Ameenullah da ya leqo fadama Faisal zai kwanta ko ya dawo kar ya neme shi ya tsaya kallon ikon Allah, baki ya bude bai ma san yayi ba, kallon ta yake kamar idon shi zasu fado, wani iri zuciyar shi take kamar ya ruga da gudu ya dauke ta ya boye haka yaji, dukan kafadar shi yaji anyi, " Man ya dai, ko ka gano abinda na hango maka ne?" Faisal ya fada cike da tsokana, daure fuska Ameenullah yai," malam dama na zo fada maka ne ka wuce dakin ka kar ka damen in ka dawo, bacci nake ji," kawai ya sa kai ya wuce " Sunan ta Lailah," iya abinda Faisal ya fada kenan yai gaba, maimaita sunan Ameenullah yai tayi har ya isa dakin shi, kwantawa yai ringingine yana ayyana abubuwa da yawa a ran shi, " Lailah, Lailah kin bata sunan ki, na tabbata wannan ba zata wuce sa'ar Lamyah ta ba, Allah sarki Lamyah, duk in da kk Allah yare man ke, ya kiyaye ki daga fadawa halaka," hawaye ne ya gangaro mai, amma sai me rufe idon da yai hoton Lailah yake kallo, miqewa yai da sauri ya leqa window , aiko yana budewa tana daga kanta, hada ido sukai daidai zata shiga mota, saurin shigewa tai, dan bata zaci zata gan shi ba,saboda gaba daya da tinanin shi ta gama rawar ta, wurga ido take dama taga ina zata sake ganin wannan kyakkyawar fuska? Aiko yana sakewa ya dafe qirji yana murmushi, itama murmushi tai data zauna, Farha ce ta fara zuba kamar kanya, Bala na amsa ta cikin jin dadi, dan dazu ta tsume bai sami damar magana da ita ba, har suka isa gida Lamyah na tina handsome din da ta gani dazu. A qa'ida kwana biyu suke a tsakani kan su koma rawa, Allah Allah Lamyah take lokacin komawar su yayi tai tozali da wannan kyakkyawa, haka ta bangaren Ameenullah, roqon shi Allah ya bashi ikon daurewa kar ya tambayi wannan sarkin surutun inda zai ga Lailah yake. Bayan ta idar da sallah ne ta yi karatun qur'ani, Farha da Mubarak ne suka zo da nasu qur'anan suka zauna suka tankwashe qafafun su, qari tai masu kamar kullum bayan sun kammala sukai ma iyayen su addu'a, bayan sun idar ne kowa ya miqe yai dakin shi, kwantawa sukai dan su koma bacci, amma kamar daren jiya,haka bacci ya kasa daukar ta, Farha ce ta juyo tace," Lamyah wai me ke damun ki ne? Gaba daya tin jiya na kula baki da walwala, ko wani abun na miki ne ki sanar dani dan Allah," ta qarasa idon ta ya cika da kwalla, Lamyah kamo hannun ta tai da sauri tana girgiza mata kai,idon ta cike da hawaye, nan da nan suka fara kwarara," Farha ban san meke damuna ba, amma ni dai nasan ina missing Abii na da Ammii ga Yah Amee shiru, ba mai nemana, in ma sun neme ni ba zasu ganni ba, zuciyata ta fara raya min na je neman dangin mahaifiyata , dan na samu wasu a kusa da ni da zasu zama majingina a garen ,"kuka take sosai, zuciyar ta na quna sosai, ga shi ba zata iya sanar da Farha me ke damun ta game da wannan Ajnabin da ta gani dazu ba, tabbas zuciyar ta ba wanda take so illa Yah Amee din ta, amma wannan baqon lamarin da take ji game da wannan bawan Allah yana bata tsoro, kukan ta ne ya tsanan ta, Farha sarkin surutu ba baki itama kukan take, haka Tani ta isko su," me zan gani haka yarannan ku sa juna gaba kuna kuka, ko mai yai zafi maganin shi Allah, ku sauqaqa wa zuqatan ku ko kun samu sauqin ko me ke damun ku," a tare suka fada jikin ta suna kuka, bubbuga bayan su tai har suka samu sukai shiru, " to yammatan Tani, ku zo muje a hada abin karyawa," miqewa sukai, suka bi bayan ta suna goge fuskokin su. Tanj ta kasance tana koyar da su wasu abubuwan da ya zamana basu iya ba, dan kar au tashi ba su san komai ba, a da Lamyah tana ganin hakan a matsayin aikin wahala, tin da bata saba ba, amma da Farha parrot ta zauna ta mata bayani, a cikin bayanin nata ne, take fada mata a nan in ba ta iya komai ba, wata zata karbe mata miji, ko da Yah Amee din ta ne kuwa, habaaa tana jin haka hankalin ta ya tashi, kishin su na Larabawa ya motsa mata, a ranar ta wahala wajen koyon girki, ta yanke ta qone,amma duk bata ji, burin ta bai wuce ta ga ta iya komai da zai ja mata hankalin Yah Amee din ta, a yanzu tana matakin tsakiya, na koyon abubuwa, Tani kuma ta zage damtse tana koya mata abincin kala2 na qasashe daban daban. *sai nace Lamyah girki adon mace wadda ta iya ta huta, wadda batabiya ba ta sha haushi, mata a dage a iya girki, da sauran abubuwan da suke saka mace ta zama qasaitacciyar mace a wajen miji da ko ina* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA. 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH page 14: Yau tin safe Lamyah take cike da farin ciki, zuciyar ta fes, " Mummy why ar u so excited ? " " yeh what's new?" " kunji min mutane kawai ku sani gaba da tambaya akan mutum ba zai farin ciki ba kenan?, to nothing new, kawai yau ina jin nishadi ne saboda RAWA, kema kin san ita ke sani nishadi ko?" Farha tabe baki tai tace " Imm bari kiga na tafi wajen Bala mu sha hirar mu saboda jiya ya wuni school, bamu zanta ba, ina son fada mai how much i love him, ina son na ga kyakkyawar fuskar shi ko hankalina ya kwanta, qawaye na suna ganin a yanda nake bai dace da ni ba, ba zasu gane mene ne so ba, so ba ruwan shi da waye kai, wana matsayi ka taka a rayuwa, wace kala ce fatar ka, ya tsahon ka yake, ko ya jikin ka yake, da ya tashi shiga zuciya baya kwankwasa, fadawa yake cikin zuciya, ba notice," tabbas Lamyah ta fada tarkon son baqon da bata sani ba, dan na tabbata in da dane wannan cakwaikwaiwar take wannan zuba zamcen sai ta katse ta, ko ta bar wajen , amma wannan karon lumshe ido take tana jin tabbas in haka ake so to itama ta fada tarkon shi a farkon ganin ta da wannan bawan Allah da ko sunan shi bata sani ba, Farha ce ta katse ta, " Kar dai ki ce man tin da na fita har yanzu haka kk baki motsa ba, naje Bala baya nan Baba ya ake shi," ta qarashe cikin zumbura baki, kwantar da kan ta tai akan cinyar Lamyah ta juya bayan ta, Lamyah ce ta dora hannun ka akan ta tana shafawa," Farha me zai hana wani satin Bala ya kaini Rimin Gata? Na matsu na ga dangin Ammii na yanzu ko na gaggauta wucewa Niger neman Yah Amee, saboda Farha my heart us trying to betray me, tana son kuma ta ci amanar Yah Amee, tabbas in abinda nake ji ya tabbata zan shiga uku, Farha zan shiga matsananciyar damuwa, domin zuciya ta bata kasamce daga cikin masu adalci ba," Farga dake kwance tana lumshe ido jin kalaman Lamyah sai zuciyar ta tai sanyi, gaba daya tausayin ta ya kama Farha, musamman da taji ruwan hawaye a kafadar ta, miqewa tai ta zauna kusa da Lamyah sosai ta jawo ta ta dora kan ta a kafadar ta( duk da dai ba wani tsokar arziqi sai dai ma ta soke wa baiwar Allah kumatu da qashin kafada🙊) lallashin ta ta yi sosai sai da ta gama kukan ta sannan tace mata " Lamyah ki sani Allah baya dorawa rai abinda ba zata iya ba, wannan wa'azin ki ne, ina son kamar yanda kk fadakar da mu kullum ya zamana kema kina saka maganganun ki a cikin aiki inshaa Allahu zaki samu komai da sauqi, don Allah ya hore maki sanin daidai da kuma abinda ba daidai ba, sai ki gode mai ta hanyar amfani da su din, ina roqon Allah daya yaye maki damuwar ki Lamyah na," da Ameen ta amsa, sai taji zuciyar ta wasai, tashi sukai suka shiga daki, Lamyah ta fara fiddo masu da kayan da zasu saka da dare, wasu skirt ne masu hade da dan gajeren wando a ciki, skirt din iyakar shi guiwa, sai rigar da ba ta wuce masu cibiya ba, iri daga multicolor ne kayan, kusan kowacce kala akwai a jiki, amma ya sha adon stones, masu kyalli,n golden a jiki," wai ban gane ba kin kwanta?" " to mi zan, dan Allah barni na dan taba bacci kafin daten yayi, yau na gaji haka kawai nake jin gajiya , kewar Bala ta cikan zuciya, rabona da shi tin shekaran jiya fa," juyi tai ta kwanta abinta, Lamyah ta dakko masu takalman sunda zasu saka nan ma ta aje, sai abayar da zasu dora, tashi tai ta tafi kitchen ta dakko cucumber ta markade bata wani saka ruwa ba amma saida ta yanka qanana sosai, tana fara markaduwa sai ta debo madarar shanu, da zuma sannan ta saka kwai a ciki, sai dan tomeric powder da cinnamon powder da ta zuba, qara markadawa tai saida suka hade tsaf, sannan ta juyo a dan mazubi, dakin su ta koma ta dakko masu zannuwan da suka ware don gyara jikin su, dadawa Farha duka tai a yar cinyar ta da ihu kuwa ta miqe, dariya ta saka , ta miqa mata zanin, harara ta banka mata " dan cin zali kawai ina kwance har bacci ya fara dibata, ki makan duka a cinya sai kin lotsamin ita," dariya abun ya ba Lamyah sosai," me din zan lotsa kamar wata katifa? Ke ai sai dai a karya ba dai lotsawa ba," Farha ce ta biyo ta akan sai ta rama kuwa tun da abun haka ne, aiko suka fara zagaye dakin, da Lamyah ta samu dama sai ta shafawa Farha wannan hadin , sannan ta kwasa da gudu, a haka har suka gaji suka zube a gado, suna maida ninfashi, bayan sun sha dariyar su ne suka tashi kowa ta shafe jikin ta fea da shi," wai ni wannan kuma na meye, kusan kullum sai kin fiddo da sabon abu, duk lokacin gyaran jikin mu yai sai naga sabon abu kk fiddowa ina kk koya?" " a gaskiya a kwa wadan da Ammii na ta koyan, akwai wadan da da kaina na qirqira," " gaskiya na gode dan i want to look beautiful for Bala today, sai ya rasa gane wacece wannan, shin canjo ni akai," sai ta dira wani tsallen murna, Lamyah kada kai kawai tai tana murmushi, dan Farha na bata dariya, ko dake shima Balan ya mato akan ta ba kadan ba,dai dai sun gama ne Mubarak ya shigo, a duniya in yaga su Lamyah sun yi abunnan tsoro ke kama shi, aikk zaro manyan idon shi yai waje ya kama baki, juyawa zai da gudu ya fice aiko abokiyar fadan shi ta cafe shi, shafa mai tai a kuma tu, yana bude ido sika hada ido da fuskar ta da tashi, ya kwalla qara, yana qoqarin sauka, ta hana shi, sai tsorata shi take, Tani ce ta shigo ta karbe shi, " yaro gobe ma ka qara min rowar chocolate din ka, in ba sai na ma wanda ya fi wannan ba, ko kai kadai kk son yin qibar," " to laifi na je da komai kk ci baki qibar," ya fada cikin kuka sannan ga tsoro ar the same time, ai ko cikin fushi ta zabura zata damqo shi ya kwalla qara yace " Tani dauke ni kar ta kama ni," ba Farha ba har Lamyah dake gefe tana sha'anin gaban ta sai da ta sa dariya. Qarfe takwas da kwata a bakin mota tai masu, wani irin kyau da qamshi ke fita a jikin su, fuskar su tai wani haske mai bam sha'awa, ga shi ba tabon komai tai smooth, Farha na ganin Bala ta fara karairaya har suna hada baki da Mubarak," Bala my baby,"cike da tsokana Mubarak shima ya karye qugu yana yarfa hannu, yanda take yi, ya maqe murya shima sannan ya fada, aikk juyo wa tai zatai magana Lamyah tace," haba ke kamar baki san Mubarak ba, so yake ya bata maki rai, ko hirar ma da Balan ya gagare ki," kwafa tai ta juya tace "zamu hadu ne ai watarana," Bala ne ya qaraso cike da Fara'a ya iso, aiko tin da suka shiga ba abinda ke tashi sai surutun Farha, Bala shi ko dadi yake ji a ranshi, dan muryar abar qaunar shi ba qaramin sanyaya mai take ba, amma Mubarak da Lamyah sun juya idon su ya fi sau a qirga, a haka suka isa, Lamyah ce ta fito cikin faduwar gaba,yau kuma me za ta tarar, haka suka wuce dakin da suke shiryawa, ko ta ina ta wirga ido bata ga Handsome ba, Farha yau cewa tai ba inda zata tana wajen Bala zasui qala'in hirar da ba sui ba tin shekaran jiya, Lamyah ce tai ma Mubarak kiss a goshi ta tafi, tafe take cikin yanga, ta isa dakin da suke kwalliya, Faisal ne ya leqo, "ya kyakkyawar kin shirya ne," daga mai kai kawai tai,kamar yanda ta saba bata magana yauma haka, " ina Farha? Na manta ba ma magana zaki min ba muje kawai," ya sa ta gaba suka isa filin, tafi da ihun mutane ne ya sanyaya zuciyar ta, ji tai wani nishadi ya kama ta, dan ita abinda ke burge ta kenan, hawa tai cikin qasaita da isa, ta fara rawar ta cikin tsantsar kwarewa, da gwanancewa a kowanne stape ta dauka, ta shagaltu da rawa sosai, in da wasu maza su uku suka hada kai, ni kaina saboda qarar kida bana jin me sike fada, tafawa naga sun yi, sannan suka isa gaban ta, kudi masu yawa sosai suka watsa mata, dayan garin watsa maya kudin sai da yai dabara ya taba cinyar ta da ta fito, aiko ji yar kamar ya saka hannin shi cikin buhun flour dan laushi, ji.yai he wants more, qara miqa kudin yai ya shafo gefen qafar ta, nan da nan jikin Lamyah ko ya dau rawa tsoro ya shige ta, a hankali ta fara rage takun ta alamar ta kusa sauka kenan, ta tafi, dan gujewa wadannann mayun da ta kula sun sa mata ido yau, wandon shi har wani dagawa yake dan tsabar jaraba, lashe leben shi yake, yana mata wani irin kallo haka ma abokan shi, nan da nan kuwa ta sauka, tai hanyar tafiya wajen kwalliyar su, binta suka so yi amma suka dakata, tana isa jiki na rawa ta janyo abayar ta ta saka, Faisal ne ya iso da kason ta wanda a yanzu suna karbar wajen dubj dari da ashirin, saboda manyan yaran dake zuwa kallon rawa, nan take ta karba ta saka a jakat, wani guntun murmushi ta sakar mas, ta sa kai ta wuce shi cikin sauri, magana yake mata ma bata kula shi ba, a hanyar ta ta fita ne ta ci karo da wadannan samarin, kan ta daga kai ta ankara da su har sun zo dab da ita, shafo fuskar ta dayn yai," kaiiii yarinyar nan amma ke jinin indiawa ce ko? Ko larabawa, ko turaw? Amma dai ba bahaushiya ba, to wataqila bafullatana?" Dariya suka saka daidai lokacin da dayan su ya janye mayafin ta, gashin ta ya bayyana, ya rufe fuskar ta, kuka ta fara tana qoqarin yin magana ta roqe su ne, sai ga Ameenullah, zai zo leqen rawar ta, sannan ya kira Faisal, yana ganin haka kuwa da gudu ya isa wajen, bai tsaya bata lokaci ba wani bahagon naushi ya sakarma dayan da ya kai hannun shi jikin ta, sannan ya kama hannun ya ja gaba ya mayar baya da qarfi saida yai qara, aikk take wannan saurayu ya kwalla ihu, jin haka yasa sauran saka gudu, wurgashi gefe yai yana bins hi da wani mugun kallo, jan hannun ta yai suka bar wajen, motar shi ya wurga ta, fuskar shi kamar a kai ake tutu dan yanda ya bata ta, kwatancen da Faisal ya mai na gidan su a jiya wajen surutun shi ya ke bi,mamaki ne a ranta amma kukan da take yaqi qarewa haka suka isa gidan su, suna isa ya bude pin din bangaren ta, budewa tai ta sa kai ta fita, kan ta shige gida ta juyo da niyyar mai godiya cikin bacin rai yace," in da kin san baki kware a yawon karuwancin da kk fito ba da zaman ki kikai a gida, dan gaba ba abinda zai sa ni taimakon ki haka ta sake faruwa," da gudu ya ja motar shi ya bar wajen, cikin kidima da kalaman shi, masu qona zuciya ta shiga gida da gudu tana kuka wiwi, ga muryar shi da ta riki ta ta, kamar ta san muryar? To a ina?..... ... *Haermeen Haermmaerh na son ku da yawa, dan haka take sanar da ku cewar ko wacce mace ta iya creating abubuwan da suka dace tayi ba sai an zaunar da ita an koya mata ba, ke sa kan ki kina zaune zaki iya cewa bari na hada kaza da kaza na saka a miya naga yau ya zai, ko na hada kaza da kaza nai gyaran jiki na ko gidana ko dakina da dainsauran su, be more creative gurls, Allah ya hore mana fasaha da fahimta, Me Love u XX❤* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAN RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Page 15: Haka Lamyah ta kwana cikin tsananin baqin cikin kalaman wannan bawan Allah, da ko sunan shi bata sani ba, ga kuma baqar magana daya gasa mata, ga muryar shi da tai mata kama da ta san ta, to a ina? " kaiii this is so complicating," " meye yake complicating din sis na? Is it the fact that you run back home with out letting us know, or is the fact that i have come to understand cewar Handsome ne ya dawo da ke?" "Gurl pls kui hakuri, wani abu ne mummuna yaso samuna amma Allah ya kare wannan dan rainin ya taimakan," ta fada tare sa gyara kwanciyar ta, ," hmmmm kin san tashin hankalin da kk saka ni? I was so worried, ji nai kamar na sa hannu aka naita ihu, inna rasa ki a rayuwata ban san ya zan ba, na rasa kowa nawa, ina zan saka kaina," Farha ta qarasa tana kuka sosai, " kar ki damu my sis, kinji, qafata qafar ki duk inda zani, yanzu ma si nake ran asabar dinnan mu je dangin Ammiii mu ga ni ko za mu dace su karbi abinda ta haifa, wataqila sun sauqaqa min fayyace wa Mubarak mu su waye, in kin amince ko ina zani ke mai iya zuwa ce in dai ba Bala ne zai hana ki ba sai kui zaman ku anan,ke ko auren ki kina iya wa ki zaman ki nan," rungume ta farha ta yi tana mai zubda kwalla, dan yau surutun ta ya qare, ta samu sister from another mother, tabbas ta yard akwai masu kafa zumunci ba tare da sanayyar komai ba. Yau farha da asuba bayan sin kammala komai da suka saba, karatu, addu'a, azkar, bata koma bacci ba, wanka tai wa Mubarak, ta hada kayan su,Farha ta so bin ta, amma tace su je ita ta zauna ta kula da gida, bayan nan ma ya kamata ta ci gaba da zuwa rawa, dan so take in auren ta ya tashi, tai ma kan ta komai, zataji dadin hakan,sosai, suna kuka kamar wadan da aka ce ba zasu sake haduwa ba suka rabu, Bala na ta aikin ban hakuri, ya rasa wa zai lallasa cikin su, a haka ya ja mota suka dau hanyar Rimin Gata, suna isa, suka nemi a nuna masu gidan mai gari, nan ko aka kaisu, bayan 'yan gaishe gaishe da kuma tambayar su waye? Lamyah zama tai ta labarta masu komai da ta sani game da mahaifan nata, hawaye taga mai garin na sharewa, duk ya yamushe ya takwarkwashe," oh ni Haladu, ashe ina da rabon ganin zuri'ar Malam Muhammadu ta kwarai kuma a rayuwata? Wadan can yara nashi da suka rage 'yan asara, wahalallu da uwar su ta tsaya masu sui komai da suka ga dama, ko ganin su bana son yi, ina takaicin ace wai zuri'ar Muhammadu ne su, 'yannan Allah ya miki albarka, ya raya mana ku da imani, Allah ya jiqan iyayen ki, sallama akai tare da jinkirtawa, sai da akai mai izinin shiga sannan ya shiga, " Barka da rana Abba, ya kufan jikin?" " barka dai Musaddiq, jiki da sauqi alhamdu lilLAAHi, daga ina haka da uwar ranar nan, ko an kammala bautawa qasar ne yasaka dawowa?" "Eh Abba, nayi ta gwada layin ku jiyan na sanar da ku dawowa ta, sai inna kira yaqi shiga, nace kawai kun ganni," ya qarasa cike da fara'a addu'o'in alkairi mahaifin nashi yai ta mishi, shi kuma yana amsawa, gabatar masa da Lamyah mai gari yai sannan ya mai bayanin ta, dan yana da masaniya akan labarn Ameenee, da El-mustapha, daga kai sukai a tare dan su kalli juna su gaisa, Lamyah a kunyace ta gaida shi, shi kuma kasa amsawa yai saboda ganin tsabar kyau a tattare da ita, sai da mahaifin shi ya maimaita mai me ta ce sannan ya amsa baki sake kamar wawa, umarni mai gari ya mai akan yai leading din su ciki,Bala kuma zai koma a ranar, tare da mata alqawarin dawowa,shi da farha taga wajen, sallama sukai, Mubarak nata kuka, akan zai bi Bala, da kyar aka lallashe shi , Musaddiq ne ya dauke shi yana mai wasa, suka shiga ciki, shigar su ke da wuya, ya nufi dakin uwargida wato mahaifiyar shi da ita, qawa ce a wajen Delu, duk da halayyar su ba ta gama zama daya ba, amma kusan daya suke ta bangaren kishi, banda kishi bata da matsalar komai, bayan gaishe2 da gabatar da su Lamyah ne ya aje Mubarak yai dakin shi, yana shiga ya dafe qirjin shi, at d same time kuma ya daka tsalle ya fada katifar shi, " nayi mata nikam, ya Allah in wannan baiwa taka rabona ce Allah ka bani ita, innba rabona bace Allah ka musanyan da mafi alkairi," lumshe kyawawan idon shi yai, yana tinanin kyakkyawar fuskar ta, murmushi yai, yace " Lamyah" . Lamyah bata samu matsala ba a kwana hudun da tai a gidan mai gari, sai dai abu biyu kr damun ta, har yanzu ba'a hada ta da dangin mahaifiyar ta ta ba, balle kakar ta, sannan wannan dan mai garin fa na takura mata, da nacin kallo da magana, yauma zaune take tana shan Tea, ita da Mubarak, ya shigo, " A'a qanwata, me kk ci haka, ba gayya , miqa hannu yai ya karbi cup din hannun ta, ya daidaici inda ta saka baki, ya sha, tare da lumahe ido, a ranshi yana ayyana wataran fa bakin ta zan ji a nawa, da sauri ya bude idon shi, dan gudun. Kar ai abin kunya, sai yaji ma kamar ta gane me yace, kauda kai yaga tayi, cike da kunya tace, " Yah Musaddiq, ragowa ta fa ka shanye, kuma ni ai ban qoshi ba," ta qarashe cikin shagwaba, daidai nan Inno ta shigo ta same su, wani kallo tai wa Lamyah ta kauda kai, ta shige daki, kwalawa musaddiq kira tai, ya miqe yana cewa Lamya ta bashi 2mnts, kada kai tai tana mamakin yanda yake rawar qafa akan ta, " kaii me nake gani a can, wanan yarinyar mai kama da 'yar tsana tana yi maka," hade fuska yai sosai, dan yasan in yai lakwa2 wannan karon ma ba yarda za tai da zabin shi ba, a kullum tana mata biyayya amma bata gani, sai tai ta manna mai jikar qawar ta, Delu, Saddiqa, har wani kirari suke mata na Saddiqa amanar Musaddiq, ita kuma tai ta yanga tana rawar kai, 'yace a wajen Hamza, wanda ba abinda ya sani sai lalata yaran mutane, qanana, shi dayan tsabar shaye2 bama a san in da yake ba yanzu, kwata2 Saddiqa bata ji, bin mazan unguwar su kuwa kamar karya, ciki ta zubda shi yafi a qirga, ga ta ba arabi ba boko, in musaddiq na wannan complain din, Inno na ce mai nima ban arabin ba ban bikon ba kuma na haife ka, ya kanyi mata kuka akan ta barshi da zabin yammatan da yake kawowa na mutunci amma sam haka zata qeqasa qasa taqi, ga shi mai garin ma shi kanshi shakkarta yake ji, " da kai nake magana ka hade gira, ko kaima kanzama dan zamanin ne?" " ni dai a gaskiya wannan karon Inno dole a barni na zabi abinda nake so, dan wannan ma ba kamar sauran bace, inna hakura a bayan wannan karon ba zai yu ba," ya miqe cike da fushi ya bar dakin, kama baki tai, amma shakkar dakatar da yaron ta shige ta, dan ta san shi yaro ne mai biyayya, amma yau akan mave gashi yana neman juya mata baya, a haka ta ji ta tsani Lamyah, tsana mai tsanani. Yau ne da yamma Mai gari ya sa aka kira mai delu da Hamza, dan su shaida dawowar Yar uwar su dan sauran qannen mahaifin ta wasu sun riga mu gidan gaskiya,masu taurin kan ne ke da rai, take suka ce ai su sun ma manta da waye Muhammadu bare zuri'ar shi, Malam Abubakar ne ya zo shima idon shi yai ja alamar yai kuka sosai, kukan tinawa da Aminin shi, sun halarta a wajen, in da mai gari ya masu bayani, Musaddiq na gefe, amma hankalin shi na kan Lamyah, wannan ne yasa daga Hamza har Delu sukaji ko suna da niyyar karbar ta sun fasa, dan da ganin wannan kallon na so ne, yanda Musaddiq yaqi diyar su da can, yanzu tsanar ta zai, duk ko da kyaun da Allah ya mata itan ma, haka su ma suka nuna to dangij uban ta na haqiqa sun qi karbar jikar su balle ita, meye hadin su, dan ta kuma ba yanda zai ya dau wannan balagaggiyar ta kai gidan shi, kuka kam Lamyah tin da aka ce Bappanayen mahaifiyar ta sun qita ta fara shi, Malam Abubakar kam yai kukan rashin aminin shi, sannan yai masu barka da zuwa sosai, ya karbe su hannu bibbiyu, haka aka tashi taro Lamyah bata da madafar dangin uba. *Niger* " Haba Ameenullah, kaifa na kasa gane alqiblar ka, kwanaki har ka amince zaka auri yarinyar nan amma yanzu sam kace a'a akan me, to bari kaji, ka sauya tinani,san ba zamu zama qananan mutane ba, Lamyah ko ko yau ta bayyana na maka al'qawarin aura maka ita, amma wannan yarinyar nan da wata biyu kamar yanda mukai alqawari za a aura maka ita, Naufaliyya ya rinyar kirki ce, kusan ni dai ban taba jin ance ga matsalar ta ba, dan haka kai hakuri ai wannan al'amarin," tinda Baaba ya fara magana bai ce komai ba, haka Momma ta dora da nata,itama bai tanka ba, ba abinda yake hangowa face kukan Lamyah dake taba ran shi,kalaman da ya mata yasan basui daidai ba koda karuwa ce, balle Faisal ya gaya mai ko wanne daga halayen ta, amma tsananin kishin da yake halittar shi ne ya hana ya kasa daina hango ta tana tiqar rawa a gaban qatti, wani ma yasan in ya je gida da tinanin ta yake bacci, yana tina hakan yaisaurin daga kai cikin tsananin kishi yace," Baaba ni ku auran koma wace, amma dan Allah ku nemo man Lamyah itace cikon rayuwa ta," ya qarasa cikin hawaye, dan ko so da kishin waccen YAR RAWAN zai kashe shi ba zai aure ta ba, ba zai taba zama inuwa daya da ita ba.......... *Readers i am so sorry for the late update, those that ar worried about not seeing my post here i come💃🏻 thank u so so so very much for the love, i have been busy this past 2 days, but inshaa Allah, i will try as much as i can to update it for u, thank u so much again. HAERMEEN HAERMMAERH NA SON KU XX❤* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH page 17: Jitai an ja ta baya, dubawa tai taga Musaddiq ne, saka yatsan shi yai a kan lips din ta, idon shi taf hawaye, " da gaske kk baki so na? Son yaya da qanwa kk min? Kin amince na auri Saddiqa? Ko da bana son ta? Ki duba wannan lamarin fa ki gani ba a min adalci ba kwata2, in aka hada ni da wannan yarinyar sauran mazan qauyennan, ni na san nayi 'yan mata kala2, kuma soyayyar da ake gudanar wa ta zamanin nan na taba a baya, amma daga baya da ilimi ya shigeni na tuba, dan Allah ki yarda na aure ki," " Yah Musaddiq ba macen da zata ce bakai mata ba, amma ni matsalar da aka samu zuciyata cike take da rudani, ka tausaya min nima kar ka qaran akan na da, ka barni na koma inda ake mutunta ni, kaima ka fada ka taba soyayyar zamani amma ka tuba, to itama in ka aure ta da ilimin da kk da shi zaka ribace ta ka daidaita mata rayuwar ta, ka taimaka min ka ceci 'yar uwata, ka tina ita daya nake da ita a dangin mahaifiya ta da nake saka ran zan iya hada kai da ita, in ta shiryu, mu na sada zumunci a tsakanin mu, wannan jihadi zakai, tinda in kyau ne itama ba a baya take ba, kusan da kadan zan fita, halaye ne kawai bata da su masu kyau kai kuma zaka iya taimaka mata, plssss for me?" Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, idon shi ya kada yai jawur, ga qirjin shi dake dagawa saboda tashin hankali, ji sukai an saka ihu, da gudu suka fita, Farha suka gani ta shaqe Inno, tana dima mata duka, " an gaya maki jaka ce ita da zaki mata abinda kk ga dama, meye hadin ki da ita da kk da 'yancin ci mata mutunci haka, tinda nake da ita nasha ganin kukan ta ban taba jin irin na dazu ba, jakar ki ce da zaki sata a wancan madafin baqiqqirin, sai ko yau kin shiga na rufe ki in yaso iya azabar da kk ji wataqila kin gane Lamyah tana jin fiye da haka, tinda ko risho bata taba kunnawa ba," kakari kawai Inno take, da kyar ta furta," 'Yannan daga ina kk diro kamar aljana kk dukana, in mutan boye ne kui min rai ba zan qara ba, dama da ganin yarinyar nan jinsun su ce, na dade da zargin hakan, dan kyaun ta ya fi gaban namu mutane, ku taimaka kui min rai," Musaddiq ne ya isa da gudu ya kwaci Inno da kyar, dariya a cikin shi dan jin kalaman ta kamar ta kashe shi,amma yasan bai isa yin su ba,Lamyah kuwa wajen Farha tai dake ta masifa tana yarfa hannaye, fadawa jikin ta Lamyah tai, tana kuka, ran Farha qara baci yai ta banbare ta kuma yunqurawa kan Inno da sauri Lamyah ta riqe ta tana girgiza mata kai, " Farha ya isa mana, Main tek hain, mu je gida, ku dauke ni a nan garin, kui nesa dani, bana son qara dawowa in da ba su qaunata, ina son zuwa neman Yah Amee, in na samu Yah Amee rayuwata zatai dadi, komai na zai daidaita, Bala ku zo mu tafi pls," kamo hannun Mubarak tai dake taya ta kuka, fita zasui Farha tai dan zburar nan a gaban Inno, tako kurma ihu tana a ceceta, Farha ta dan sa yatsan ta babba ta shafe hanci da shi, tana wani baubbudawa, gaba daya Inno ta tsorata da lamarin wannan yarinya, wajen mai gari Lamyah ta so zuwa ta mai sallama, amma sam Farha tace ba za a ba, da dake mata iskanci ba yazama mijin tace ba bai hana ba me zasu je mai? Da kyar Lamyah ta shawo kan ta sukai mai sallama, ya basu hakuri sosai, Malam Abubakar ma sin yi sallama, a take a gaban Lamyah Misaddiq yace a sanar da su Delu ya amince zai auri Saddiqa, nannda wata daya, kowa yai murna amma ban da shi, zuciyar shi kamar garwashin wuta haka yake jin ta, haka suka tafi bayan musayar lambar waya, duk da Lamyah taci alwashin ba zata qara sati a Nijeria ba Nijer ta nufa. Bayan sun koma gida ne Lamyah ta qara basu labarin komai, da yanda 'yan uwan mahaifiyar ta suka ma qi saurarar ta, da yanda Delu ta qi amsar ta, da mutuntawar Musaddiq a wajen ta, sai yanda Inno ta wahal da ita bayan ta gano yanda Musaddiq din ke son ta, aiko kamar an sawa Farha barkono a duwais haka ta miqe tana" ni da baku raba mu ba na lallasa ta itama na danna ta a dakin girkin na rufe qofar taji ya abun yake, muguwa kawai, wayace dan ta ya nace maki," Lamyah ce ta kama ta ta zaunar da ita ta dora kanta a cinyar ta tai luf kawai, shafa kanta tai tayi ita kuma da sigar tausayawa, " Ya wajen rawar ki, kin ci gaba da zuwa kuwa?" " Eh ina zuwa, har Faisal ya sanar dani, Handsome yai aure a cannqasar su, nan da sati biyu zai dawo, mahaifin shi ne a nan yanzu," wani irin faduwar gaba ne ya kama Lamyah, yayi aure? To meye nata a ciki? Kaiii amma zafin da zuciyar ta ke mata in bata matse kwalla ba ba zata ji dadin zuciyar ta ba, ta shi tai tana masa fatan alkairi tai bandaki da sauri ta danna murfin qofar, kuka ne ya kwace mata mai cin rai, a ranta tana ayyana gwanda tai wannan kukan koma na meye, ko zuciyar ta ta huta, yi take tana sakewa, saida taji ranta yai fes ta wanke fuska ta fita, kwalli ta shafa ta bi lafiyar gadon ta kwanta. " zaki je ne? In zaki ga kaya na sayo mana, ki sa naki, dan na fada wa Faisal kin dawo," miqewa tai ta fara saja kayan, dan gwara taje ta cashe ko ranta ya mata dadi, bayan sun kammala ne, Bala ya debe su, suka fice, yau shigar larabawa sukai wa Mubarak, kamar yanda suka saka Abaya suma, bayan sun isa sun faka motar su ne, suka wuce kamar yanda suja saba, barka da dawowa Faisal ya mata, yai leading din su wajen rawar as usual, rawa take cike da kasala, amma yanayin ta ba qaramin burgewa yake ba, tana cikin yi ne nishadi na shigar ta, nan da nan yanayin rawar ta na sauyawa, ihu ake kamar zasu tsaga wajen, " Malam Sale dakkon jaka ta a mota ina jiran ka anan, na mance ta" ya kashe wayar, Mubarak ne da Farha ke guje2 kamar yanda suka saba, karo Mubarak yai da shi, aiko ya qanqame shi," pls ka taimake ni, wannan qashi da ran zata daken," dariya sosai ya ba bawan Allahn, aiko daha shi yai sama dan ya mai magana, me zai gani....... 😱😱😱😱😱😱😱😪😪😪😪😪😪😪😂😂😝😝😝😝 [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Page 16: An daura auren Ameenullah da Naufaliyya, yau ne tarewar su, a fuska da yanayin ta kowa zai budi baki abun alkairin ta yake fada, yarinya ce nutsattsiya. Ango da amarya na hango sun yi sallah ya mata addu'a kamar yanda sunna ta koyar da mu, sai nonnoqewa take, Ameenullah ne ya miqe ya je yai wanka a dakin da yake nashi, ya gyara jikin shi, futar shi ma amarya ta miqe ta dakko wasu turaruka ta saka amma ni dai ban hango ta tai wanka ba balle brush, haka ta saka kayan bacci ta miqe a gado, Ameenullah ne ya shigo dakin cikin sallama, tana ji ta qudundune tana wani noqe kai, bayan ya qarasa shigowa ne ya dage abun rufa ya shige, wasanni ya fara da ita, amarya ta fara miqa , tana gantsare jiki, tin tana jurewa taga inaaa, wannan kunyar bazata iya jure ta ba, Ameenullah ya hadu, shi kuma ta nashi bangaren wasanni yake da ita, amma zuciyar shi da idanun shi tare da ruhin shi 'YAR RAWA Lailah ce a idon shi, cikin tinanin da yake qoqarin kawarwa, ya fara addu'ar saduwa da iyali, yana shiga yaji sabanin abinda yake son tarar wa, amma wasannin da take mai, da kuma asirin da sukai mai ita da mahaifiyar ta na daya sadu da ita ba zai taba daga maganar budurcin ta ba, shine ya shige shi, qasan zuciyar shi yana jin zafin samun iyalin shi ba a matsayij budurwa ba, amma ya furta ko ya nesanta da ita ya kasa, sai ma ji yake sha'awar shi na qara rising, yi sukai tayi har wajen 4am na asuba, sannan ya miqe ya je wanka, zuciyar shi cunkushe da abubuwa, kwata2 ba farin ciki ko walwala, a tattare da shi, wanda ya kamata ya samu farin cikin ne a matsayin shi na ango biyo shi wankan tai, ba kaya a jikin ta, tana wani yanga, a wajen wankan ma sai da ta shagaltar da shi, kiran sallah yaji za a shiga masjid yana manne a HQ bai ma gama kusantar ta ba balle yai maganar wanka ko sallah, da hanzari ya zare jikin shi ya gaggauta wanka ya fita haushi duk ya kama ta, qunquni tai tayi kafin ta fito, madadin ta qarasa wankan tinda ta jiqe ta koma tai sallah in yaso tai baccin inaaa, gado ta koma a hakan, ta kwanta tana jiran ya dawo su dora daga inda suka tsaya,.ba shi ya dawo ba sai wajen 7am, dan saida ya kammala duk wata ibada da ya san yana yi da asuba, aiko ranta ya kai qololuwa wajen baci, ko da ya dawo yana mata maganar tai sallah? Banza tai da shi, ta juya ta kwanta, matsawa kusa da ita yai yana shafa bayan ta zuwa qugun ta, bakin shi akan wuyan ta, nan da nan ta juyo, ta hade bakin su, kamar mai jin tsananin yunwa, Ameenullah tsananin mamakin yarinyar da ake cewa saliha yake, zaro ido yai, yana qarewa bayan ta da take turawa baya sosai ido yai, " Anya yarinyar nan ba a hadani da wahala ba? Kar ta tsotsen jini a kwanakin da zan kan na koma Nijeria," shafashi kawai yaji tana yi ko ta ina, tin ba ya da sha'awa har sai da ya tsinci kan shi da son abun shima, da kyar ya samu ta kyale shi, sukai bacci. Ba su suka tashi ba sai wajen 1pm suna tashi yaje dakin shi yai wanka, yai brush, ya canja kaya ya tafi masjid, a sannan ne hakimar ta miqe taje tai wanka, tai brush, a saja kaya masu matuqar kyau da nuna tsiraicin ta, komai nata qarami ne, hatta gashin ta guntu ne, saidai fara ce kuma bata layin munana, sannan bata layin kyawawa, sadda sadda inji fulani😀, ba zancen sallah ita a tattare da ita, kitchen ta je ta dudduba abubuwan ciki, kwai kawai ta soya masu ta hada Tea, sai bread data sa masu a gaba, nan ko ta hau ci dan maida energy😀 tana kammalawa ta muqe a wajen, bacci ne ya dauke ta, Ameenullah na shigowa yaga yanda ta ke bacci dariya ce ta kama shi, " Yarinya qarama sai jaraba, ga shinan daga cin abinci ta bige da bacci, habaa, ayi mutum bai san komai ba sai dai aita abu daya kamar cin kwan makauniya?" Shima jan plate din mai kwai yai ya ci ya hada Tea ya sha ya miqe ya dauke ta ya maida ta daki, shina ya kwanta, baccin su suka koma sosai, a ranshi yace" gwanda nai baccin nima kan ta farka, dan na kula wannan komawata Nijeria shine zai cecen, kan na koma ta zuqe ni," baccin su suka sha sadidan, a haka sai da sukai sati biyu masu kyau, suna shan amarci, gaba daya halayen ta ba wanda basu fitowa Ameenullah ba ya gan su,na farko bata sallah, sannaj ga ta da son xxx, ga rashin iya magana, gata da qazanta, rashi iya girki, kwalliya kam tana gaba, yanga ma haka, kwarkwasa da fari ba a barta baya ba, amma qazantar ta da rashin sallan ta yafi komai damun shi, dan abinci dama ya saba a gida ma Momma Aisha ba ta qaunar girki, masu aiki ke masu, to ita wannan tsabar kishi ta hana a dakko mai aiki, a wannan satikan mahaifiyar ta, ta zo kusan sau biyu, ba komai take kawo mata ba illa magungunan mata, sai na mallaka, su basa asiri akan komai ma miji sai dai su malleke shi ya zama nasu su kadai, a haka suke wanda shi cikin ran shi, sam baya son Naufaliyyah, Lamyah yake so, amma a qasan zuciyar shi, ya fi son kasancewa da 'YAR RAWA Lailah, dan ko kalmar so din ya furta ba wanda yake gani sai Lailah 'YAR RAWA, ko sha'awar shi ce ta motsa ita kawai yake son yai maganin komai da ita, ya rasa yanda zai ya cire yarinyar a zuciyar shi. *NIGERIA* " Ai sai ki fito waje ki kama min ayyuka ko? Dan banga amfanin zaman ki a daki ba, bayan dangin naki karankaf sunqi qiba," Lamyah ce ta fito tana share hawaye, fuskar ta tai jawurr kamar ta shafa wani abu, takalmin ta ta zira, ta isa gaban Innoo, " Gani inno me zan yi yanzu?" " au tambaya ta ma kk me zaki? To tashi na kai ki madafin ki ga me zaki," kitchen din gargajiya ta kai Lamyah, aiko suna shiga ta fito da gudu tana.nemk iska, hade da tari, " Laaaaa ji iskanci, kuga mun yarinya zata mun tijara, hayaqin ne baki taba shiga ba ko meye sabo wajen ki? Kun wuce kinje jun tuqe tuwon nan tas ko sai na yanke maki shegen gashin nan da kk taqama da shi?" Shiga ta qara yi tana kuka mai cin rai, data san haka ne da bata zo ba, gashi nan da Bala ya dawo ta umarce shi sai nan da wata daya, , gashi gaba daya kwanan ta takwas, kuka ta sake fashewa da shi, na tausayin kan ta, " Abiii, Ammiii da kuna nan da rai da ban shiga wannan wahalar ba, da ban soma ganin kalar wannan wajen ba ma, amma ya Allah ka shaida zan yi wannan wahalhalun da suka kunno mij ne domin ka, Allah ka bani qarfin iko ka sauqaqa min komai," " Qunquni kk min haka dan na saki aiki, shigowar Musaddiq kenan, aiko tana juyawa da niyyar dakko ruwa ta watsa mata ta gan shi sai ta wayance da goge fuska tare da sharce majina, ita a dole Lamyah ta sata kuka, qarasawa yai ya janyo hannnun Lamyah data fara tuqa tuwon, ya fiddo ta waje, " daga yau sai yau, na sake ganin kina irin wannan aikin sai na mugun saba maki , kinji ko baki ji ba?" Ya daka wata gigitacciyar tsawar da ta saka Inno dafe gini, dan tabbas Lamyah yake kallo yake magana, amma ta wani bangaren kuma ya tauna tsakuwa ne dab aya taji tsoro, Lamyah kuwa dan tsoro durqushewa tai a wajen tana kuka, kuka take sosai cike da tsoro shi, a hankali ya dago ta ya sa ta gaba zasu tafi , cike da kishi sai kace wani mijin ta, " Malam ai sai ka sake mata hannun ko? Tin da naga ba sarki ko limamin daya daura maku aure ko?" A sannan ne ya kula da yanda ya riqe Lamyah da ta gama tsorata, da firgita da shi, sannan ga tsoron shigar ta kitchen din nasu da bai sake ta ba, yaga tabbas in ya sake ta tana ma iya faduwa, shiru yai ya kyale Inno tana sababi, daf zasu shiga dakin ta ne taji Inno nacewa," kaqi sake mata hannun ko? To sai dai ka canja masu wajen kwana ita da qanij nata, amma ba dakina ba, munafukai, anya Musaddiq wannan aljanar yarinyar bata rude ka ba ka salwantar da kan ka a wajen ta?" Wannan furici ba Musaddiq ba har sauran kishiyoyin ta sai da ya daka, amma an tsoron iya inji 'ya'yan mayya, ba wanda yai magana sai ma shigewa dakunan su da sukai, Lamyah ce ta kwace jikin ta ta fada dakin da gudu, ta dakko wayar ta ta kira Bala, tana kuka ta kasa magana, hankalin shi ya matuqar tashi, yana tare da Farha, da kyar ta labarta mai komai, tace karya bari Farha taji, bata san a kunnen ta akai komai ba, ta cika tai fammm, hawayen itama ke na jin rashin imani na wadannan mutane akan marainiyar Allah, aiko rufe qofar motar tai tace " muje" tare da jan hancin ta, ta share hawayen ta, Baka kam kasa mata musu yai, dan shina zuciyar shi tayi Rimin Gata. Hankalin Musaddiq ya tashi jij wayar da Lamyah tai , tabbas yasan yau zai rabh da ita, cike da tashin hankalu ya isa gare ta, " haba Lamyah, in baki hakuri ba kin facing yanayin rayuwar da Allah ya tsara maki ba ta ina zaki fara cin jarabawar Allah a kan ki?" " Sam wannan ba rayuwar da tazo man bace ni na kawo kaina, sakamakon son dangin mahaifiyata, da ban zo ba da ina cikin walwala da nishadi, da ban zo ba da ina tare da masu so na ko da ba jini daya muke da su ba, a qarqashina suke, amma soyayyar su ta wadata a gare ni, ka je kawai musaddiq, yau Bala zai mai dani gida, ba zan zo na zama sanadin hadaka da mahaifiyar ka ba, kai mata biyayya ka auri Saddiqa, kai za ka iya gyara ta a matsayin ta na jini na , ka taimaken kai sanadin shiryuwar ta, Allah zai baka lada mai yaw, kar kai tinanij rayuwar da tai a baya, ka aure ta domin Allah, i am sorry to say,ni dama kaga tin fari ba wai ina maka son aure bane a matsayin yayana na dauke ka,..." kafin ta ci gaba ya fuce a dakin kamar zai kife, ganin haka yasa Inno farin ciki, ta shiga dakin, " habaa yarinya, ai wanda yace zai cituwon inno zallar muya kawai yake sha, ke a suwa, zaki zo rana tsaka ki sa dana ya fara bijireb sannan kuma na yarda ya aure ji? Ai ba zai yu bq, gwanda ki tattara ku bar gidan tin kan rai ya baci?" Cikin kuka Lamyah ta juyo ta kalle ta, ta mata wani kallo da bata san ta iya shi ba ma, ta juya ta hade kayan su tsaf, Mubarak ta dau maya fi zata leqa ta kirawo, tana leqawa soron ta............ 😱😱😱😱😝😝😝😝😝😝😝 *lols just chill guys Lamyan ku na nan lfy tana gaida ku* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH page 18: "El-mustaphaaa?" Shine abinda bawan Allahn nan ya furta kawai, da sauri ya hau jujjuya Mus'ab yana kallon shi, ganin haka ne yasa Farha miqa mai hannu akan ya bata Mubarak, gaba daya ta tsorata da ganin canjin mutumin a lokaci daya, ga shi ya fara zubda hawaye sosai, a firgive tace," Malam bani qanina mu tafi meye haka, ko an fada maka nan wajen makoki ne?" Fizge Mubarak tai wanda shima a yanzu ya fara tsorata da mutumin, tabba Baaba Mus'ab ya san wannan yaro jinin abokin shi ne, to amma ina Lamyah, dan wannan ba ita bace, ya san Lamyah ta hanyar hotuna, da kuma zuwan da sukan yi Dubai lokaci zuwa lokaci, anan ne sukai mata alqawarin boye wa Ameenullah ita har sai yaje da kan shi ya ganta ko kuma ita taje Nijer, " hukumullahu laa ajabun, wannan yaro tabbas dan Aminina ne, baiwar Allah ki taimaken ki sanar da ni ina zan ga AISHAA LAMYAH,," jin ya ambaci haka ne, Farha ta matsa kusa da shi sosai tace," kaiiii malam dakata kaji, ni fa da kk ganina hakan nan kar ka nemi kawon raini, ko wani 419, karrr nake ganin mutanen duniya yanzu, in ma wani tuggun ka ke son hadawa to bari na fada maka ka kiyayen, dan in daki qato ni ba wani abu bane waje na, a ido ne zan maka kamar va zan iya aikata hakan ba, amma duk wanda zai taba Lamyah a shirye nake dana sadaukar da rayuwata dan kare ta ta," " tabbas kin cika masoyiyar gaskiya, amma baiwar Allah ki taimake ni ki taimaki Lam......." wata murya mai zaqi suka ji daga bayan su, an kwala kira da " Baabaa" juyawa suka qarayi dukkan su ,Farha tin kan ta juya ta san mamallakiyar muryar, Baabaa Mus'ab da gudu2 ya aje Mubarak itama da gudu sosai ta isa gare shi ta fada jikin shi tana kuka sosai, kuka suke ba qaqqautawa, Mutuwar aminin shi ta dawo mai sabuwa fil, ita ma mussing Abii din ta take, da Ammii sannan ga farin cikin ganin Baaban ta, tabbas tasan a yau ta gama ganin Yah Amee din ta, sannan ta san Allah baya bacci, Allah yana amsa addu'ar bawan sa da ya yarda shi Allah ne, ya yarda da ya roqe shi akan komai ya kwantar da hankalin shi ya jira sakamako daga mai dika, Lamyah imanin ta ya qaru akan na da, domin tai wa Allah godiya a wannan lokaci yafi a qirga, Farha ce ta je ta kama hannun ta," can u guys pls tell me what is going on here?" Murmushi Baaba yai dan ya san wannan tabbas ba a taba Lamyah gaban ta mutum ya sha, kuma a yanda ya kula tana da kusanci da Lamyah in ko haka ne to tabbas yasan ta san ko shi waye," 'yata ni ne mahaifin Ameenullah, Yah Amee din Aishaa Lamyah, " ai ko wani tsalle ta daka ta dane Lamyah, tana murna, sai ga hawayen taya Lamyah farin ciki na bin fuskar ta, tare da hawayen tinanin tabbas rabuwa da qawar ta kuma 'yar uwar ta yazo, kukan ta qaruwa yai da kyar Suka samu tai shiru, Faisal ne ya qaraso da kudin Lamyah," to ni da kk bar min kudin me zan da su, kin san yau kin fi burge kowa wajen nan dan haka ne kudin suka fi na kullum kar....." maganar shi maqalewa tai ya duqa qasa yana sosa kai," Baaba barka da zuwa," qasan zuciyar shi yana mamakin ganin Lamyah a jikin Baaban abokin shi, ga Mubarak da farha a gefe idon farha ta sha kuka, shima haka da Lamyah, ," kudin meye kk ba 'yata Faisal?" In ina Lamayah ta fara, ta amshe kudin tai wa Faisal sai da safe, a haka Baabaa yace ba zai bar Lamyah tafiya ba tare da yasan inda take ba, nan take yai ma drivern shi waya yazo ya shiga motar shi da Mubarak da Lamyah ita kuma farha suka tafi da Bala, tun da suka shiga motar Farha ke kuka, ba irin lallashin da Bala bai ba amma taqi shiru, hankalin ta ya tashi matuqa, dan tasan tabbas rabuwar ta da wani bangare na jikin ta ya sake zuwa mata, nan take kan ta ya dau ciwo, zazzabi ya rufe ta, Bala ma hankalin shi a tashe yake ga masoyiyar shi ba lfy, kuma komai kan idon shi ya faru, ya tabbata rabuwar shi da uwar dakin shi yazo, haka suka isa gidan kowa da abinda yake saqawa, bayan sun shiga ne, suka nufi ciki, inda Baaba ya kira Baba mai gadi, bayan sallama da yai ya sanar da su yana son nan da kwana sha daya zasu tafi da Lamyah, nan take wajen ya kaure da koke2 Baba mai gadi kan shi hawaye yake,anan Baaba ya fuskanci lallai Lamyah yarinyar kirki ce, tai halin iyayen ta, " kar ki tafi ki barni 'yar uwa ta,in kk tafi za sake komawa cikin maraici ne, ki tausaya min , ko aure na baki gani ba zaki tafi kwanakin sun mana kadan Baaba," kuka take sosai Lamyah ma kukan take, sun manne juna kamar wadan da aka ce tafiyar yau dinne, ," ku dakata, wannan kukan da kuje ba magani bane ba fa, ke an kusa auren naki ne? Waye manemin naki, na roqa a kusanto da auren, dan kuwa tabbas zan tafi da 'yata da dana, ba zan bar su anan ba ba su da kowa, ko me ake. Buqata a auren ki na dau nauyu, ke koda mijin ne bai shirya ba, domin ke masoyiyar diyata ce komai zan iya maki," Baba mai gadi ne ya nuna mai Bala a matsayin mai neman auren ta, ya sanar da shi matsayin karatun Bala, da aikin da yake a gidan, yaji dadin hakan sosai, yace to ai abu yai kyau duk gida ne ma, dan haka a na sauran kwana goma zasu tafi za a daura auren, ta tare a randa zasu tafi, in yaso sai su zauna a cikin gidan kawai, sun yi murna da hakan sosai, amma fa banda Farha, dan ita yanzu ba ta da sauran murna sai tashin hankalin rabuwa da Lamyahn ta, ko daga kai batai ba, Baaba ya fuskanci hakan ya sa yace," to ku naga sai murna kuke anaryar ma naji tace ta fasa a ba wa Bala wata ya aura," da sauri Farha ta daga kai tace," yaushe mukai haka da kai," cike da zaro ido, aiko nan take wajen ya kaure da dariya,kunya ta kama ta ta miqe daki da gudu, Lamyah ma bin ta tai, sukai ta dariya, tare suka dawo, kitchen suka shiga suka debo mai abinci da kayan motsa baki kala2, dama bai ci abinci ba nan take ko ya ci ya qoshi, sannan sukai sallama akan gobe zai dawo, bayan ya tafi ne suka zauna suna ta tattauna yanayin yanda komai zai tafi, Bala ne ya fara hamma yai masu sai da safe, kafin Lamyah tace," to amarya aiki ya samen ya kamata na fara gyara ki kamar Yanda Juwaireren mama na ga tana gyaran jiki kema haka zan din ga maki," miqewa Farha tai ta shige daki tana qunquni, " ba sai ki gyara nin ba tinda ni daya ce amaryar? Kema kina zuwa za sui ramm da ke a ba Yah Amee din ki, kunqara ta can," " Farha me kk cewa ne, kin san ban son kina magana qasa2 dan na san halin ki sai ki zage ni tass ta haka ina nan baki bude," Farha bata ankara ba taji duka a baya, dama a wuya take, kuma tafi Lamyah qarfi, kokawa suka fara cikin daren Mubarak da yau idon shi ya soye ya fara dariya yana " Yauwa qashi da rai, cika mata aiki, ke kuna kumburin buredi zaune ta," suna jin haka suka saki juna sukai kan shi, yana ganin sun yo kan shi ya zare ido ya dora hannu aka yai hanyar fita da gudu, sai dakin shi, kan su isa ya sa key, yana dariya, yana qara tsokanar su, kowa a cikin su ta tsani sunan da yake kiran ta da shi, a haka suka je sukai wanka sukai addu'a suka kwanta. Shirye2n biki sosai Lamyah tai wa Farha, qawayen su na wajen RAWA suka gayyata, harda yan baqin cikin su, sai da suka gayyata, su kuma suka ci alwashin zuwa ko dan suga dame yaran ke taqama su ke nuna su wasu ne. Farha ta sha gyara wajen Tani da Lamyah, Lamyah kullum sai ta kwadan ta mata zogale danye da manyan timatir, da kuli , ai ko nan da nan Farha hips din ta ya fara fitowa, ita kuma Lamyah ta dage da gyara belly din ta dan so take a bikin Farha ta cashe rawar da bata taba yi ba, hakan ne yasa take shan gwalba wadda ake hadawa da nono amma bata sa nonoj haka take jiqa ta ta murje kwallayen tana sha bayan duk wanu cin abinci, nan da nan kuwa tumbin ta yai qasa, ya dada shigewa yai flat yai kyau, ita kuma Farha sai Lamyah ke bata kwalbar bayan ta saka mata madara a ciki, na musamman ta sa aka yo mata dakan hannu na busasshiyar aya da kayan qamshi a ciki, da minannas, sai dabino busasshe, da madarar shanu da zuma Lamyah ke hada ma Farha ta sha, amma wajen shan kullun sai an kokawa, dan Lamyah ma cewa take sai ta sha," yacin kk sha kema sai an miki auren,ke za a aurar ko ni, ni ban gane ba , in aka zo ci ko shan me dadi kina gaba, in aka zo masu daci da bauri ki noqe, kaji min yarinya , ni gaskiya Tani na min wariya," dariya suke sakawa sosai, aiki duk randa aka ma Farha hadin tsumi masu bauri baurin nan, sai ta danne Lamyah ta dura mata, in taqi taita soka mata guiwar hannun ta a cinya, ita kuma abun dariya yake bata, kamar cakulkuli, a dariyar nan zata samu ta dura mata, sai ta gama sha tai allah ya saka mata, " zai saka miki mana da alkairi randa Yah Amee ya same ki a matsayin mata," ai ko da taji haka farin ciki na kamata sosai. A kwana a tashi a sarar mai rai( Allah ka bamu sa'a ka sa mu cika da imani, Allah ka sa mui kyakkyawan qarshe ya rahman) a yau aka daura auren Bala da Farha akan sadaki naira dubu hamsin, wanda Baaba Mus'ab yai ma Farha waliyyi, Baba mai gadi ya karba wa dan shi auren Farha cikin murna da jin dadi, mahaifiyar Bala ta halarci auren, bayan kowa ya watse ne, aka bat Lamyah da Mubarak, da Farha, sai Tani dan itama a gidan zata kwana yau, kuka kowa yake kamar wadan da akai wa mutuwa, yau Mubarak ne jikin Farha lafiya laou ba rikici bate doke2, ya qanqame ta yana ta ta aikin kuka, Tani ce tai jarumtar miqewa tace," ku mui hakuri,mu zamu ba kan mu hakuri, tafiya ai ba mutuwa bace, za a na gana wa duk sanda aka so, an bamu adireshin ku na can, ga lambar waya, sannan kuma gidannan dai yana nan ba inda zamuje dan zan ci gaba da aiki anan, duk sanda taso ganin munza ta zo gare mu, dan haka kumu tashi mu fara hada kayan nan, " miqewa sukai jiki a mace suka hau hada kaya, sai da suka gama tass Lamyah ta je inda ta adana jakar da Abee ya bata ta dakko, ta dora kan akwatinan kayan su, wankan kwanciya sukai, kowa taje ta kwanta, ranar farha da Lamyah a manne da juna suka kwana, cikn dare Farha tai ta masifa a cikin bacci wai ba za a tafi mata da qawa ba, Lamyah tai murmushi mai cike da hawaye a idota sauka gadon tai taje tai alwala tai nafil2 tai addu'o'i kamar yanda ta saba yi a duk sanda wani abu zai sameta, sai ta mai addu'ar neman zabin Allah. Da safe kam an sha kuka da bori wajen farha, da kyar su Lamyah suka bar gidan, Bala ma sai sharce kwalla yake, ga tausayin amaryar shi,ga kuma tausayin su duka, na rasa uwar daki mai adalci. *NIGER REPOBLIC* ...............................😝 [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Page 19: Da gudu ta qanqame Momma, a tare suka fashe da kukan farin ciki, kewa, da kuma rashi, Baaba bai hana su ba, sai da suka gaji dan kan su sukai shiru, sake Momma tai ta fara leqa makeken parlon tana kwala ma Yah Amee din ta kira cike da farin ciki da zumudin ganin shi, a sannan ne fa hankulan iyayen biyu ya tashi, dan tabbas in Lamyah taji yai aure ba zaman lfy, to amma ya zama dole su sanar da ita, kamo hannun ta Momma tai tana shafa fuskar ta cikin kulawa," 'yata ki ci abinci, ki wanka, ki dan huta mana sai kiji ina Amee din ki yake," girgiza mata kai ta soma, idon ta cike da kwalla sannan tace," A'a momma, ni ina son na gan shi yanzu, ina son na fara bashi daddadan labarin da ya dade kunnuwan shi na son su saurara, na gaji da aje wannan sirrin dake raina, abubuwa da dama na yawo akaina,ina cikin rudani, bana son wani matsala ta faru daga bangare na," a hankali Momma Aishaa ta share hawayen da ya gangaro mata dan tabbas ta san yau akwai daru, sun so just for today, Lamyah ta huta, kafin a bata labarin komai amma inaa........... ...... Ta bangaren ango da amarya kuwa ana nan ana kan aikin da aka saba, da kyar ya samu ya sulale gefen ta, yana maida nunfashi, kamar wanda yai gudu, zufa kawai yake kamar manomi, ita ko sai wani yauqi take, ta dora kan ta a qirjin shi qafar ta a kan tashi, hannun ta na wasa da gashin qirjin shi, a hankali can qasan maqoshi ya fara magana," ki shirya na kai ki gidan mu, ku gaisa da su Momma, dan ni nan da kwana hudu zan koma Nigeria, kuma nan gida zan barki, amma in kina so, zaki iya na maida ki gidan mu, ki zauna bangare na har na dawo, dan nan ke daya ba zaki so ba," wani irin a bu ne ya tokare mata wuya, yanzu duk dadin nan da take kwasa tafiya zai? Ita ya ma za ai ta barshi tafiya shi daya yai watanni baya nan? Ya zata iya sabo da rashin shi bayan ya saba mata da jikin shi? A gaskiya da sake, ko ya tafi da ita ko ya maida ta gidan su, kaiii anya zata iya zama kuwa? Wadannan tambayoyin ne ke mata yawo a kai, sai da taji ya shafo gefen cikin ta, wani dan juyi tai a jikin shi, yana ganin haka ko ya qoqarta miqewa, ya san halin ta so take su koma ruwa," ki shirya bari na je na shirya a dakina zan jira ki in kin gama ki mun magana," ai kan tai wani yunquri ya fice, yana shiga dakin shi yai ajiyar zuciya, ya danna key, toilete ya shiga, ya sakar ma kan shi ruwa, zuwa tai qofar dakin shi din ta rufe sannan ga qarar ruwa, tsaki ta ja mai qarfi ta juya ta koma, toilete ta fada itama ta shirya, cikin wani material mai tsada da kyau kalar baqi mai ratsin yellow a jiki, tai kyau daidai ita, ya gama shiryawa kenan suka jero suka dau hanyar gidan su. ......... " Baaba ku fadan ina Yah Amee na yake pls, i really want to see him," ta qarashe cikin hawaye masu dumi, sallama suka ji gaba dayan su suka juya, gaba dayan su su biyun ido suka zaro a tare suka nuna juna," kaiiime kk yi anan?" " keee me kk yi anan" nan take yace " ke zan tambaya," " ko dai na tambaye ka ba don nan gidan mu ne, ga Baaba na da Momma ta, kai fa me kazo yi?" Wata dariyar rainin wayo ya saki, sannan ya wuce ta ya kamo hannun matar shi sukai ciki suka zauna kan kujeru, qasan zuciyoyin su ba qaramin murnar ganin juna sukai ba,dan zuqatan su sun yi kewar juna sosai, Baaba ne yai ma Momma nuni da suma su zauna, zama sukai Baaba yai gyaran murya, sannan yace" yanzu dai na ga alama kamar kun san juna , amma ba damuwa, komai zai zo da sauqi da ikon Allah, ammmmmm Ameenullah ya iyalin ? Ina fatan kuna nan lfy?," kan su Lamyah ya kulle sosai, wannan ba abun da za ai shiru bane, a ina Baaban shi ya san wannan tijararriyar? Har take ikirarin su a iyayen ta? Amma zai bi yanda suke so, amsa mai yai, da tana lfy, suka gaisa da Momma da itama abun ya mata daban, kamata yai a zauna ai ma kowa bayanin juna, sannan a warwarw komai amma Baaba ya kawar da zancen, bayan gaishe2 ne da akai, wanda in da sun kula da Naufaliyya zasu ga yanda ta cika tai fammm,dan zuciyar ta ta gama amince wa zama anan in yai tafiya, a da kam tana tantama, amma yanzu ta amince, musamman da taji Baaba na duqunqune zance, wannan mace da kyau kamar ba jinsin mutane ba, ina za ta yarda ta zauna a gidan su mijin ta, salon mijin ta ya na zuwa gaida iyayen shi tin bai son ta ya kyasa? Inaaaa ba da ita ba gada a qabari, sannan ga dikkan alamu sin san juna ma, tabota taji an yi, ta juya sashen shi, taga yana mata nuni da Momma, duqar da kai tai ta gaida ta, itama amsawa tai, idon Lamyah na kan na Ameenullah, shima haka, ko wanne da abin da ke saqawa, shi tashi cike take da farin ciki zullumi, fargaba, da rudani, ita kuma tata cike take da tsananin tsoro, kar dai ace wannan ne Yah Amee din ta, ga shi da mace, lallai da ta mutu, abu biyu sun hadu mata kenan, ga shi shine Yah Amee din ta, sannan kuma mutumin da yai mata satar zuciya ba zato ba tsammani, "Oh yau ya zan yi" shine a bin da ta furta ba ta san ya fito fili ba, kallon ta kowa yai, nan take ta tsume ta dau jakar hannun ta ta koma kusa da Momma, kwantar da kan ta tai kafadar ta tana shagwaba," Momma zan shiga na watsa ruwa ina ne dakina?" " Ya kama ta kam tashi mu je na nhna maki," tafiya suka kama, mamaki ya kashe Ameenullah, na ina suka samu wannan daha zuwa ji uanda take neman kwace mai waje, tabbb inaaa ba zai yu ba,da sake, to shi in ya tashi shagwaba yai a ina, wannan baligar da ta yi a kai ta daki ta cinye mai waje( ni kuma nace kai baka ji kunya ba risheshe da kai kace an cinye ma waje😂😝)bin su ya tashi zai yi Naifaliyya ta riqe hannun shi tare da murza cikin tafin hannun shi tana wani kashe ido, da lasar lebe, nan take yaji kasala ta rife shi, ya koma ya zauna, Baaba da ya kula da me ya faru ya girgiza kai yai layar zana. Baaba ne da wasu abokan shi biyar, sun taru, shigowa ta qarshen zancen su naji, inda naji Baaba yana " Alhamdu lilLAAHi, yanzu da ya dawo tinda an daura, sai a kai mai amaryar shi," sauran ma murna suka taya Baaba na dawowar Lamyah da kuma daurin auren da akai kan in iso na Lamyah da Yah Amee ba da sanin shi ba, ba da sanin matar shi ba, sannan ba da sanin Amarya Lamyah ba. Sai dai nace Allah ya bada zaman lfy kuma a wanye qalaou. Kwalliya ta ci ta kece raini, ta fito dakin ta zuwa kan dinning, inda Lamyah ta fito itama cikin qamshi da hasken fuska, dan ko mai bata shafa ba sakamakon yunwar dake addbar ta da kyar tai wanka, tai brush ta fito daga ita sai riga da wando iya kwaurin ta, gashinnan ta daure ta baya, yana lilo,sai agogo dake hannun ta, zama tai taja kujera,sannan ta fara zubawa kan ta abinci,ko kula da Naufaliyya batai ba, amma ita tin bude qofar ta ta qurawa hips da boobs din Lamyah ido, sannan ta. Kalli yanda cikn ta yake a shafe, kamar zai hade da baya, sai ogon gashinta da fuskar ta mai cike da kyau da kwarjini, kai lomar farko da Lamyah zatai tana daga ido sukai ido biyu, saurin kauda kaiNaufaliyya tai, amma dole ba yanda zatai Lamyah ta kama ta, yamutsa fuska tai, ta kalli Lamyah tace," ke a garin ku haka ake in aka tashi a bacci, baki san ki gaida manyan ki na?" Wani kallo Lamyah ta bita da shi, dan tabbas Naufaliyya zata girme ta, amma ba zai wuce da 'yan shekaru biyu uku ba, a ganin ta su kuma ba komai bane, dan ko Farha ta bata daya da kadan, " a garin mu ba a koya mana gaida wadan da zasu zauna si qurawa wani ido ba har wanij ya dinga zaton ko ba kowa a wajen ba, har sai ya tsargu daga kallon maitar da aka bi shi da shi," miqewa Naifaliyyah tai," ke har ni zaki kalla ki cewa mayya, nawa kk? Wacece ke a gidannan? Waya tsaya maki da zaki kallen matar da a cikin gidannan ki zagen," da sauri ta cire hannu za ta kaiwa Lamyah mari, Lamyah riqe hannun tai tace," ko da wasa, ko da mantuwa, hannun ki ya taban jiki, da sunan duka bada niyyar tausa ba ko wani abu makamancin haka zaki sha mamaki, dan ni ba komai nake dauka ba, ina da son mutane amma daga lokacin da idona yai arba da naki naji bana yin ki sammm, dan haka ki kiyaye" jan kujerar baya tai ta wuce cikn takun isa da qasaita na macen da take taqama komai yaji a jikin ta, daki ta koma, abincin da bata ci ba kenan, yunwar ma sai taji babu, ita ko uwar gida an barta baki sake kamar qawuya, Lamyah bayan ta koma daki, ta sake nunfashin da take riqewa mai qarfi, " Dama na iya fada? Dama zan iya rama abu in an min? Ko dai tsabar kishi ne kawai ya ja hakan? Don hae ga Allah ni tinda na ga wanda nake wa son da ban san sanda ya shigen ba da wata naji gaba daya na tsane ta," juya kai tai ta kwanta a hannun dama, hawaye ne masu zafu ke bin kuncin ta, kaiii jama'a yau ina zata saka kanta? Komai sai tayi kamar zata same shi sai ya kufce mata. A wannan yanayi kullum Lamyah da Naufaliyyah suke, har Naufaliyyah ta gaji, ta ce zata koma gidan ta, su momma basu hana ta ba, ta tarkata ta koma, Lamyah kam zuciyar ta kamar ta fashe, dan gani take ta koma suna tare da Handsome din ta, " Handsome dina? " wata dariya tai ta gefen baki, dan ganin wautar kan ta da kan ta, a haka dai lokaci na ta ja har Ameenullah ya dawo, inda nan gidan su ya fara sauka, ya isko Momma bata nan da Baaba, Lamyah ce kawai a gidan.......... *Readers ga ango ga amarya fa*😱 [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *This page is for u Aunty Rumaisa, thank u so much for everything, I heart u da yawa, kin cancanci yabo mai yawa, kina matuqar taimaka min da an tambayi novel kina kusa an samu. Love u XX❤ Page 20: HAUSA NOVELS SOKOTO WHATSAPP NO: 07068808039 ABDULMKIBAB.HEXAT.COM Waqa ce ta Arabs kawai ke tashi, mai cike da matuqar dadi, ga duk mai sauraro, gaba daya ta cika parlon da kidan ta mai ratsa zuciyar masoya waqe2, ko Ameenullah da bai cika son waqe2 ba yau ya yaba wannan, ruwan da ta dakko daga fridge a kitchen ta ruqo tana qoqarin budewa, at d same time tana rawa, qugunnan kamar ba a jikin ta yake ba dan juyin da take da shi, ga rigar ta dake dagawa, sai dogon wandon da ta saka wanda ya matuqar matse mata qugun, ga gashin ta dake baje a bayan ta, amma tana rawar tana jujjuya shi, sake baki yai kamar dolo, qoqarin zama yake a kujera ashe bai ida qarasawa daidai wajen zaman ba, qarar faduwar Ameenullah ne ya firgita ta, ta kula da shigowar mutum, ihu ta kwalla, ta sake ruwan, nan take ruwan ya zube, shi kuma ya tashi yana wani basarwa, kar ta raina shi, gudu zata sa ta fada cikin ruwan, aiko ta bare baki ta fara kuka, da sauri ya isa gare ta, dan taimaka mata, ashe ma matsoraciya ce, ya ayyana a ranshi, wani murmushi ya sake, daga ta yai, tana ta faman kuka," ke ki wa mutane shiru, kin kunna kida kamar kina gidan RAWAR taku, ko an gaya maki gidan mu gidan RAWA ne?" " sadda kai tai qasa dan gaba daya yanzu wani nauyin shi take ji, bata kuma san meye dalili ba, sannan kullum hasashen ta na qara tabbatar mata wannan shine Yah Amee din ta, amma yau ta yanke shawarar tambayar shi ko shine Yah Amee din ta? Bata kula shi ba dingisawa tai zata kujera ta zauna, haba wani qara ta sake, saboda azabar da qafarta taji ta mata, dafe gini tai tana hawaye, sosai ya tausaya mata amma ai ita ta jawa kan ta, kama hannun ta yai yana bata rai, wani irin lantarki take jin na bin jijiyoyin ta, shi kuma ji yake kamar da dai duniya bai taba jin hannu ko jiki mai dadin tabawa irin na Lamyah ba, tinanin shi ya kawar, can qasan zuciyar shi na ci gaba da tuhumar wace ita? Dan in da wata mai mahimmanci ce a rayuwar shi da iyayen shi sun sanar da shi wacece, amma zai jira ya.ga zasu mai bayanin wanan mara kamun kan?zaunar da ita yai zai fice a gidan dan kula da yai ba kowa, ga Naufaliyyah da ta dame shi da kira, dada kama hannun shi tai ido na kwalla sosai, ta daga manyan idon ta dake zubda hawaye tace," Yah Amee?" Muryar ta cike da rawa, a gigice ya juyo, yana kare mata kallo, yanayin yanda yake kallon ta ne yasa ta tabbatar wannan shine Yah Amee din ta, hawayen ta qaruwa sukai kamar panpo aka bude, shi kuma jikin shi har rawa yake ," Lamya" amsawa tai kuma a lokaci daya ta miqe ta fada qirjin shi da gudu,rungume ta yai sosai suna kuka, Ammii n su da Abii suke tinawa sosai, kamar wadan da a kaiwa mutuwa a lokacin , sallamar Momma da Baaba ne ya katse su, da gudu Mubarak ya je gare su ya kama qugu yana kallon Ameenullah , irin kallon ina jiran qarin bayani akan abinda ka mata, da Ameenullah ya gane nan take ya daga hannu sama da nufin kare kan shi," ba abinda na mata," amma Mubarak bai dai na kallon shi ba, sai ma daga gira daya da yai ya gyara tsayuwa," na rantse ban mata komai ba, rawa take ta dakko ruwa ta fadi, shine na taimaka na kawo ta nan, zan tafi ta riqen hannu ta kira suna na a nan na gane Lamyah ta ce shine ta rungume ni muke kuka, kuma ita ta fara riqen hannu, ta rungume ni, wait a minute, why am i even explaining my self to a kid?" "Whatch it man i am not a kid,nan gaba kadan zan iya zama Yayan ta, haka Uncle Bala da Farha sister suka ce,"Baaba da Momma da suka dade da fara dariya, tun Ameenullah na zuba bayani ne suka fashe da dariya sosai, Lamyah kuwa ba abinda take face kallon Amee din ta, shi kuma yana tinanin me ya hana iyayen shi sanar da shi ita ce? Amsa aka bashi," Saboda ina son na aura maka ita kamar yanda na maka alkawari, amma ganin yanda kuka nuna kun san juna, kuma na san halin ka, tinda na ga inda ita da Farha suke RAWA, dan kan na dawo sai da na bincika komai, kuma an tabbatar man da irin tsanar da kk wa halayen ta, wannan dalili me yasa aka daura auren ku, ba da sanin ku ba," wata zabura sukai, Lamyah yar qara ta saki saka makon fama in da ta bige dazu da tai, kallon ta Ameenullah yai da sauri, zuciyar shi bai san me take qunshe da shi ba, farin ciki ko disappointment ne? Dan gaba daya a yanzu ya rasa wa yake so ma, shin Lamyahn shi ko Laila YAR RAWA? ya zai yi , wannan dake gaban shi gaba daya baya son halayen ta, dan gani yake kamar ta gama biyewa mazan dake wajen rawar tasu, sannan kuma yana son ta a qasan ran shi, dan itace mace ta farko da ya fara jin komai akan ta, ha kuma natural son da yakewa Lamyahn shi, kai everything is complicating. A nata bangaren kuw, banda mamakin wannan aure da aka hada ba abinda take, tabbas Yah Amee ne burin zuciyar ta, shi take son kasancewa da shi, in da so samu ne ma, yau ace an hada su su tafi gidan su tare, amma inaaa son da take mai ba zata iya zama da shi da kishiya ba, ace su biyu suke morar shi, musamman in ta tina wace a matsayin mayat shi, wani kuka ta sake mai cin rai, ta hau dingisawa tai dakin ta, gaba daya tana tafe albarkatun jikin ta na motsawa, ko dan wannan jiki Ameenullah zai yarda da auren ta, amma tabbas bai san ranar da zai daidaita zuciyar shi akan ta ba. Bayan ta tafi ne suka qarasa tattauna komai da Baaba, sannan suka saka lokacin biki da tarewa, nan da sati biyu, sallama ya musu ya tafi gida cike da tinanin da ya rasa ina zai saka su, yau duk maitar Naufaliyyah bata gane komai daga wajen shi ba, a haka ta hakura ta barshi, dan ta kula yau ba a daidai yake ba, gashi ita ko dan tarairayar nan bata iya ba, abinci wannan siyowa tai ta aje mai acikin abin take away din ko ta dan mayar wani wajen duk da yasan ba ita tai ba, dan bata iya din ba. Tana shiga daki wayar ta ta ratumo ta hai kiran Farha,Farha ana can ana zubawa Bala shagwaba , taji waya na ringing, miqa hannu yai ya dakko mata ya amsa ya kara mata,da kyar ta amsa da " Hello" " ke dalla tashi zaune Lamyah ce," ai da hanzari ta miqe har tana kusa kifawa dan murna, tsalle ta daka ta dale Bala, suna fuskantar juna, saka wayar tai a Handsfree, aiko Lamyah ta fashe da kuka, nan da nan jikin Farha ya hau tsuma kamar mazari," wane dan kan uban ne ya taba ki a gidan, kaf din su ki min bayani, bana tsoron ko wanne gauta a cikin su, ni rana ce dafa su zan, maza ki min bayani," Lamyah na jin haka ta tsagaita da kukan," Dalla uwae mafadata ni ba abin da kowa ya min," " to me kk wa kuka?" " Baaba ne ya... ya.... auran Yah Amee, "wata shewa Farha tai tana ta murza Bala, gaba daya Allah 2 yake ta aje wayar ," to in banda ke meye na kukan,bayan mafarki ne ya zama gaskiya," "a da ba? Yanzu yanda nake ji a zuciyata ba zan iya zama da shi ba" " baki da hankali ne, me yasa ba zaki iya zama da shi ba?" " yana da wata matar fa," kuka ta fashe da shi, ta hadiyi wani abu mai daci a wuyan ta, Farha ce ta sake wani ashar, " aure fa" daga Bala tai ta koma gefen shi,"wane qaton ne ya mai aure bayan an san ko ba jima ko ba dade zaki bayyaa agare su, to bari kiji kar ki yarda ki zaina da kishiya, ko ya sake ta ko a raba maku gida, ko kuma ya san abin yi, yo ni mutum ya min kishiya ma ba sai na babballa shi ba," ta qarasa tana huci sosai, wayar Bala ya amshe yana gimste dariya, gaisawa sukai da Lamyah sannan ya fara mata nasiha mai ratsa jiki da jijiya, nan take Farha da ta cika tai fam ta sauka," but still is not fair, yaushe ma Lamyahn tai girman zama da kishiya," daga qarshe suka mata addu'a suka mata fatan alkairi, da alqawarin zuwa bikin nata, kashewa tai ta zame ta kwanta, hankalin ta gaba daya a tashe yake, sai dai kawai a kaso dari t samu sauqin ashirin. Gyara ta sosai Momma ta fara,ba qaqqautawa, sai dai komai zata bata tana amfani ne da abubuwan mu na gida, kama da ga kayan lambu zuwa kayan marmari, sai kuma dangin aya, dabino, kwakwa, cukui, da zuma, ko gyaran jiki da natural abubuwa Momma ke wa Lamyah amfani, nan da nan ko kyaun ta ya qara fitowa, jikin ta tsabar kyau wani sheqi yake kamar macijiya, gaba daya Momma kanta ta san dan ta ya gama dacen mace anan. Tin saura kwana uku Farha ta dira a Nijer, sun sha murna sosai ita da Lamyah da Mubarak, sai kace zasu tsaga gidan da murna, dangin Momma sun fara zuwa suma, kowa sai son barka yake da amarya Lamyah, a gefe kuwa amarya zuciyar ta cunkushe take, duk yanda farha ta so mantar da ita baqin cikin ta abun ya faskara, tayi iya yin ta har saida itama ta koma yin shiru, Mubarak ne ya shiga tsakiyar su ya zagayo da hannun shi ta wuyan su" kaiiii shirun nan naku ya burge ni, for the first time Kumburin buredi, da Qashi da rai sun nustu ba fada, ba hira ba hayaniya," ido suka hada a tare sukai kwafa, ai ko kan ya ankara sunyi ram da shi, ihu yake yana neman taimako, dakin rufe yake, sai da suka gama yamutse gadoj kamar wasu yara, sannan suka kwanta suna ta dariya suna maida nunfashi," God i am gonna miss all this," hawaye ne ya gangaro ma Lamyah, Munarak ne yace," My goodnee really, Lamyah? To ba dani ba ni na gudu wajen Mommana, ta hadan abinci duk kun yashen ciki," fita yai a guje , su kuma suka saka dariya, Farha ce tace," yaron nan in yana abu kamar wani babba, he is just 5 to 6 yanzu fa, amma maganganun shi da wayon shi kamar dan 8 ko 9, Allah ya raya shi, tabbas ta bakin nashi ne tin da da yakan ce zai zama yayan ki,in Bala na kitsa mai hakan nakan musa kullum," murmushi sukai suka miqe zuwa sallah. An ci an sha, an kuma yi biki lfy, in da Farha taso tai rawa amma aka hana ta, taji haushi sosai, tai qunqunin ta ta gama tace aiko yau ko a gidan amarya ne sai ta dance, ile ko bayan an kai amarya, mutane an tattafi, daga Lamyah dake ta kuka, sai ita Farha, sai wata yar uwar su Momma, da ta kan zo, mai suna Rahama, kida Farha ta kunna, tin Lamyah na daurewa ai sai ga amarya ta cire mayafi tana takawa, suna yu suna ihun jin dadi, a haka Ameenullah ya dawo, shi daya ya shigo, dan a nan su Farha zasu kwan, ita gobe zata wuce, shiyasa Lamyah ta dinga kuka sai abar mata ita, da kyar Momma ta yarda, dan gaba dayan su kuka suka sata gaba suna yi, Ramla ma gobe zata koma gidan Momma, leqowa yai ta yar hanyar da basu rufe ba,yana ta qarewa Lamyah kallo, gaba daya hankalin shi ya ma tashi, burin shi kawai ya gan shi kusa da amaryar shi..... *Sauran qiris wayar nan ta ja na aje rubuta 'yan rawa sai bayan kwana biyu ko uku, inna huce daga faduwar gaban da ta ja min, nai rubutu mai yawa na fice hankalina ya tashi dana tina ban saving ba, ina komawa naga ashe bai gogu ba, da wallah sai na warke na dawo*😭😂😂😂 [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *I dedicated this sweet page to all MAMU NOVELLA members, especially the active 1s, Yan labe layi daya ne naku*😙 *I heart u da yawa, mun zama sisters from another mother, Allah ya qara mana hadin kai da so da qaunar juna, My qawalliya rabin duwais ( Mamu Autar Hajiya) Maryam Alqali,ina roqon Allah daya baki ladan hada zumunci da kikai mai qarfi* Page 21: Wani juyi Lamyah tai hade da banqara qirjin ta, sannan at the same time qugun ta ta maida shi gefe, ta saka hannu ta tattaro gashin ta gefe, tana kada qugun ta a hakan, wata ajiyar zuciya mai qarfi ya aje, bai san da zuwan Naufaliyyah ba sai ji yai ta daki kafadar shi da dan qarfi, a firgice ya juyo, wani mugun kallo ta ke bin shi da shi, gaba daya idon ta yai jawur, fuskar nan tai jawur, haka ma hancin ta, sunkuyar da kai Ameenullah yai yace," shigowa ta kenan zan miqa masu wannan naga suna shashanci, ni kuma bana son shiga," harar shi tai dan a tsaye take tin shigowar shi, har matse qafafun shi da yake da komai a idon ta, qwace ledar hannun shi tai ta dauki hanyar dakin, zata kai masu, tinawa da yai ba Lamyah kadai bace a dakin, da qawar ta masifaffiyar nan, sannan ga Rahma kar ta fadawa Momma , bayan nan ba zai so wulaqanta Lamyah har haka ba ace a first nyt din ka kishiya ce zata kawo ma kazar amarci ba kuma da arziqi zata ba da fada zata je, shan gaban ta yai ya jawo ta jikin shi, sannan ya hade ta da gini, nan da nan jikin ta ya hau rawa, miqa mai jikin ta take gaba daya tana aje nunfashi, yana ganin haka a ranshi yace," yau na shiga uku," kiss daya ya mata a goshi, ya shafi gefen fuskar ta, sannan ya kauce, idon ta arufe yake amma jin da tai kamar baya nan ya sa ta bude ido, aiko nan take wasu hawaye masu dumi suka fara bin fuskar ta, ta durqusa a wajen tana kuka, mai cin rai, yau Ameenullah din ta ya zama na wata, yau da wata zai kwana ba da ita ba, a qa'ida ko bai kwana da wata ba lokacin waccan ne ba zai kwan da ita ba, aiko yau za a yi ta, dan maganin matan da ta dirkawa kan ta, ba qaramun damun ta yake ba, miqewa tai tai dakin ta, wasu arnan kayan bacci ta saka, ta feshe jikin ta da mayun turarikan ta,wanda a ciki harda hadin na asirin su na mallake Ameenullah, murmushi tai na gefen baki, sannan ta tura qofar dakin Ameenullah dan ta kai mai ziyarar ba zata, me zata gani..... .. Wucewar Ameenullah, dakin Lamyah ya fada da sauri ya rufe qofar, kamar wanda aka kora ciki, ajiyat zuciya ya sauke kan ya daidaita kan shi, Lamyah da farha masu rawa tare da Rahma yar kallo ba qaramin firgita sukai ba dan ganin yanda ya fado kamar an biyo shi," wayoo Allah kai da waye?" Farha ce ta watsa mai wannan tambayar ta maqale a qarshen gado tana wulla idanu, Lamyah kam har ta fara kuka, sai Ramla data kasa magana jiki na karkarwa, bata rai yai ya harari Farha da take jiran amsa yace," Nida aljani ne," aiko a tare suka zunduma ihu, kowa ta qara qanqame yar uwar ta, dan tabbas da gaske yanda ya fadi akwai abinda ya biyo shi, dariya ce ta kwace mai bai shirya ba, " dalla malamai ku nutsu, wannan uwar Rawar da kuka me ai ta isa kira maku aljanun ba sai na zo da su ba, ke gaki jiki ba nama, a bushe amma kin dage wai ke rawa kk, to gwanda ma ita, tana da abun girgizawar, ba ma wannan ba Lamyah ki zo dakina ina son magana dake," idon Farha ne ya qanqance da masifa, ta miqe kenan tana tattaro kalamai da maganganun wassafa mai ta ga ya kama hannun Lamyah sun fice," Bashi, sai kuma ka biya," shine abinda Farha ta fada kenan ta sakko daga gadon tana ta mitat tsoron daya basu. ...........suna shiga dakin, auran ledojin ya aje a qasa dan dama uku ne ya aje ma su Farha daya ya zo da sauran nan, daya ta Naufaliyyah, daya ta Lamyah da shi, yana ajewa kuwa ya juya kan Lamyah data takure, a gefe tana watsa ido a dakin, kallon ta yai kamar ace fir ta gudu, ," sai kace wata ta Allah, dalla malama ki qaraso , ni magana nake son muyi dake," qarasa wa tai kanta a qasa, tana wasa da yatsan ta,duqar da kan da tai ne ya bata damar ganin kayan jikin ta, aiko wata kunyar shi ce ta kamata, dan laffaya aka nadota da shi, kayan qasan wasu fitinannun kaya ne irin yadin nan me mannewa a jiki, sannan doguwar riga ce iya cinya amma an tsaga ta ta gefe, sannan an matse ta daga sama, bata taba jin kunyar zama da irin kayan nan ba sai yau, Ameenullah kuwa duk inda hankalin shi ya ke ya kai qololuwae tashi, amma daurewa yake kar ya ja musu masifar Naufaliyyah, zama tai a darare, ya daka mata tsawa," ni dalla ki matso ko magana kk son nai ta daga mury ne?" Kada kai tai alamar A'a, matsawa tai sosai, shi ma qara matsawa yai jikin ta sosai, ledar hannun shi ya dakko, ya bude, kaji ne manya, masu laushi, guda biyu, sai drinks, da snaks, janyo dan qaramin table din gefe yai,ya dora su, umartar ta yai da su ci ta tashi ta bace mai a daki, ci ta farayi, dan ko tana jin yunwa, after all Yah Amee din ta ne, bata ga abin jin kunya ba, zagewa tai ta ci sosai ta sha abin sh, suna gamawa tai qoqarin miqewa, juyawar da tai, yai ido biyu da shape dinta nan take ya kware ya hau tari, ba qaqqautawa, da sauri ta juya nan ma ji yai kamar an qara kware shi, dan yanda ta sunkuyo qirjin ta ya bayyana mai jiyai kamar nunfahin shi zai dauke, jus ta zuba a cup ta zauna daf da shi,jikin ta na gogar nashi,ta kai mai baki, tana ta faman zuba mai sannu, idon ta fal hawaye, kurba yai, a hankali nutsuwar shi ta dawo, jan ta yai ya aje cup din hannun ta ya hau kissing din ta ba ji ba gani, suna a hakan ne Naufaliyyah ta shigo, kusan suma tai dan tsabar kishi, ai ko yaja jin qamshin ta bai san sanda ya ture Lamyah ba ta koma gefe, wani kallon mamaki ta bishi da shi, sannan ta bi inda yake kallo itama ta ga meke faruwa? Naufaliyya ce ta cika tai fammm, idon ta har qanqancewa yake dan masifa, " Lamyah sai da safe, ki addu'a kan ki kwanta," wani kallo ta bishi da shi na lallai ka rainan wayo, duk da ba tsoron first nyt da take ji tabbas she really want to experience it at her own first day, in her matrimonial home, amma da dikkan alamu wannaj matar tashi bazata taba bari su sake ba,duk da soj da suke wa junan su, tabb ashe akwai yaqi gaban ta," bakiji ance ki fitsari ki addu'a ba kan ki kwanta,yara qanana sai jarabar tsiya," inji uwar gida amanar Ameenullah, wani mugun kallo Lamyah ta bita da shi,tana son bata amsa taji an kama hannun ta ana leading din ta waje, juyawa tai taga Yah Amee din ta ne, suna kaiwa qofa yace mata a hankali,"My Lamyah sai da safe sleep well, and i love u so much," daskarewa tai a tsaye, yau me take ji, itace fa amrya, sannan kuma ita bata taba tsammanin zai hakura da kasancewar ta YAR RAWA ya aminta da ita da wuri haka ba, amma gashi har kalmar love ya furta mata, wani murmushi ne ya kwace mata,haushin da ta qunsa gaba daya sai taji nafila ne, tin da an bata farilla ai shikenan, ita kuma waccan jarababbiyar taje ta cinye shi, dama ita bata san komai ba ai, hanyar dakin ta tai ta isko mutanen ta na ta hira,Ramla na jin bacci amma iya surutu ta hana ta sai zuba take, kashe fitila tai ta qarasa gadoj ta haye, a hankali ta furta masu," sai da safe, a hakura da hirar nan haka Farha," haushi ne ya kama Farha sannan kuma taji wani iri game da yanayin Lamyahn," me ya miki? Ki sanar dani in wani abu mara dadi ya miki tin kan na tafi na mai tass dan ba wai mun baki shi bane dan ya na bata ranki," " cikin dan murmushi mai sauti Lamyah tace," Ammiii kwantar da hankalin ki, ba abinda ya min, kin hane?" Farha ce ta kada ido sama tace," au nice ma Ammii din yau," " to u ar being over protective,ba fa abinda ya min, da yamin wani abu kin san halina da kuka zaki ganni," ta qarasa cike da dariya, Farha ce tace " kuma fa haka ne," gyara kwanciyar ta tai,ta dan dago kai zata fara zubar ta ta, taji sun hai munsharin qarya,dan ta san Lamyah bama ta munshari ko baccin gaske balle tasan wannan shirun dan tai tsit akayi shi," Fine kui baccin , ai dai gobe zan ma tafi," Lamyah najin haka idon ta ya ciko da kwalla, tai canjen waje da Rahama ta koma kusa da Farha ta kwanta, kamar jaririya,a hankali kuwa Farha ke shafa kan ta har tai bacci, bayan addu'a da suka hada baki sukai a tare, kamar yanda suka saba a gida, cikin sha'awar yanda sike gudanar da rayuwar su kamar 'yan uwan juna ne Ramla itama tai bacci. Ameenullah, ranar ya ga ta kanshi, ba qaramn wahala Naufaliyyah ta bashi ba, dan ya sanar da ita ba ranar ta bace amma ta qi sam, sai da ta san yanda tai ta daha mai hankali ya kusance ta, qarin abinda ya bashi qarfin guiwa kuwa ganin Lamyah da yai duk dama hankalin shi tashe yake, sai dai dama yasan kawai zai rage zafi da wannan ne , amma qishirwar shi kam mai kashe ta sai Lamyah, da kyar ta hakura ta kyale shi, dan sai da taji gaba daya ya sake baya iya komai again ta barshi,amma still ta manne da jikin shi kamar wadda take tsoron kar ya fita cikin dare, murmushi kawai yai ya kada kai, halin Naufalliyyan shi sai ita. Kukan rabuwa da Farha Lamyah take kamar ba zasu qara haduwa ba ki kuma ba waya, tin Ameenullah na lallashi, yanda ya ji jikin ta ya dau zafi da alamar zazzab zai kamata,ya sa ya daka mata tsawa, tai tsit, amma idon ta sai hawaye yake,Farha ma kukan take sosai," Malami ka daina firgitan ita,haka xan tafu na bar ma ita baka san meye lallashi ba?" Ta fyace majina tana kare mai kallo, dariya yake son yi dan shi yarinyar dariya take bashi, kamar wata uwar ta, dan dai da gani ba wani girman Lamyah tai sosai ba, amma yanda take mata kamar ita ta haife ta, harara ya watsa mata yace "in zaki wuce ki wuce ni dalla kn sa yarinya zazzabi na neman kama ta," cikin kidima ta taho zata taba jikin Lamyah taji, dan ya bata haushi ya ja Lamyah suka shige gidan suka bar ta nan, dariya kamar ta shaqe shi, suna shiga Lamyah ko ta fashe da kuka, a idon shi da yanda yake jiyo muryar farha kuwa yasan tana can tana masifa, kawai sai ya kwashe da dariya, jan yo Lamyah yai jikin shi yana lallashi,da kyar tai shiru, sai ajiyar zuciya ta ke, waya ya dauka yaji waccan aunty masifar sun isa gidan Momman ne? An sanar da shi sun isa, fadawa Momma yai da a bata dubu dari, dan bai samu sikai rabuwar arziqi ba, sannan a mata godiya sosai, dan tana burge shi, amma yana son kwasar ta yaga tana masifar nan kamar wata uwar mata, bayan ya kashe wayar ne yaga Lamyah na murmushi, anan ya gane ita kamar Ammiin su take, qaramin kindness na faranta ranta, shima murmushin yai, suna haka sukaga Naufaliyya ta fado parlon a hargitse, kanta buyaya, rigar hannu daya a sake tana qoqarin saka dayan, daga ita sai pant, tana muzurai, idon ta na sauka kan Ameenullah ta saki ajiyar zuciya, dan bata san fitar shi ba, takawa tai zata wajen shi da sauri ya miqe yai hanyar daki, dan kome za ai baya son yana bata ma Lamyah rai, kuma ya san halin Naufaliyyah burin ta kenan, bayan haka bai isa zama ba ta qaraso, yanzu ta tashi bacci, ko brush ba tai ba,kuna yasa da tazo zata kai mai fuska tace zatai magana, shikk baya son ya yaba ta gaban kishiya, shiyasa ya miqe, Lamyah kam ranta yana suya ta barwajen , daki taje ta sha kukan ta, sannan ta fita zuwa kitchen.......... . [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH My Sophy (Mrs J Moon) this page is for u dear, missing u da yawa, Allah ya dawo mana da ke lfy, HAERMEEN HAERMMAERH NA GAIDA KI❤ Page 22: Yau sati biyu cip da auren Lamyah da Ameenullah, duk wata hanya da zata hada Ameenullah da Lamyah Naufaliyyah ta ci nasara wajen katange ta, sai akai sa'a ta samu nasarar hakan ne da taimakom Lamyahn da kanta, ba dan komai ba sai ita Lamyah tana matuqar jin haushin yanda ace kamar Ameenullah ya kasa isa da iko a gidan shi, duk yanda ta so da ganin shi haka ta dau matakin zaman cikin dakin ta, wanda gaba daya Naufaliyya ta hana Ameenullah kusantar qofar dakin ta ma, tayi nasara da cikar asirin ta na bashi umarnin ko me Lamyah ke buqata zata iya isar mata ba sai ya je ba, a haka suke har wa yau, da Ameenullah ke zaune yake tinani, gaba daya kamannin shi ya sauya, gayun nan nashi sam ya ragu, ga wani qasumba daya tara,yai dan wuya, Naufaliyyah ta riqe wuta, ta mai da shi kamar ruwa ko da yaushe buqatar shi take, shi kuma a duk sanda ta buqace shi baya da zabin da ya wuce mata hidimar da take so, gashi gaba daya wata muguwar sha'awar Lamyah ke hana shi sakat, dan ya kasa goge image din surar ta a idon shi, wataran in ya zauna a parlo dan ta zo wucewa tana leqowa ta ganshi zata doka qofa ta wuce, yana cikin tsaka mai wuya, wasu siraran hawaye ya share, " My one, me kk yi a zaune anan,?" Saurin goge fuskar shi yai ya daga kai ya kalle ta, ta ci uban gayu, anyi makeup na hauka an cika fuska da tarkacen kwalliya, hadiye wani yawun takaicin ta yai, shi da zata bi tashi da gaba daya ta daina kwalliya kwata kwata bata kyau, maida kan shi yai gefen da ta zo ta zauna daf da shi, kusan cinyar ta da qirjin ta a jikin shi suke, " ba komai ke nake jira na san kina can kina min kwalliya," aiko tai wani farrr da ido, ji yai kamar ya kwada mata mari, amma ba hali, shi he wonder what his parent were thinking da suka aura masa wannan, bayan ko da ta nuna tana son shi bai ce yana yi ba, bai gama ida tinanin shi ba yaji ta akan cinyar shi,tana mai salon ta , gashi sam baya son kome zasui suyi a inda Lamyah zata iya gani ko jiyowa, ita ko yau babban abinda take buri kenan,dan tasan wannan lokacin ne na fitowar Lamyah hada abincin ta na dare ta koma, dan kar tai karo da Yah Amee din ta a parlor wajen kallo, ai ko Naufaliyya tayi nasara, dan a yanda take jin ta a hannu shi kuma yana da niyyar sauke abunda yake ji game da Lamyah akan ta, sun yi nisa sosai basu sanin me ke faruwa a duniyar sam, Lamyah ta fito riqe da waya a kunne, ta na waya da Mubarak da yake rigimar yana son zuwa wajen ta, hakuri take bashi akan za ta ma Momma ko Baaba magana a kawo mata shi, hankalin ta gaba daya na kan wayar, sai da ta kashe a lokacin har ta iso tsakiyar parlorn daf da kujerar da suke ta fara fahimtar me ake aikatawa a wajen, wani qara ta saki, ta dafe kan ta, hawaye na matuqar zuba mata, kukan ta ne da qarar ta ya dawo da Ameenullah hayyacin shi, ganin ta durqushe a wajen ne tana kuka ya daga hankalin shi, ita ko uwar gayyar abin nema ya samu, rigar ta ta mayar ta miqe tai daki tana dariya, daburcewa yai, yana neman kayan shi, a can nesa da su ya gan su ya zura, wajen ta ya nufo dan bata baki, amma wani mugun kallon da bai taba sanin Lamyah zata iya aikata shi ba ya samu, nan ya qame, ya kasa koda daga qafa daya ne, miqewa tai tana layi kamar ta shawu tai dakin ta,ta saka key, kuka ta kwanta a gado tana zabgawa, kamar wadda akaiwa mutuwa, "I hate u Yah Amee, I so much hate u, kamin abinda har abada ba zan manta da shi ba, kaine ka ke fadan irin son da kk min a matsayin qanwar ka, amma yau kaine kk aikata abin da in ka dauke ni qanwa kasan ina under roof daya da kai ba zaka aikata ba, balle ace ni matar ka ce, wadda iyayen mu suka zaba maka, ko baka sona a qalla yau satina biyu, ko da gaisuwa zaka na leqo ni muyi, amma bakayi ka tare a wajen matar ka, abar son ka, ka barni ko me zai samen ni na sani, da zan iya da yau na bar maka gidan ka, amma nai alqawarin ba abinda kowa zaiji daga gareni na zaman aure na, ruwan ka ne ka gyara ruwan ka ne ka ci gaba da cin amanata," kukan ta taci gaba da shi, qafafun shi da take hangowa ta ke maganganun, yanzu gani tai kamar zama yai a bakin qofar a hankali yake kuka da jin kalaman ta, tina sanda suke a tare da Ammiiin su da Abiii din su, lokacin da suke tsantsar son juna su, ko dan su Ammii bai kamata yai ma Lamyah haka ba, dukan qofar yai yana kiran sunan ta, miqewa tai tana harar qofar kamar yana ganin ta,tace," bari na bar maka wajen naje toilete in ka gana ka bar min wajen," ta cire yar rigar dake jikin ta ya rage daga ita sai pant dan dama ko bra bata saka ba, toilete ta shige ta hada ruwa mai zafi ta shige, kuka tai ta yi, ta sha wankan ta tai brush, ta fito, gyara gashin ta tai, ta saka wasu kayan riga da wando qarami wandon har ana hango ass din ta in ta sunkuya, kalar white da red, ta daurw kanta da red band, sai jan agogo data daura, sannan ta feshe jikin ta da tiraruka masu qamshi, ta dakko chocolate din ta na Diary milk ta bare ta dau wayar ta tana cin chocolate tana katsa waya, dan a yanzu ta gama cire Yah Amee a zuciyar ta, ta barwa matar shi, dama tare ta gansu,fita tai taci karo da mutum a qofar, tabbas ta san shine, amma ta sa qafa ta take mai yatsan hannu daya saka a qofar da takalmin ta mai tsinin gaske, ta wuce kitchen, binta yai da kallo, sannan ya miqe da sauri, yana yarfe hannun, " Lamyah ki saurare ni, ba da son raina komai yake faruwa ba, someti......." " kaga malam, in dai kana son na ci gaba da zama ba tare da kowa ya san halin da muke ciki ba to kar ka sake bin inda na bi, hanyar ka daban da kai da matar ka tawa ma daban, kowa ya ci tuwon gidan su ehe, in ko ba haka ba na rantse zan kira Farha na sanar da ita komai, nai imani da Allah matar nan taka sai ta ji a jikin ta, kaima ba ka tsira ba, sai ta gana da ku kuma na fada wa Mommana komai, dan haka sai ka zaba," bude baki zai yai magana ta mai kallon au baka ji ba kenan, sum2 ya fice a kitchen din amma ya tsaya a hanyar dakin su yaga wucewar ta, sannan yana leqen ta, tana sane da bai tafi ba tai wani murmushin mugunta, da gangan take sunkuyawa, dakko spoon din da take yarwa da kanta, sai ta baza mazaunan ta sosai ta bashi view din komai, sannan ta miqe cikin yanga , hankalin Ameenullah in yai dubu ya gama.tashi, wani hadiyar yawu yai mai qara, Naufaliyya ce ta fito cikin shiri, daidai nan Lamyah ta gama hada Tea din ta da yar Indomie dinta, tana fitowa cike da yanga, tana kada jiki,kamar ba abinda ya faru, wuce su tai ba ta tanka kowa ba. "Malam kallamu in ka gama kallon nata zan fita, Ummata na kira na akwai abinda zan karbo," a ranshi yana jinjina wannan rainin hankalin umarni ma take bashi ba neman izini ba, tinawa da abinda ya qudurta a ranshi ne yasa ya amince da sauri har yana ta bari ya dakko mata kudin da zata ba Umman ta in taje, aiko xike da tsantsan son kudi ba kunya ta koma tana mai lissafin gidajen da take son zuwa,kudi masu yawa ya qigo ya bata,yace ta dau duk lokacin ta,shi fita ma yake son yai, ranta kwal ta fice. Wanka yai ya sha gayu, yau harda shaving yai, nan da nan ya fito Ameenullah din shi,fuskar shi cike da nishadi, ga tirarika kamar anyi barin su a jikin shi, haka ya shafa mai ya fito, sake da jallabiyya kalar maroon, tai matuqar masa kyau, kai tsaye dakin Lamyah ya nufa, tana kwance tai daidai, bayan ta gama da abincin ta, ta qara chocolate, waqar Nancy Ajram take sauraro, tana kwance tana rawa da jikin ta, gaba daya ya tafi, ji tai an shafa cinyar ta da take a miqe, da sauri ta miqe tare da dan sake qara ," meye haka malam, meye na shigo min dakiiiii," jan maganar tai a lokacin da Ameenullah ya dago kan shi, wani irin kyau da kwarjini ne ya fito masa, kasa ci gaba da masifar tai, ta qura mai ido, idon shi taf hawaye,kuka yake sosai ya fara magana," qanwata kuma mata ta ki yafeni tabbas ni mai laifi ne a wajen ki, ke da ma wajen Allah, amma in kk yafen na san Allah zai gafarta min, nasan ba zaki so Allah yai fushi da yayan ki ba ko? Duk abinda kk ganin yana faruwa ba da so na bane, wani abun bana sanin ina aikatawa ma,ki duba lamarina ki yafen ba dan ni ba," wani tausayin shi je ya kamata, da gudu2 ta taho ta fada qirjin shi tana kuka, ," amma me yasa ba zaka fi qarfin ko meye ba? Ka na nuna ma matar ka banda mahimmanci a wajen ka, kasa kullum sai ta gayan magana," "shhhhh, bar kuka kae wani ciwon ya same ki, zan iyakar qoqarina na ga na miki duk abinda yake haqqin ki ne, inshaa Allah komai zai wuce, ke tawa ce, ni naki ne, iyayen mu sun san zuciyoyin mu daya ne tun sanda suka haife mu, shiyasa suka tsaya dan mallaka mana junan mu, dan haka ki qara hakuri, kinji qanwata?" Daga mai kai tai tana sauke ajiyar zuciya, sunsuna wuyan ta ya fara," wanne irin tirare kk amfani da shi ne?" Shiru tai tana jin wani baqon yanayi na ziyartar ta, a haka da wayo da komai Yah Amee ya cika ma Lamyah aiki, tai kuka sosai, kukan rashin 'yanci, dan ko yana tsaka da lallashin ta ya mata wanka, sun dawo dakin, ya gyara mata kwanciya yaji sallamar matar shi, haka ya miqe jiki na rawa yai sanda ya fice, yai kamar ba daga dakin Lamyah ya fita ba, kuka sosai Lamyah ke yi, yau ina zata saka kanta, wannan wacce irin rayuwa ce? Kenan wannan shegiyar matar tashi tana nufin haka zasu ci gaba da rayuwa da abin son ta? Inaaaa da sake an ba mai kaza kaiiii....... *Muje zuwa Qawayen Lamyah ku bata shawarwari, wataqila ta samu mafita* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *This page is for u my priceless sister from another mother,ASEEYAH AHMAD BUNZU,❤ i love u so much for being a very gud freind, i have to say thankx for the gud things i have learn from u, is good to have u in my life dear, and don't worry i think i will be in ur country some day just to see u and my kids*😎😉 LOVE U XOXO❤ Page 23: "Daga ina kk naga fuskar ka cike da annuri, kayi matuqar kyau," ta fada tana taku daidai zuwa gare shi, yana ganin tana nufo shi gaban shi ya yanke ya fadi," kai jama'a ni kenan ban da hutu, Allah gani gare ka barawo a hannun mata," gudun karya amsa ta da qarya ne yasa shi manna mata kiss a lips din ta yana shafa bayan ta, tare da tambayar ta akan inda ta ziyarta, a haka ya shashantar da ita, qarasawa sukai gado ya tayata cire mata kayan jikin ta ,jakar ta ya dauka zai aje mata a wajen jakunkunan ta, da gudu ta amshe ta hau ce mai," da ka barta ma zan aje da kaina," mamakin canjawar ta yai lokaci daya, meke damun ta, oho ita ta sani, miqewa yai ya nufi waje ya zauna a parlor dan yana son in ta shiga toilete ya fada dakin Lamyah, haka ko akai, yana jin ta shiga, da sauri har yana tuntube da carpet ya fada dakin, kwance ya gan ta, tana ta kuka, ta duqunqune guri daya, qarasawa yai da sauri, ya jawo ta jikin shi, wani irin tura shi tai sai da ya kusan kaiwa qasa, jikin daga murya da tsananin fushi ta nuna mai qofa," get out!!!" He don't want her to repeat what she just said,haka ya ja yan qafafun shi ya fice, tabbas yasan abinda yai bai kyauta ba, amma ya zai yi? Bai an kara ba yaji ta daka mai tsawa," daga gidan uwar wa kk?" Ranta a matuqar bace, dan taji sanda Lamyah ta daka mai tsawa, kuma gashi rai bace, Allah yasa ba wani abu yake.nema wajen waccan mai kama da aljanun ba? Tabbb da ta shiga uku, qara daure fuska tai tana tuhumar shi, akan daga ina yake, cikin in inaa yake fada mata Lamyah ce ba lfy yaje ya duba ta shine take jin haushi dan da baya kula ta sai yanzu, ajiyar zuciya tai tace," kar ka damu mine, let me help her," cikin rangwada tai dakin Lamyah, kwance ta gan ta tana kuka, dariya ta saki tace," Lamyah kk ko wa? Bari na fada maki, kinyi babban kuskuren auran mijina, domin mijina nawa ne ni daya, ba a haife shi dan wata ba kina jina da kyau, dan haka tin kina iya gane hanyar gidan ku ki tafi kice kin fasa auren kan auren ya gagare ki," Lamyah bata tanka ta ba tana kwance , da taga ba zata amsa ta ba ne ranta yai mummunan baci, dan ta tsani tai magana ai shiru, tsaki tai ta fita ta doka qofar da qarfi,Lamyah ce ta dan daga ta ga wucewar ta, girgiza kai tai tace," lokacina na nan zuwa ki gama naki, dan lokaci na baki, ki gyara zaman ki da ni, ko na dauke duk abinda na san mallaki na ne dama," juyi tai, daidai nan taji ana kiran sallah, miqewa tai da qyar cinyoyin ta ciwo suke sosai, ga tsami da jikin ta ke yi ko ta ina, ruwan zafi ta dada hadawa mai tsafi ta shiga ta qara gasa jikin ta, tai alwala tai sallah, sannan ta shafe jikin ta da kayan shafa masu kyau da qamshi, ga turarukan ta masu tsada da qamshi, gyara gashin ta tai, ta saka yar doguwar riga, amrless, ta daura dankwali, ta jawo wayar ta, inda qur'an yake nan ta kunna, ta hau karatun ta, a haka akai kiran isha'i, sallah tai, tai shafa'i da wutri, tai addu'o'in ta, dan ita da ta ga biyar na yamma tayi take azkar, miqewa tai ta cire doguwar rigar ta maida na bacci, kwantawa tai, dan yin bacci, nan take ko ya dauke ta, bacci tai sosai, sai wajen 1:13am ta tashi, yunwa take ji sosai, dubawa tai komai na ta na kwalama ya qare, tsaki ta danyi ta sauka zuwa kitchen, dan samawa kanta wani abun....... Kuka yake tayi shi a kaishi wajen Farha Sister, ko Mummyn shi, " haba Mubarak why ar u being such a baby? Nan in magana ka tashi zarowa, kamar Farha ce ta haife ka, amma yanzu as big as u ar kana kuka," kunya ce ta kama shi ya goge hawayen yana wani mammazewa, shi a dole babban yaro,dariya ce ta kama Momma da Baaba wanda ya dade tsaye yana kallon su, ice cream ya miqa mai, cikin murna yace, " Baaba na gode," ya je cinyar shi ya zauna, shafa kan shi yai yace mai," kar ka damu my boy jibi zan kai ka da kaina nima ina son zuwa naga mahallin diyata," " yippyyy Momma zaki kema," " zani mana in zaku kara ni a motar taku," " zamu dake, amma ina sona kaima Lamyah Sister best chocolate din ta, Baaba," ya qarasa cike da shagwaba, murmushi Baaba yai ya shafa kan shi, yace," kar ka damu Allah ya kaimu jibin, gobe sai muje mui shopping ko," daga kai yai cike da murn, ya sauka yai dakin shi da gudu, wata takarda da biro ya dakko, yana ta rubuta me yake son saiwa Yayar shi. " Ni dai Baby na gaji, kullum amai ba qaqqautawa, tinda cikin nan baifi sati uku ba in kana sona ka neman sauqi a cire," Farha ce ta fada a galabaice, ko ina na jikin ta rawa yake saboda gaba daya ta wahala, sakamakon amai na laulayi da take fama, furicin ta ya daki zuciyar Bala, bata taba ganin bacin ran shi ba irin na ranar, bai kula ta ba, dan fushin da yake zuciyar shi komai zai furta ba zai zama alkairi ba, taimaka mata yai bayan ta gama ya maida ta daki ya gyara wajen, daga yanayin shi ta tsorata tasan tayi ba daidai ba, hankalin ta ya kuma tashi da hakan, nan da nan tai nadamar maganar ta," i am so sorry love, ban san magana ta zata harzuqa zuciyar ka haka ba" ta qarasa cikin kuka sosai, tausayin ta ne ya kama shi, dan ya san tabbas tana cikin matsananciyar wahalar laulayi, komai taci sai amai, ga zazzafam zazzabi, da ciwon mara, komai bata so, surutun tane kawai yake nan, sai abinda ya qaru,dan in abun ya motsa mata ta dinga zuba, sai ya lallaba ta tai bacci yake samun hutu. Bayan ya gama lallaba tane sun fara hira as usual tace," kaga Lamyah bata san da cikin nan ba fa, ko zamu bata mamaki ne, ko na sanar da ita kawai??" " duk yanda kika gani mata ta," ya fada tare da kissing goshin ta, bari tai a sai da safe zata sanar da ita. Tea ta fara hadawa idon ta kusan a rufe yake, bude fridge tai tadakko cake ta yanka, a plate, tazo zata fita, taji an kashe wutar sannan an amshe cup din da plate din........ *Who could that be?*😱😱😱😱😱 [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH page 24: Ihu zatai taji bakin ta cikin na mutum,mutsu2 take na kwace kan ta amma inaa qarfin su ba daya ba, a kitchen din ya samu biyan buqatar shi da ita, tin tana kuka har tai shiru sai a jiyar zuciya take, shi kanshi kukan yake, harda shessheqa, " babyna ki yafe min, ki yi hakuri da duk abinda na miki da wanda zan miki, ba zan yafe ma kaina ba alhalin ina cutar da ke, i wish i can change all this, na rasa ina zan kai sha'awar ki data damen ne yasa na kasa bacci, duk da kwana da nai da Naufaliyyah ke ta daban ce, dalilin fitowa ta kenan,na hango shigowar ki nan, dan Allah ki yafen, nasan in ba haka nai ba bazaki kula ni ba, ni kuma ba zan iya jure rashin ki ba, ki tausaya min ki na ban hadin kai plss," ya qarasa cikin matsanancin kuka,duk da haushin shi dake cin ta , zuciyar ta cike take da tausayin shi kuma, tabbas baya da iko da jikin shi tare da tinanin shi yanzu, ta sani Yah Amee din ta a yanzu ba zata iya bada shaida akan shi ba ta wajen ibada, dan a da duk a waya ta san komai da bakin mahaifan su, majina ta sha sannan ta goge idon ta, matsawa tai daga yanda ya raba mata qafa akan dinning table din dake cikin kitchen din, rigar ta ta dauka ta saka, wadda dama da ita da babu duk.daya, daukan Tea din ta da cake din ta tai, dan hasken parlor na reflecting wajen, kanta a qasa ta ce mai," sai da safe," mamaki ne ya cika shi, wannan na nufin he is always welcome kenan? Wani farin ciki ne ya mamaye shi, tana shiga daki ta aje komai ta fada gado tana kuka, kuka take mai cike da abubuwa kala2 tausayi, baqin ciki, takaici, a qasan zuciyar ta tana ayyana cewar tabbas ta haka ne zata qoqarta jawo mijin ta jikin ta dan tai maganin wannan shegiyar matar tashi,goge hawayen ta tai sakamakon wata yunwa data dada motsa mata, cake din ta ta ci tasha Tea, sannan ta cire rigar ta ta wuce toilete. Yana tsaye yana tinanin ko komawa zai ne? Wani gwarin guiwa yaji ya dau rigar shi ya mayar ya taka kamar wani barawo cikin sanda, zai shiga kenan ya kama hannun qofar yaji magana abayan shi, rintse ido yai da qarfi, da cije lebe," sannu na mamajo, duk abinda na maka dazu bai ishe ka ba sai kai sanda dakin wata ko,to wuce muje, dama nima bawai ya ishen bane dan kace kana son bacci ne na kyale ka," zaro ido yai amma bai juyo ba, kamar qaramin yaro hka ya buga qafa kamar zai kuka, " nifa kitchen naje na sha ruwa shine zan koma naga bata rufe qofa ba nazo zan rufemata," Lamyah da ta fito wanka duk tanajin su,gashin ta daya jiqe yakwanta ya mannu a sassan jikin ta tare dasauran ruwa dake jikin ta ne ya qara fito da kyaun ta, tana sane tasan ba kaya jikin ta ta leqo," meye ne ake damun mutane haka, gaba daya kun cika min kunne, ko ku koma dakin ko kui hirar, ko ku samu waje a gefe ku bar min nan," mutuwar tsaye sukai gaba dayan su, musamman Naufaliyyah, data kusan zaucewa, "wannan ce kishiya ta?" Tambayar da taiwa zuciyar ta kenan, "yeh of couse she is, who do u think she is to u then, a sister or what? "Hell nooo, i can't believe i am staying with this beuatiful creature in the same roof", yes u ar bich, and u have nothing to do about it, saboda ko jiya bokan ki ya fada maki hakan remember?" " Tabbas haka ne, na shiga uku, lallai sai na qara qaimi kenan akan Ameenullah," qarar buga qofar Lamyah ne ya dawo da su daga dogon tinanin su, a tsorace, wanda shi Ameenullah hankalin shi ba qaramin tashi yai ba, nan take ya fara hawaye, lallai ko me damun shi yake jin tsoron wannan matar ya hana shi kusantar wannan kayan alatu ba qaramin azzalumi bane, habaa, ace yana da mace kamar wannan yake rabe2, "kukan me kk?" Gogewa yai ya wuce ta bai ce komai ba, binshi tai , suna isa daki ko ta fada mai kamar wata karya, tin yana yi dan kauda sha'awar Lamyah a jikin ta har kwakwalwar shi ta bashi cewa, Lamyah fa daban take, ba mai maye gurbin ta wajen ka, dan haka ka sararawa kan ka ka samu hutu, kai ta addu'ar komawar ka aiki da wuri, dan sai nan da sati, a hankali ya nuna mata alamun shifa ya gaji, haushi ne ya kamata tace to kuwa sai dai yasan ya zai da ita ita bata gaji ba, kuka ta fara masa shima kukan ya sa mata,kallo ta bishi da shi, daga baya ta miqe ta dakko wani maganim maza a jakar ta, ta kiqa mai," karbi ka sha, yau sai dai ai wacce za ai,ko ka biyamin buqata ta ko kuma nace ban yace maka ba dan ina da hakkin wannan a wajen ka," daga kai yai ya kalle ta, gaba dya ya galabaita, ya rame, yai duhu, karba yai ya tashi yaje ya sha ya dawo, ba su jima ba ko ta maqale mai , sai wajen 4:37am ta saurara masa, tako bingire da bacci, kan shi tsananin ciwo yake mai, da kyar ya miqe yai toilete yana hada hanya, wanka yai,anata kiraye2n sallah, yana fitowa ya saka wasu kayan ya fita masjid,hamshaqiya mandiyar ko ta bude uban baki tana ta bacci harda munshari. Tin fitar su da Lamyah ta koma murmushin mugunta tai, dan ta tabbata duk ta dasa musu bomb a zuci, kaya ta saka ta hau nafilfili, ta hada da karanta qur'ani, dan tana ganin awa daya ne ya rage dama ta tashi ibadar dare,is of no use ta kwanta, a haka akai kiran sallah,tai sallah, ta dora da azkar din bayan kowacce sallah, sannan tai azkar din safe ta miqe, idon ta cike da bacci, amma sai da ta gyara dakin ta ta feshe shi da kayan qamshi tai wanka ta saka kayan ta da suka zame mata jiki, qanan kaya kenan, ta samu ta haye gadon ta, nan take bacci yai gaba da ita. Wayar ta ce ta tada ta wajen qarfe 12:20pm miqa hannu tai ta lalubo wayar, dannawa tai ta amsa cike da magagin bacci, ," Bacci kk? To sai ki tashi ko kuma bbyn ki yai kuka, dan so yake yaji muryar maman shi," waccakewa tai tace," ban gane ba? Me kk nufi da maganar ki?" " hhhhhhh ina nufin i am pregnant sweery," da tsananin murna ta miqe ta sakko ," dan Allah, kaiii masha Allahu la quwwata illah billah, wayyo dadi, Allah ya raya, ya inganta, Allah ya rabaku lfy," sun dade suna waya kafin sukai sallama, da gudu ta sauka daha gadon ta fita waje, karo sukai da shi, aiko ba tai wata2 ba ta dale shi tana ihun murna, " Farha is pregnanta Yah Amee, we ar going to be mums," wani irin yanayi ta jefa shi ciki, a hankali ya dora hannayen shi a bayan ta, ya qara rungume ta, rada mata yai a kunne," kinga muma in kika ci gaba da bani hadin kai sai kema next yeh ki zama mum, ko yau kk ban dama nan da 9month za a iya kiran ki Mummy," a hankali ta fara zame jikin ta cike da kunya, tana dariya qasa2 zata gudu, har ta taka da gudu ya bita ya riqo ta, romancing din ta yake kamar ya zauce, tin yana yi shi daya ta fara biye mashi, daki ya kai ta, suka sha sha'anin su hamshaqiya Naufaliyya bata nan,aiko tsautsayi ya sa sukai bacci suna manne da juna... .. *OH my God she is going to........ me kuka ganin zata masu readers?* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *Wow ! I must say thanks to all my fans, u guys ar awsome,ur comments give me the urge to write more and more to u, i wish u enjoy and lern so many things in this novel, don't forget that i love every and each one of u guys. HAERMEEN HAERMMAERH LOVE U XOXO❤* Page 25: Leqa ko ina take na gidan amma shiru bata gan shi ba, sannan bata ji wani alamu na yana gidan ba, tinani tai maybe ya wuce masjid, duba da lokaci wajen qarfe 2:40pm wataqila daga sallah bai dawo ba, kaiii amma ai baya kaiwa haka, ana idarwa yake dawowa, miqewa ta yi tai hanyar kitchen wanda direct kana hango dakin Lamyah ne, kallon qofar tai cike da kishi tana hararar wajen, ai ko ta ga hular Ameenullah, irin qaramar nan ta saqa a qasa daf da qofar dakin, wani ashar ta saki ta zabura tai wajen da gudu kamar mahaukaciya, bata tsaya bata lokaci ba ta banka qofar, daga yanda ta bude qofar Lamyah ta farka amma jin alamun Naufaliyya ce sai tai kamar bacci take, juyi tai ta qara rungume shi, shima cikin baccin ya qara manna ta da qirjin shi, yai murmushi, tare da furta " I love u so much qanwata," wani mahaukacin naushi ta kai mai a fuska, a gigice ya miqe, ta dale gadon, ta kai ma qiejin shi naushi, " har fada mata ka ke kana son ta, gaba daya Ameenullah ya gama firgicewa, daga hannu tai zata qara kai mai naushi, taji an buga ta da qasa, dubawa tai taga waye? Lamyah ta gani a gefe ta dau riga tana sawa kamar ba ita tai ba, yunqurawa zatai ta miqe kafar ta riqe, ga azabar da zuciyar ta take ga azabar kwadata da qasan da akai, wanda har yanzu ta kasa gane aikin waye a acikin su, kuka ta saki mai cin rai, yau mijin ta ne a jikin wata, " tashi ka fita," shine a binda Lamyah tace ma Yah Amee din ta, fuskar ta ba wasa, dan tabbas ta fison ita tana korar shi kafin shi ya tafi ya barta da ciwon zuciya, miqewa ko yai, ya debi kayan shi yana sakawa, ganin shi ba kaya yasa Naifaliyyah kusa sumewa, mijin ta ne dakin wata kuma ba kaya? Ya Allah , " for how long kuka dauka kuna cin amana ta a gidannan?" Ta fada hawaye na bin fuskar ta kamar wadda ta kama kwato da 'yar ta, Ameenullah ne ya tsaya zai mata bayani Lamyah ta daka mai tsawa akan ya fita mata a daki in yaje can ya wa matar shi bayanin, ficewa yai da sauri, tabbas in yana bin umarnin Lamyah to ita yasan dalili, ba dan komai bane sai dan son ta da yake, da kuma kasancewar ta wani sashe na jikin shi, kuma abinda tai bai ga laifin ta ba in dai za ta na bashi hadin kai, ita ko Naufaliyyah tsoron ta ne yake ji ya cika mai ko ina na jikin shi. Qoqarin miqewa take ta bi bayan shi ta sauke mai kwandon bala'i amma fa sam ta kasa miqewa da alama tai targade ko buguwar qashi tabbas, Lamyah ce ta tako gaban ta a hankali, " bari na fada maki wata magana bitch, ki sani Yah Amee nawa ne, aro na baki, is like baki san meye zuru ba, zuru na miki naga iya bakin qoqarin ki na iko da isa da mallaka, amma naga alama na kai gejin da ba zan jure duk wani iskanci daga macen da na raina wa aji da komai ba, ki duben ki dube ki, in ba qaddara irin ta Allah da yake wa bayin shi ba, ya qaddara masu abu kuma su bi shi su samu lada, ni nafi qarfin ko wacce mace ta kusanci Yah Amee dina, dan kuwa komai da yake buqata zai same shi a nan, ke kan ki kin san ba ki fi ki zama mai aikina ba, amma tinda Allah ya hada mu dole na sauke haqqin ki akaina, ina me gargadin ki da kema ki fita harkata, ki saken haqqina dake kan ki, in ba haka ba ......." mamaku ne fal zuciyar Ameenullah dake tsaye bakin qofa, da ita kan ta uwae gayyar, ashe Lamyah tana da baki haka,( habaa kun manta wace qawar ta) zuwa tai zata wuce ta gefen ta tana sane ta take mata yatsan hannu qaramin, qara ko ta sake, nan da nan Lamyah ta juyo kamar gaske," Opsyyy ban gani bane, a ficen a daki kan na fito wanka, bana son na fito jikina ya ga naki, na qara datti," shiegewa tai tana kada jiki,Naufaliyya kamar ta hadiyi zuciya, a hankali ta qoqarta ta tashi,aiko ta saki qara qafarta tai tsami sosai, Ameenullah ne ya shigo ya dauke ta cak, dik da dukan da take kai mai a qirji, amma bai sauke ta ba, zuwa sukai dakin su ya aje ta a gado, qafar da ya kula har ta dan hau ya kamo, ta ko sake ihu, ya kama ya ja sosai, nan d anan tai wata qara, a take ta nemi ciwon ta rasa, ya gyaru, ai ko dira tai ta fara masifa, wani abun ma bi kmata ace ko da da karuwa ta gan shi ba ta furta, amma inaaa ba da'ar wannan komai yazo mata fada take, shidai bai ce komai ba kan shi a qasa kamar wani soko,ko gama wa batai ba ta zari jakar ta da key din mota ta fice, shi kuma toilete ya shiga, wanka ya fara ya tina da moment din su shida Lamyah, da yanda ta saki jiki da shi, suka sha soyayyar su, da yanayin shagwabar ta mai kyau, sannan Lamyah ta iya tattausan lafazi, ta na da girmama mutum, murmushi yai da ya tina yanda take ambatar Yah Amee dina a da da yanzu, wani dadi da so da qaunar ta ke ratsa shi, a haka yai wankan ya fito, kimtsawa yai yai sallah, dan sun makara sosai. Lamyah na can ta shirya tai sallah, yau tinani tai itama bari tai kwalliya kamar mace mana a gidan mijin ta zaman daki ya qare sai na parlor yanzu,itama ai gidan ta ne, wasu riga da skirt na atampa ta dakko, Farha ce ta kai masu dinkin, ba qaramin kyau sukai mata ba, sun matse ta ta duk in da ya kamata, ta kafa dauri, sannan ta feshe jikin ta da tirarika masu matiqar qamshi, takalmi tasa mai rangwamen tsini, baqi, inda atampar jikin ta tana da ratsin baqi da pink, sai dan fari a jiki, kitchen taje tai masu abinci mau dadi, ruwan shan su ta samu ta tope shi da ayatul kursiyyu, 7 falaq 7 nas 7, ikhlas 7, tai amanarrasul 7, sannan ta topa a abincin su ma haka, ta dauka tai parlor, dakin Ameenullah ta nufa, tana shiga ta gan shi kwance yana kallon sama, isa tai gare shi ta kwanta a saman jikin shi, wata ajiyar zuciya mai qarfi ya sake , dan hasan wace ko a mafarki yake, " Yah Amee na tashi muje mu ci abinci yunwa nake ji ," kamo ta yai ya juyar da ita ya zama shine a sama yana binta da wani kallon so da qauna, yaushe ya samu matsayin cin abinci a gidan shi, hmmm ," My Lamyan na gode tashi muje," daga ta yai bayan ya mata kiss a lips suka fice, zama sukai suka ci suka sha sukai qat, Ameenullah kawai abincin hotels din daya taba shiga yake hangowa, amma sam bai ci mai dadin wannan ba, matsawa yai kusa d aita ya hau kissing din ta, a haka ta banko qofa, tana shigowa ta daka salati, amma Ameenullah ko gezau bai ba, Lamyah ce ta dan zame kadan, ta kalle ta,shima ita ya kallah, har yanzu akwai tsoron ta a jikin shi, amma sai yaji kamar an dauke mai kaso 30% muqewa yai zai shige dakin shi, ta bashi umarni suje dakin ta, bai musa ba ya bita, hararar Lamyah tai, dan ta gano ita ta bugata da qasa dazun, in tace zata ci gaba da biye mata kassara ta kawai zatai kamar yanda bokan ta ya sanat d aita yanzunnan da ta fita," ki rabu da yarin yar nan physically and spritually, ni dai kam tafi qarfina, ke kuma kin ga abinda ya same ki ai wajen yin fada da ita, duk wanda rai yaiwa dadi bai kai ya mai shi ba ai ko?" Tina hakan da tai ne yasa ta buga uban tsaki tai daki, zaune ta gan shi yai shiru, masifa take ta mai amma bai tanka ta ba, wani yunqurin tashi ya mammake ta yake ji amma ya kasa, shine dalilin shirun na shi, zuwa tai jikin shi ta kwanta ta hau kuka," ni dai Allah yanzu ka daina so na, gaba daya waccan figigiyat yarinyar tana neman dauken hankalin ta, dan Allah ka daina kula ta kaji," wani kallon baki da hankali ya mata, sannan dama wayace yana son kin? Amma a zahiri janta yai jikin shi ya hau lallashin ta, miqewa tai tace" bari na debo maka ruwa, ka sha", mamaki da dariya ta bashi, yaushe yake da wannan arziqin? Murmushi yai yace ," na qoshi yanzu naci abinci na sha ruw,"a ranta ko tace inaa ka isa yau dinnan zaka sha wannan abun nawa da ma zo da shi ba zaka min salalan tsiya ba ina ji ina gani, ," k shikenan ," matsawa tai jikin shi zata fara maii aikin na ta da ba gajiya take ba ya miqe yace yanzu za a kira la'asar bari yaje ya shirya,baqim ciki kamar ya kashe ta,ficewa yai dakin shi kamar ba Ameenullah da ta mallake da asiran ta ba," hmmm we shall see" ta komar da kan ta ta kwanta. Yau tin asuba Mubarak ke murna,ya hada duk wani abu da zai kaiwa Mummyn shi, sannan ya fidda kayan da zai saka, Momma kam data shigo tada shi Sallah ta gan shi yana surutan me zai ce ma Mummyn shi in sun hadu, dariya tai ta yi, tana kwaikwayon shi,haka ta koma dan ganin idon shi bude, amma ta sanar da shi yai sallah, qarfe 1:05pm a farfajiyar gidan ameenullah tai masu, Lamyah tai girki mai dadi, ta yi drinks kala2, sannann ga kwalliya ta ci, dan ita tayi ne sabida yau zata kira Yah Amee din ta yaci abinci, dan tana ganin ta wannan hanyar ne zai samu sauqi.daga kowanne mugun abun matar shi, a hankali kuma sai ta sa ya gyara yanayin ibadar shi, ta aje plates ne taji dan qaramin hannun da take kwana da tashi da tinanin shi ya riqe ta ta baya,juyawa tai da sairi suna ganin juna sai murna, da gudu ta sake shi tai wajen Momma, ta fada jikin ta, sai murna take, wajen Baaba taje ta duqa qasa ta fara gaida shi, " Tashi tashi diyata,," kama hanun ta yai suka je kan kujeru, suka zauna,gaisuwa suka sake yi, sannan suka tambaye ta Ameenullah ta shaida masu yana daki da Naufaliyyah, ammabari taje ta kura su, miqewa tai ta tafi, tana zuwa ta hau kwankwasa qofa, tai tai taji shiru, can taji hamshaqiyar tana," ka tashi kaje kafin wannan ballagazar ta karya mana qofa," zuwa yai ya bude qofa, nan da nan qasan zuciyar shi yana mai kamar ya dauke ta ya gudu, amma kuma a saman zuciyar shi wata tsanar ta yake jin na taso mai, ," malama meye?," hadiye baqin cikin ta tai tace, Baaba da Momma ne suka zi," yaji dadi sosai kamar ya tafi da gudu ya rungume su, dan yai missing din su, amma inaa sabanin haka ne ya biyo baya," shine zaki zo kina damun mu muna hutawa? Bacen da ga nan,kice bana nan in kun koma,"wani sakin baki tai ya. Rufe qofa ya barta nan tsaye, a sanyaye ta koma," na ju komai bar su Allah ya fidda shi daga halaka," amsawa sukai dika sukai ta hita sosai, ita ko duk zuciyar ta ba dadi sosai, a haka har suka tashi tafiya, ta sha kuka kuwa sosai, ita da Mubarak,ji tai kamat ta bisu. Waya suke da Farha ta kwashe komai ta fadawa Farha, "kan uban can, tin yaushe ake maki hakan baki fadan ba sai yanzu, lallai zuwa Nijer ya kama ni, sai na gyarawa wannan qaramar Yar barikin zama........ *Ina zuba ido naga zuwan aunty masifa, wake jira ? Ko ni daya ce?* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *Sis Juwaireren Mama Allah ya baki lfy ya sa kaffara, sister ku yata 'Yar uwata addu'a pls, Allah ya bata lfy*😭 Page 26: Wai ance sabo da yi gawa da gatsine, yau rawar ce ta motsawa Lamyah, a parlor take, cikin shigar ta ta qaramin wando, da yar figigiyar riga, kalar pink, sai band din data daure gashin ta, in a pony tail style, bayan ta dan raba shi daga tsakiya kadan, ga qamshinnan na tashi ko ta ina, wata irin sarqa ce da rigar tazo da ita golden a zagaye da qugun ta, kida ta kunna tana taka rawa a hankali, tana jin dadin yanayin idon ta rufe, dan a kan idon ta Naufaliyya da Ameenullah suka fita, rawa take tana juya kowacce gaba ta jikin ta, a yanzu Lamyah ta qara cikowa, ko ina na jikin ta yai dim da shi, Ameenullah da ya dawo ne ba tare da tasan yana tsaye daidai qofar shigowa ba ya qura mata ido ko qiftawa baya yi, wani yawu ya hadiya, ga qoshi ga kwanan yunwa, rawa take ta kai sama tai qasa juyi take da hips din ta kamar ba a jikin ta yake ba, tin da yake ganin rawar ta bai taba ganin irin ta yau ba, a cikin rawar ne ta zame band din kanta, gashin ta ya sako ya baje a bayan ta, ta yo gaba da shi sannan ta saka yatsun ta tai baya da shi, a hankali ta maida qugun ta gefe, ta juyo da kanta daidai saitin Ameenullah d ya sake baki yana kallon ta,suna hada ido taji gaban ta ya fadi, wani irin tsoro ne ya kama ta dan bata san da dawowar shi ba, nan da nan ta nemo remote zata kashe, umar ni ya mata da ta bar shi, a cikin jikin shi yake jin kamar ya shaqe ta dan tsana haka kawai yake jin haushin ta, amma qasan zuciyar shi wani irin so da qaunar ta ke mai yawo a ran shi, musamman na kallon 'yar iska da yake mata a da kuma ya ji ta ba haka ba, sannan kuma ya ganta tana da ibada,matsalar ta daya wannan rawar, shima kuma tana dada sace zuciyar shi da ita, dan ta san yanda zata sarrafa jikin ta, jitai ya kamo qugun ta da qarfi, a hankali yaso mata, amma bangaren dake jin tsanar ta ba zai bar shi ba,tsanar ba gaira ba dalili, yar qara ta saki wadda ta qara daga mai hankali ta qasan zuciyar shi, kafadar ta ya kama da take a bude,da nufin ya shafa, amma ya matse mata da qarfi sai da idon ta suka yo waje, " Yah Amee pls stop u ar hurting my shulder pls," hawaye ne ke zuba a idon ta da gudu,qoqarin kwace jikin ta take, amma ba hali,gaba daya komai na shi ya gama kwancewa, anger, lust, duk sun baibaye shi, ga kuma tausayin ta dake damun shi, ganin kukan ta ne ya sa ya sake ta da sauri ya daga hannayen shi sama, alamar defence, kawai bin shi tai da kallo cikin damuwa da tinani, daki ta shiga da gudu tana kuka, shi kuma ya zauna a wajen yana maida nunfashi, tare da zirarar da hawaye, wani na bin wani, " meke damuna ne, Ameenullah ka tina fa wannan yarinyar amanar ka ce, ko ka manta Ammiin ka da Abiin ka ne, ka manta wace ce Lamyah a gare ka? Nooo ban manta ba, kawai ji nake na tsane ta,bana son ganin ta, ji nake inna ganta kamar na shaqe ta, amma ina son ta, ina son ta, ina son ta ina qaunar ta," ya durqushe a qasa yana kuka sosai, bai san meke damun shi ba, ya zai yi," pls someone should tell me what to do," shine abinda yake ta fada kenan, Lamyah ce da ta jiyo kukan shi na qaruwa ta fito cike da tausayin shi, a yanzu ta cire kayan can ta zura riga doguwa, dik da dai ba wata doguwa bace sosai amma ta kai qaurin ta, sai dan kwali data daura, rigar nada dogon hannu, da atampa aka mata, sai aljihu guda biyu gefe da gefen rigar ta sama ta matse ta qasa ta bude sosai, ba qaramin kyau kayan suka mata ba, dan tana shiga data fara kuka, ta jiyo Ameenullah na yi yama surutai sai taga rashin dacewar zaman ta tai fushi da shi,bayan ta sam meye matsalar shi, dalilin sauyawar ta kenan, ta fito gare shi, miqa mai hannu tai, ji yai kamar ya dauke ta da mari amma ya miqa mata nashi,kamo hannun shi tai, ta zauna a kujerar ta kwantar da kan shi a qirjin ta tama shafa bayan shi a hankali, daga sama zuwa qasa,ajiyar zuciya yake ta yi, a hankali ta ke rera karatun qur'ani mai girma a kunnen shi, wata nutsuwa ce ke shigar shi, suratul baqara ta ke karanta mai, wani irin tashi tsigar jikin shi ke yi, ba na wasa ba, nan da nan jikin shi ya hau karkarwa, tsoro ya cika zuciyar Lamyah, da za a ce fir a lokacin data taka, amma in bata tsayawa mijin ta ba ba mai tsaya mai, ci gaba tai muryar ta na rawa, a haka tin yana jijjiga har y daina jikin shi ya sake yai mata nauyi sosai, minshari taji ya fara, alamar yai bacci kenan, wayar ta ta zaro a aljihun ta guda biyu, kowacce ta kunna karatu, daya suratul ali'imran,daya ta kunna suratul jinn, ta ci gaba da baqara da bakin ta, bacci ya samu mai nauyi sosai har wajen La'asar, yake ta bacci, ita kuma bata gajiya ba, ga dai shi ya mata matuqar nauyi, qirjin ta kamar zai fashe take ji, amma haka ta hakura, da kan shi ya farka,cikin ambaton Allah, da addu'ar tashi daga bacci, daga kai yai ya kalle ta, ya mata murmushi, itama murmushin ta mai amma fa na yaqe, dan yana daga ta wani zafi ya daki qirgin ta, na gajiya, kiss ya mata a goshi, sannan ya miqe ya nufi dakin shi, yana shigewa ta durqushe tana yarfe hannu,tana " wash Allah Yah Amee ba dai nauyi ba , wayyo qurjina, " tana yi tana fidda iska daga bakin ta tana shaqar wani, alamun bude qofar shi taji, tai maza ta qame tana mai murmushin yaqe, murmushin shima ya mata, ya wuce masjid yana fita ta miqe a dudduqe tai daki tana raki, alwala itama tai tai sallah, sannan ta dakko jug ta hada mai fresh jus, sannan ta kai daki, ta maida hijab din ta har qasa, ta dakko hisnul muslim din ta ta hai karanta mai addu'o'in duk da suka kamata,sannan tai mai Ayatul kursiyyu 7, Iklass 7, falaq 7, Nas 7, Amanarrasul 7, sanna ta mai suratul jinn 3, ta dade zaune tana addu'o'i dan so take daga yau,ko wanne asiri ya kauce a jikin Mijin ta, ya bassu sui rayuwar su mai inganci, tana gamawa ta cire qaton hijab din ta ta wuce kitchen, aje a cikin fridge, ta fara masa girki mara nauyi, a ruwan girkin ma sai da tai wadannan addu'o'in da karatun, a haka ta masu french rice da vegitable stew, a gefe kuma ta masu papar meat with boild egg a ciki,yaji kayan kamshi, da na lambu, ba qaramin kyau abincin ya bada a ido ba balle qamshin shi dake tada yunwa ko a qoshe kk zakaji kamar an maka yasa😉 hadawa tai tai wa a bincin bismillah akai 21, sanan ta rufe, daki taje tai wanka, Ameenullah da ya dade da shigowa, haka nan ya tsinci kan shi da jin kunyar ta na abubuwan da yai mata a baya saboda tsoron wannan yar kwal uban, ji yake ashe bai kai namiji da zai iya tsayawa a gidan shi ba, bai kai namijin da zai shiga taitayin shi ya riqi Allah da ibada ba, har sai yarinya qanwar shi ta zo ta nuna mai komai, ina renon da tarbiyya tare da dasa masa tsoron Allah a zuci da su Ammiin shi sukai masa ya tafi, nan take zuciyar shi ta tsinke hawaye suka fara mai zarya, Lamyah ce da ta sha wanka tai matuqar kyau, yau shigar material tai, doguwar riga har qasa, an mai din kun gayu, tsayawa ma fasalta dinkin zai batan dan lokacin dake hannuna, duk wanda ya ganta zai ma ce ta ci gasar sarauniyar kyaun da za ai bana, a gefen shi taje ta kwanta bata hana shi kukan ba, amma itama kukan ta saka, a firgice ya juyo dan jin kukan mutum a gefen shi, kuma na abar son shi, kusan suma yai da ya ganta," La...... laaaa....Lamyah?" Tsaida kukan tai ta kashe mai ido daya sannan ta cije lips din ta na qasa," ka gama kukan? Na zaci ba yanzu zaka gama ba sai na taya ka,kaga in abincin mu ya huce bamu ci ba, ka san yanda za kai dani dan bana cin sassanyan abinci," ta fada tana wani shagwaba mai tafi da hankalin mai kallo, wata irin kasala ta saukar mai ya janyo ta a hankali jikin shi, sannan ya miqe da su, daga baya ya daga ta cak sukai waje zuwa cin abinci, abinci suka fara ci bayan ta zuba mai, ta debo tai bismillah zata bashi, sai ta kauce sai ya miqo baki sai ta kauce, gaba daya yawun bakin shi ya tsinke,ji yake kamar ya saka hannu in ta hana," Lamyah ina wasa dake ne, ni ki ban naci in zaki ban ' Yar baqa kawai," aiko ta cika nan da nan," nice baqar, Allah Yah Amee yanzu na ma fika fari,kuma na fasa baka abakin ci d kan ka ai baqa ba ta ba fari abinci ba,"ta fada ta re da murguda baki daga qarshe, hakuri ya bata ya mata alqawarin siyo mata lots of Diary milk chocolate din ta,sannan sukai bismillah a tare suka fara ci da hannun su na dama, ba ruwan su da wani gayu,a ci abinci da wuqa da cokula wuqa a dama cokali a hagu dan tsabar bata. Bayan kammala cin abincin su ne suna zaune a parlor,suna hira, Lamyah na kan cinyar shi, ta raba qafar ta tana kallon shi, gaba daya ta yamutse mai sumar kan shi, shi kuma idon shi kusan a rufe suke, sun yi jawur, yana amsa ta da kyar, in sun yi hira sun yi hira, sai ta sunkuya tai mai kiss, lips din su gaba daya sun yi red, suna cikin haka Naufaliyyah ta shigo,yanayin da ta gan su yasa ta saki jakar hannun ta da sauri ta dafe qirji, tare da sakin ashar,basu daga kai ba sai da suka yi yanda suka saba, sannan suka saki juna, juyawa yai a hankali yace," malama ki fita sannan ki jamin qofar ki je gida har sai na neme ki, sannan, kar ki kuskura ku matsamin sai sanda na neme ku da kaina, in ba haka ba, a duk randa kikai yunqurin nemana a bakin auren ki dake kaina," kurma ihu tai zata shigo ta shaqe Lamyah, da ta rusa mata komai,amma inaaa wani mugun kallo Ameenullah ya mata, wanda ya matuqar tsorata ta, matuqa, bata taba sanin yana da fushi haka ba,Lamyah kanta a hankali ta zame tai gefen shi, ta tsorata ita kanta da ba da ita yake ba, Naufaliyya ce ta kalli jakar hannun ta, yau tin safe take neman maganin da zatai amfani da shi, Ameenullah ya ce ya saki Lamyah da bakin shi, amma yanzu farat daya wannan yarinyar mai zubin mutan boye ta rusa shi, kuka ta duqa ta rushe da shi,miqewa tai a harzuqe yai wajen ta,ai tana gano shi ta kwasa da gudu tai waje, buga qofar yai ya rufe, Lamyah matsiraciya ta saka ihu, tare da fashewa da kuka, ta qanqame waje daya, zuwa yai da sauri ya dago ta jikin ta sau rawa yake, hankalin ta ya tashi, zuciyar ta na ta harbawa, dariya ce ke son kama shi amma ya dake, sai ya rama raina mai hankalin da tai waje. Cin abinci dazu,zawa ya sakar mata mai qarfi," keeee meyee haka !, " firgicewa ta yi ta gigice ta saka kuka sosai, tare da kwabe baki, sai ga majina da hawaye na zuba, dariya ce ta kama Ameenullah wannan karon ba zai iya riqe ta ba, ai ko ya fashe da dariya ,yi take kamar an aiko shi, ita ko kuka take tin qarfin ta, miqewa tai da gudu za tai dakin ta,dan ta gane latsa mata hammata guy din keyi, kawai caf ya cafe ta yai dakin shi da ita, sai mutsu2n kwacewa take,amma ta hana, tin a hanya yake romancing din ta, da kyar ta kwace kanta bayan sun shiga, da kyar ta iya furta "Yah Aaaameee lokacinnn sallahhh ne faaa," tsagaitawa yai yana kallon ta, da idon shi da suka sauya, suka qara lumshewa, dire ta yai, a gado sanan ya wuce toilete yai tsarki yai alwala ya fice masjid, itan ma hakan tai ta koma dakin. Ta tai sallah, tare da aje azkar din ta ba tai ba, yana dawowa ta dakko hisnul muslim ta je wajen shi, addu'o'in yamma ta kwanta a cinyar shi tana yi da qarfi, nan take ya gane me take nufi, so take shima yayi, ai ko tare suka gama. wayar ta ce ta fara ringing, dagawa tai taga an rubuta Sweetheart F a jiki,dagawa tai ta shiga daki," Hello Sisto, ya abubuwan ke tafiya, na lallaba Bala da kyar ya barni zuwa amma tace sai jibi zan taho, dan haka kan na zo ki fara takalar fadan shegiya yanda dana zo zan qarasa cin uban ta," dariya Lamyah tai sosai tace" sannu iya masifa, kin sa kowa na jiran ya ga zuwan ku Nijer, musamman yan Group din BANI NAI KAINA BA, QASAI TATTUN MATA, RIBAR BIYAYYA, ZO KIJI YAR UWA, INA MATAN SUKE, da dai sauran groups, sai ki sha zaman ki" nan ta kwashe duk abin da ya faru daga farko zuwa qarshe ta fada mata, Farha cizin lebe tai da yatsa," Kashhhhh na si matuqa na zo na dan dirji shegen leben nan nata na qasa daya zazzago, jikin ta yai tsami dan uban ta,ta ji ba wai tsoron ta nake ji ba" dariya Lamyah tai sosai, Ameenullah ne ya shiga bai ce komai ba ya kwanta a kusa da ita, ya janyo ta yana shafa kanta, lumshe ido tai, ya fara mata wasa a kunne, nunfashin ta ne ke sauyawa, maganar farha taji daga sama," ke meke damun ki?" "Ba komai" itace amsar da ta bata da kyar, a daidai lokacin da farha ke son mata wata tambayar ne Aneenullah ya zura hannun shi a rigar ta,kashe wayar tai da sauri ta juya gare shi, yana ta mata dariya," ai na zaci zaki iya jure salo..., kan ya qarasa ta kai bakin ta na shi, ina ganin za sui abun manya na fece🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀kar su lalata maku ni😭😭😭.......... *Su Lamyah an shahara yanzu Oh ni Haermeen Haermmaerhna😭 na fece kan ta bata ma Haermmaerh na ni🏃🏻‍♀* *I am sorry for any typos coz is unedited* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *This page is for u guys* *Sis Ramlat* *Sis Hajjaju* *Baba Larens* *Bilkisu zarewa* *(GOGGOS)* *Fateema Radda* *Komai nake kuna raina Me love u XX*❤ Page 27: Naufaliyyace na hango a zaune a bakin dan qaramin gadon dakin Maman ta, dake malale da ledar daki, sai akwatin kayan ta da ke gefe alamar tin akwatin ta ne na da datana gida, Mamar ta ce ta shigo dauke da flask din abinci da cup a hannun ta," wai ni ba zaki bar wannan kukan da kk kwana kina yi ba, in sarautar sarkin kuka za a baki ai da tini an nada ki kowa ya huta haba, ko an fada maki kukan zai sa ya maida ki? Ki ci abinci ki sha, sai na fada maki shawarar dana yanke," tana jin haka ta miqe ta koma kusa da maman nata," mama sanar dani me zai sa na koma wajen Ameenullah da wuri, Mama bana son abinda zai sa mu rabu da Ameenullah, rayuwata zata wulaqanta, ki duba ku ga irin halin dana shiga a kwana daya, kin sani ina da.matsananciyar buqata, innai sati a gidannan zan koma ruwa, ga aure a kaina, Mama ki taimaka min," ta qarasa cikin matsanancin kuka, mahaifiyar ta ta tausaya ma gudan jinin nata, " karki damu Naufaa na, kamar bani ce uwar ki ba? Me zai daga hankalin ki? Bayan muna da boka aikatau, yanzu ya aikata mana aikin komawa Ameenu," " haka dai xaku qare, a yawon neman asiri ba, ba xaku zauna kui wa kan ku karatun ta nutsu ba, ki saka 'yar ki akan turbar gaskiya sai bata, akan shegen yawon asirin nan dubi dakin ki yanda ya koma,komai ya qare ya lalace, ina ce Uwar Ameenullah qawar ki ce? Amma gidan ta, dakin ta, surturar ta, wa zai hada dana ki, ke da sauran qawayen ki ma da basu biye2n bokayen, babban jahilcin ki har yau kin kasa gane su waye bokaye da malaman tsubbu da kk bi, na farko dai dan ni kk fara bin su, amma ko kin min asirin Allah ya bada iko ya kama ni, baki ganin yanda Allah ke warware man da qarfin roqon mai dika? A iya shekarunnn da muke dake, baki ganin cewa roqon Allah yafi roqon boka ko malamn tsubbu? Habaa ki bude idon ki da zuciyar ki ki gani cewar Allah na basu aron likaci ne , yana basu dama da iko akan abinda suka buqata ne domin ya musu talala, ranar gobe qiyama ya kama su da laifukan su, ku sani ke 'ya ta da kuma mata ta, Allah mai yawan gafara ne, mai karbar tuban bawa ne duk tsananin zunubin shi,har shirka , amma in lokaci bai qurewa mutum ba, kuna da tabbacin ranar da zaku mutu ne? An baku garantin mutuwa lokaci mai tsaho? Ko gajeren lokaci aka baku? Babu daya, dan haka kuji tsoron mutuwar fuji'a mutuwar kwaf daya, ba kusan a ina zaku mutu ba, me kukeyi za a karbi rayuwar ku, ki na aikata zina, kina aikata shan giya, ko kuna kan hanyar ki ta zuwa wajen boka la'anannen Allah? Ko kuwa kina sallah? Ko tasbihi? Ko karatun qur'ani? Ko yiwa iyaye ko miji hidima? Baki san fa lokaci ba,kin dage ke sai kin dora yar da kk haifa a cikin ki, wadda in kukaje lahira sai Allah ya maku hisabi akan komai, har tarbiyyar da kk bata, so kk ta kai qarar ki wajen Allah akan baki bata tarbiyha mai kyau ba? Kuji tsoron Allah, ku zauna ki kame kan ki, ki shiryu, ta dalilin haka Allah zai duba halin da kk ciki ya sa mijin ki ya dawo da ke,kuma batun sha'awa da kk magana akai ai ke kk jawa kan ki ,na farko wannan dure2n magungunan da kuke ke da uwar ki ku hana mutum sakat ai ta abu daya, ku a wahale mutum a wahale, ga na biyu baku banbance haram ke da girman ki kallon iskance2n turawannan kk a waya ko a talabijin, ga maganganun batsa da ba a rasa ku da ita, ke kuma yanzu zamani ya kawo maku wannan wayar ta jaraba,hirar batsa da qawaye maza da mata kina matar aure, ga karanta littafan batsa zalla wani mara tsoron Allahn zai zauna ya rubuta, kema da ba tsoron Allah ne ya cika ki ba ki zauna ki karanta tsaf, sha'awa ta tashi dole ki nemi mafuta, gashi yanzu baku son karanta wa'azin ma da zai amfane ku, sai iskanci, sai kun gama karantawa ku zo kundamu mutane suna zaman zaman su, to in baku gyara wannaj ba, wallahi Allah nesan ta ki zai da Ameenu na fada maku kenan," Baban Naufaliyyah kenan Alhaj, Rabi'u, tinda ya fara wa'azinnan jikin su ya mutu, zuciyar su ta tsinke sosai kuka suke sosai gaba dayan su, a qasan ran su suna dada tina tabargazar da sukai a rayuwa, kowa na tina rabon data kafa goshin ta a qasa da sunan sallah an dade, ba magana Maman ta ta miqe ta bar dakin, kuka ta kwanta tana yi a zuciyar ta tana istigifari, har dai ta miqe ta fita dan dajra alwala, tana yin alwala tinani ta tsaya yi, to ita ta inama zata fara rama sallolin ta? Kuka ta rushe da shi na tsantsar tsoron Allah, tsoron tinawa da irin azabobin daya tana da domin masu wulaqanta sallah, nan da nan ta fara sallah ba ji ba gani, dan tasan Allah ba dauke mata zai ba, ta bi da istigifari. " Wash Allah, Mine dan tahon da wannan cup din na gefen gado dana aje," dauke da cup din ya fito ya zauna kusa da ita, cikin tsokana ko ya kai cup din bakin shi, warcewa tai ta fara shura qafa," Tab yau inna yarda na zama danwake yara sui kalace da ni da safe, ina ruwan ka da abinda ke cikin cup dina zaka sha min, Allah ni ka biyani abuna," kukan gaske ta fara mai," Haba My Farha, ni ne fa mijn ki Bala abin son ku," " kai ni kar ka wani min dadin baki,tashi ka hadon wata madarar kuma madara cokali biyu, millo cokali uku, ka gauraya kar ka sa sugar, kar ka sa ruwa," " amma dai kin san asibiti sun hana ko," " kai rabu da su qaryar vanza ce, itama likitar dana je tsohon ciki gare ta,yaji ta dauro a leda tana barbadawa a hannu tana sha, shi shan yajin basu hana mu bane? Amma take tandewa, ni debon kae yawuna ya gama zirarewa, ka tashi mana kana bata lokaci Hubby," ta qarasa cike da shagwaba tana buga qafa,miqewa yai yana " Farha halin ki sai ke, Allah ya sa in kin haihu ki rage wasu," " me kace ? Ni dai ko lashe kar ka lasar min abuna ehe ina hango ka bari ma ka ga na biyo ka,"dariya Bala yake sosai, a ranshi yana ayyana kar su haifi yara masu rowa, tinqis2 ta bishi, dan yanzu ta danyi qiba ba laifi, yana hada mata ta amshe tai godiya ta kona ta zauna, lumshe ido tai kawai tana afawa, ga surutu fal bakin ta amma dadin wannan hadin madarar ya hana ta, sai ta dakko zata fesa dai ta tsaya,haka har ta sha iya shan ta tai bacci a wajen,gyara mata kwanciya yai ya rufeta, zama yai ya qura mata ido yana murmushi, lallai xuwan Farha rayuwar shi alkairi ne,gashi ya samu aiki da babban muqami, ga kudi na zuwa mai ko ta ina, ya sau gida ya sai motar kan shi, sai dai bai ma saka ranar tarewar su ba, dan Lamyah tai uwa tai makarbiya tace bazaau bar gidannan ba, in dai ba wasu nasu zasu saka ciki ba. *RIMIN GATA* " kash subhanallahi,wai sau nawa zan fada maki je Saddiqa ki na maida hankali wajen ibada ne, duba lokacin sallah fa ki gani kina kwance abin ku," "dan Allah Yah musaddiq kai hakuri,gaba daya jikina ne a mace zuciya ta na ta tashi shi yasa, yauwa dama ina son fada maka, dazu Delu ta aiko wannan wai na sha maganin mallaka ne," ran shi ne ya baci ainun, dan wannan karon ya ga alama zuwa zai har gida ya tsefe wannan shegiyar tsohuwar, dan yanzu tsabar son da Saddiqa ke mai yasa gaba daya sai a abin da yace shi zatai, shi kan shi yanzu ya fahimci abin da Lamyah ke fada,dayai sanadin shiriyar ta gashi yana jin dadin zama da ita, sai dai fa konda wasa baya barin ta fita, baya bari taje ganin gida, sun yi mitar,sun kai shi qara wajen mai garin, har sun gaji, ga shi yanzu tana da shigar cikin wata uku, ba qaramin son cikin yake ba, Innar shi ma haka, ga mai gari daya qosa yaga jikan shi, gata take sha ko ta ina, tana matuqar son ganin 'yar uwar ta da yake bata labari kusan ko da yaushe, ta kwadaitu da son ganawa da ita, gashi layin da suka basu na waya baya shiga, ta gefe daya kuma Delu kushe mata Lamyah da zuri'ar su kullum take in ta zo,she is so confused,so take kawai taga wacece Lamyah ta karance ta da kan ta ta nemi ajin saka ta a zuciyar ta, duk da tana jin qaunar ta a ranta, dan a dangin su kaf ba mace kusan kamar ta, sai dai labarin Lamyah kawai da take ji, " da wannan dogon tinanin da kk da miqewa kikai kikai alwala," miqa mata hannu yai cike da shagwaba ta kama tana narke mai," A'a fahh ni ki daina min wannan salon baki sallah ba,dan kin san b hakuri na cika ba ni, kuma inna tsaida ki lokaci wucewa yake, je ki alwalar in kin isa ki dawo ki min haka ki gani," cike da dariya ta kwace hannun ta ta wuce shi," kwalelen ka dan ni ba lfy na cika ba ehe," " haka kk ce ko, to amarya zan miki,"kuka ta saka tana buga qafa," ke baki san wasa ba ,kece fa amarya kuma uwar gida ba wata ta biyun ki balle ta ukun ki, har a samu ta hudun ki, kwantat da hankalin ki, maman Aishaaa Lamyah,"wani dadi ne ya kama ta ta fice tana muemushi, dan sunan da suke son sama diyar su kenan in macece. Yar guje2 naga suna yi a tsakiyar parlorn su, dikkan su ba wasu kayan azo a gani ne da su ba, as usual shigar ta ce ta qananan kaya, shi ma daga boxer sai vest, yayi 'yar qibar jin dadi da hutu,yai matuqar kyau,kalar shi sai haskawa take, haka itama ba qaramin kyau tai ba, gashin ta ya sha gyara, kamota yai yana mata cakulkuli tana ta dariya, da kyar ya qyale ta suna maida nunfashi, miqewa yaga tayi," ina zaki?" Bata amsa shi ba taje ta kunna kida ta dawo ta zauna," wai yaushe zaki dai na RAWA ne," " sai sanda na girma, tin da kullum ce min kake yarinya," ta qarasa tare da turo baki, dariya yainsosai, itama ta biye masa,kama hanun shi tai ,"yau so nake mui rawa tare taso na koya maka," miqewa yai ya bi bayan ta, rawa ta fara takawa a hankali, tana juya jikin ta a nashi, ji yai lallai da haka rawa take kar Lamyah ta daina ta, tai tayi kullum, suna cikin haka ne suka ji kwankwasa qofa......... *wa muka samu kuma ya katse mana RAWAR mu☹* *Unedited really sorry for any typing error fans,Me Love u all*❤ [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Page 28: Miqewa suke qoqarin yi su shiga domin suturta jikin su ne aka murda knob din qofar aka shigo, Naufaliyyace kan ta a qasa sai Maman ta, dake biye da ita, dago kan ta da zatai tai mummunan gani, dan Ameenullah ne dauke da Lamyah sun dauki hanyar dakin shi, yana ganin su ya hade fuska, sanye take da qaton hijab, har qasa, fuskar ta dauke da annuri, alamar nutsuwa, amma kishinnan na maqale a ranta, addu'a ta fara na Allah ya kawar mata da mummunan kishi, a hankali taji zuciyar ta na sanyi, ba sui masu izinin shiga ba, su kuma basui yunqurin shigewa ba, Lamyah ce ta dira qasa, tai dakin ta a kunyace, dan a qallah akwai babba a wajen, yanayin su kuma yayi girma vabba ya gan su haka, Ameenullah ne yai qoqarin shigewa shima, " Yah Ameenullah mu shiga ne?" " Da ni na kawo ku?" Yai shigewar shi, dakin shi, Lamyah ce ta fito sanye da doguwar riga baqa mai fadin qasa sosai, kanta ba dankwali as usual, gashinnan a baje a gyare, izinin shiga tai masu, ta durqusa har qasa ta gaida maman Naufaliyyah, bayan sun gaisa ta miqe tai kitchen ta debo masu drinks, sannan ta hado da snaks, ajewa tai gaban su, aiko ba kunya ba tsoro suka fara diba, Lamyah baki ta sake daga baya ta hade bakin ta, sakamakon murmushin yaqen d Naufaliyyah ta sake mata, miqewa tai ta basu waje, dakin Yah Amee ta shiga, samun shi tai zaune ya dafe goshi, janye hannun shi tai ta zauna kan cinyar shi, ya zagayo hannun shi yana kallon ta yana lumshe ido, goshin ta ta hada da nashi, a hankali yake dago fukar shi yana qoqarin kissing din ta, kwalele take mai, sai tai qoqarin kai nata amma sai tai brushing lips din ta ta janye, magana ta fara mai," My love, ina neman alfarma a wajen ka, ina roqon ka da kome zasu ce maka ka tsaya ka nutsu ka amshi yafiyar su in sun nema, domin duk abin da suka maka nima ya shafen amma ni tin randa ta bar gidannan na ji ban ji dadin tafiyar ta ba, nai shiru ne gudun bacin ranka, amma ni gaskiya ina buqatar dawowar ta, ba dan bana jin dadin zama na da kai ba sai dan ina tinanin Momma bazata ji dadin barin diyar qawarta da kai ba, kuma kasan rashin jin dadin mahaifiyar ka akan ka ba a bune mai kyau ba a rayuwar ka duniya sa lahira, akwai matan da suke ma mazajen su abinda yafi na Naufaliyya kuma a hakura a zauna, plss my baby kai hakuri kaji," ta qarasa tana wani irin juyi a jikin shi, tare da motsa hips din ta, cikin hanzari ta qarasa riqe lips din shi , kamar jira yake, tana ji ya kama tai qoqari ta zare tana mai dariya, "je ka ka dawo zan maka wani abu" yana lumshe ido ya fita, kifewa tai a wajen tana kuka mara sauti, kishi ne danqare a cikin zuciyar ta, amma sai ta tina da Hadith din Rasulullah da yace" imanin dayan ku baya cika sai ya so ma dan uwan shi abin da ya so ma kan shi," ta haka ne kawai take ganin zata iya daidai ta su, in ba haka ba yanda Yah Amee ya dau fushi bata jin zai saurari kowa akan Naufaliyyah dan tin da ta tafi ko da batan hanya bai taba kiran sunan ta ba. Bayan gaishe2 da sukai, idon shi ya sauka kan Naifaliyya da ta qura mai ido, tsaf ya gane irin kallon, dan guntsun tsaki yai ya kauda kai, dauke idon ta tai daya ciko da hawayen, ta cije lips din ta, " Ameenullah naji labbarin duk abinda yarinyar nan ta aikata, kuma a gaskiya na zo nan ne domin baka hakuri, domin duk abinda tai akwai sa hannuna ciki, da kuma gurbatacciyar tarbiyyar data samu daga wajena, mahaifin ta ya mana waazin da ya shiga zuqatan mu daga ni har ita, dan son Rasulullah kai hakuri, ka yafe mata, ka kira abokiyar zaman nata domin ta bata hakuri, tabbas mun cutar da ku," ta qarasa cikin tsananin nadama wadda ta kasa boyuwa a fuskar ta, jikin shi ne yai sanyi da yanayin su dika, tabbas akwai tsantsar nadama a tattare da su,miqewa yai ya shige bedroom din shi, kwance ya tadda ta, tayi kuka har ta gaji, fuskar ta tai ja,musamman hancin ta, dago ta yai yana bubbuga bayan ta, saurin miqewa tai tana yaqe, murmushi ta so yi amma tai failing,hawaye ne ya biyo baya, girgiza mata kai yai," in ina ganin hawayen ki zaki sa na koma na kore su dan ba zan taba aje abinda zai bata maki rai ba," da sauri ta share hawayen ta tace," kayi hakuri ba zan qara ba," murmushi yai ya ja ta toilete ya wanke mata fuska, ya bazo mata gashin ta ta gaba,yanda zai diga rufe fuskarta, sai dai idan ta mayar da kanta, kama hannun ta yai suka fita, tana ganin sun kusa wajen su tai qoqarin kwace hannun ta amma yaqi, a tsaye ya tsaida ta gaban Naufaliyyah," ke na fara aure kafin na ga qanwa ta farin cikina, kafin na samo alqawari na da na dade da burin samu, na aura kafin kowa, ke ce macen da ta fara kasancewa da ni a matsayin miji, kin yarda damar da kk samu da matsayin ki, in kina son zaman lfyr ku daga yanzu zuwa har abada, ki zauna lfy da ita, na san wacece Lamyah, ba ta da son hayaniya, in ba taba ta akai ba, ba ta da fada in ba janta akai ba, ke kuma na san halin ki, kowanne, dan haka ku zauna lfy da juna ku riqi Allah a zamab ku,kar kuna sani gaba a zaman ku, kuna saka Allah a zaman ku, domin in kuna saka ni a farko zaku na sabawa Allah,zakuna shiga haqqin junan ku, shi aure ibada ce, kuma ba kowa ake wa ibadar nan ba face Allah,dan haka in kuna son samun nasara duniya da lahira kuna tina Allah, ko sabani kuka samu, in da hali kuna warware shi a tsakanin ku, ta hanyar tattaunawa a junan ku, ku zama kuna ma juna uzuri, sannan kuna ba juna hakuri akan laifukan da kukaiwa juna,...." nasiha yai masu sosai da ya sa a cikin kaso % na kishin su kashi 50% ya fice, zuqatan su suka samu nutsuwa sosai da shi, hannu ya miqawa Naufaliyyah ta miqe ta isa gare shi,ya hada su ya rungume, Maman ta ce tai gyaran murya, sika sa dariya dika, cike da kunya,bayan ta masu addu'ar zaman lfy ne sai ta masu sallama ta tafi, zaunar da su yai akan doguwar kujera, " da farko dai kusan nace komai ya faru Allah ya qaddara hakan, amma tabbas akwai rashin bin dokokin Allah dake jawo komai ya tavarbarewa bawa, ya rasa dalilin faruwar abubuwa marasa dadi a rayuwar shi, a qa'ida ya kamata tin da akai auren mu da Lamyah yazama mun raba kwana atsakanin mu, amma bam hakan ba, muka ci gaba da zama na tauye haqqin ta, dan haka a yau ina son mui magana a tsakanin mu kwana nawa ya kamata muna yi?" Lamyah ce ta kalli naufaliyyah ta mata alama tai magana," da farko dai ina mai qara ba ku hakuri ku yafeni, akan soj zuciyar dana aikata maku, kuma ina ganin kwana biyu yayi, a gani na fa amma," ta fada cike da murmushi, dik sin aminta da hakan, Lamyah ce ta miqe ta fara takawa," to ango da amarya ni na shiga ciki, na barku lfy," Ameenullah ne ya sake baki, a ranshi ko gani yai wannan yarinyar ta gama da shi, tabbb, ina alqawarin da ta mai? Lallai za a yi ta, ya nuna bai yarda ba Naifaliyyah taga ba a kyauta mata ba, cikin yaqe ya juya ya hada ido da Naufaliyyah da ta gane kwata2 ranshi bai so ba, amma ya zatai itama tana buqatar shi. Dare yayi Naufaliyyah anci kwalliya, an harde a gado Ameenullah ne ya shigo, " ya na ganki anan? Ai bina dakina zaki dan gaskiya ba zan din ga yawon bin dakuna ba ina da dakina, ai kamar jira take, har tana kusan kifewa ta miqe jiki na rawa ta kashe fitila ta ja qofa ta bishi, waiiiiiii makaranta kun san wace Naufaliyyah, ba sai na gaya maku budirin da aka sha ba ranar, dan ko abun sai su kawai, Ameenullah ya wahala🤣har mamaki yake wai ita wace irin mace ce? Komai tin anayi da dadi har a wahala? Gashi abin haushin ma in ba dan ta iya style kala2 ba sam bata kai Lamyah komai ba ta fannin ni'ima, ( makaranta kar ku manta fa ita gimbiyar kayan mata ne kala da kala, amma Lamyah ta fi amfani da natural abubuwa, bata yarda da shan kayan da bata sani ba, komai zatai da natural take yi, yanda zai gyara mata jiki, ba ya gyara ta na dan lokaci ba daga baya a bata ta ba, dan haka yana da kyau mu farka mu kiyaye binda zai amfane mu da wanda ba zai amfane mu ba). *Bayan wata biyar* " Masha Allah barakallah, wannan baby ba qaramib kyau yai ba, Sannu my sister, kin yi matuqar qoqari,ba mai cewa daga jikin ki wannan qaton baby ya fito ba," dariya sukai, amma banda Naufaliyyah, wadda gaba daya kallon da Farha ke watsa mata yake matuqar tsorata ta, amma tsabar hali irin na Farha ita zata juya ai dariyar da ita amma ta hana matar mutane sakewa, tin da suka zo Nigeria, Farha ta hana Naufaliyyah sakewa sam, yau dai Lamyah ta shirya yi wa Farha magana, " Sister ki bari mana, na fada maki komai yai daidai," habaaa dama jiran kadan take," eh amma da komai yai daidai ai ni ban fadi albarkacin bakina ba, baiwar Allah bari kiji, lokacinnan abinda ya hana ni zuwa na sumar dake da duk wani boka da malam tare da masu baki shawarar taba wannan gold din nawa shine wannan cikin, kwata kwata bari na fada maki gaskiya naji matuqar haushi da kk shiryu ban je na taba lafiyar jikin ki ba, amma bari kiji, alqawarin karaya da targade na kan ki a duk randa kk batawa 'yar uwata rai ina fatan kin gane," kamar wawuya Naufaliyya ta kada kai, cike da matsanancin tsoron Farha, " Gud now we can be freinds" miqa mata hannu tai sukai sallama, cike da ajiyar zuciya Naufaliyyah ta sauke hannun ta, Bala ne ya kira mai jego ta miqe ta fita, " Sistern kinnan can kill with only her look, ba qaramin tsoro take van ba," dariya Lamyah tai sosai ," qashi da ran kk tsoro?" " keee bar wannan qashi da ran cike zuciyar ta take da qarfida izza," " Allah yasa ba zance na naji ana yi ba," " Aaaa mu ba zancen ki muke ba mukacenyaro kyakkyawa da shi tubar kallah," Lamyah me zatai ba dariya ba, kyakyatawa taje kamar me, wayar ta ce tai qara ta dauka, "Yah Amee na" shine abinda aka rubuta a wayar, murmushi tai ta daga, tashi tai ta bar waje, bayan sun gaisa ya fada mata bayan suna da kwana uku zasu zo har Baaba suje Rimin gata dan ganawa da iyayen ta na can, gaban ta ne ya fadi da tinawa da tai da su........ *Sai nace Farha Allah ya raya baby boy, TEEM FARHA INA BARKA🤱🏻* [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *Qarin bayani da magana akan abinda novel din 'YAR RAWA ya qunsa* Page 30: 1- Neman ilimi abune mai matuqar mahimmanci, both western education and islamic one, dan in kana da ilimin addini dana zamani akwai abubuwan da dole zaka banbanta da mutane da dama. 2- kar mui wa mamatan mu kuka, kuka irin na jahilci, kururuwa da iface2, mu zama komai zamui mui amfani da ilimin mu, kuka dole ne, amma mu yi shi yanda islam ya nuna mana ba kuka irin na jahilai ba,mui kuka mai hade da nemawa mamaci rahamar Allah, shine asalin soyayyar mu a gareshi. 3- Yana da kyau kowacce mace ta zama cikakkiyar macen da zata kange kowanne lungu da saqo na zuciyar mijin ta, yanda ba zai so rabuwa da ita ba ko na secod daya sai da babbar lalura, in ko bata tare da shi zai ji matsanancin kewar ta, ba yaimurnar qaya bata nan ba. 4- ki zama matar rufin asiri, matar da ko wanne hali zaku shiga ke da mijin ki ba mai ji, zaki hakuri, har ki sama maku mafita, ko ki sama wa kan ki mafita. 5- Yana da kyau bawa ya kiyaye dikokin Allah a kan shi, a koda yaushe kuma a kowanne lokaci, in ka kiyaye dokokin Allah Allah zai kiyaye ka daga dikkan abun qi. 6- Mu riqe ibada, duk wanda ya riqe ibada da azkar na safe da yamma, Allah zai kare shi sannan zai mai katanga daga manyan kaba'irai, zai daukaka darajar shi duniya da lahira. 7- Bawa ya guji yin shirka ga Ubangijin shi, shirka ko wacce iri ce haramun ne, hukuncin shirka wutane direct, sai idan bawa ya tuba, shirka ta fara daga kan canfi ne, qin dayan ta Allah, zuwa wajen bokaye ko malaman tsubbu,neman biyan buqata a wajen wanda ba Allah ba, musamman buqatar da bawa ya san ba wanda zai biya mai wannaj buqata tashi sai mahaliccin shi. 8- MATA MU GUJI MUMMUNAN KISHI, mumkunan kishi na kai mata da dama wuta, wai shin mene ne a kishi ne? Kishi ni a tawa fahimtar shine, qoqarin kiyaye abinda kk so kar ya fada ga halaka,da kuma faranta ma abinda kk so ta hanyar halak, dan haka in kenan qarin aure a wajen mazajen mu zai zama ya fidda mijin ki daga halakar misali zina kenan zaki kishin shi ki bashi dama a duk sanda ya zo maki da batun qara aure? Sannan ba zaki zama mai fasadi a cikin gidan shi ba saboda kawai an maki kishiya? Zaki zama mai qoqarin faranta ma mijin ki ne kawai ba tare da kin cutar da abokiyar zaman ki ba, kowa ta shi ta fisshe shi, da dama abinda mata bamu sani ba shine,ki gama haukan kishin ki, da biye2n bokak ki, mijin ya kubce maki da kiftawar ido, sannan ki gama mai gatan in ba dan Allah kikai ba ke ko dan Allah kikai ya zo ya baki kunya gaba ga kishiyar taki, ko a bayan idon ki ya zage ki tas dan kawai ya samu wajen zama gun waccan, dan haka koma zaki na kishi ki yi shi bisa tsarin islam, ki kyautata zaman ki da abokan zaman ki, ki ba mijin ki dama ya halasta abinda Allah ya halasta mai. 9- In Allah ya sa zama ya hada mu da dan da ba mu muka haifa ba, mui mai riqo na tsakani da Allah, ruqon gaskiya, domin ba mu san me zai zama ba gaba da zamu mora, kai ko ba zamu mora ba ma zamui domin Allah ya bamu lada, ta wani bangaren kuma bamu sani ba muma zamu rayu da namu? Su waye zasu riqe mana namu? In kikai ma dan wnai riqo mai kyau aiwa naki mai kyau. 10- Komai qanqantar abinda Allah ya hore maka in kaga wanda bai kai ka ba yana buqatar taimako ka taimaka mai, kaima Allah sai ya duba abinda kai ya qara maka. 11- Riqon alqawari yana da matuqar mahimmanci da lada mai dimbin yawa. *Wannan hasashe na ne a cikin wannan novel mai suna 'YAR RAWA, duk wadda take da nata hasashen qofa a bude take dan a qaru da ilimin da Allah ya bata itama na gode* *Haermeen Haermmaerh na godiya da soyayayyar ku da addu'o'in ku na alkairi a gare ta, tana matuqar son ku itama*❤ [1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH *I am so sorry fans, yesterday's chapter is awful, banda lfy ne, kuma ban da sha'awar rubutun kwata2, amma saboda yanda naga wasu na son nayi yasa nayi din abinda kuke so shi nake so,hope za a yafe ma Haermeen Haermmaerh*❤ *Ana uhibbukum katheeran*❤ Page 29: Wasu larabawa na gani kyawawa su uku,sun sha dogayen riguna har qasa, a cikin garin lagos, da alama duk da kyaun su gajiyar da sukai bata boyuwa, yau kwanan su uku suna yawon neman Lamyah, da Mubarak, wanda suke amfani da hoton ta dake cikin wayar mahaifin ta, wasu maza suka samu su biyu a wata mota mai baqin glass, suka tsaya, El-Hussein shi ke jin turanci shine yai masu magana," Assalamu alaikum, pls do u know this gurl? Her name is Lamyah," hada kai sukai suna kallon hoton kamar masu nazarin ta, sai suka fara magana qasa2, dayan ya ce ma dan uwan shi," Oh boy this people rich oo, we fit collect there bag, and take them to Oga Mikel na him know wetting him go do with them abi?" " u don talk wetting dey for my mind," kada kai sukai dayan su ya amsa da ," yes i know her, let us take u to her," cikin tsananin farin ciki zuciyar su cike da mugunta da kwadayi suka shige, muhammad har wani kada kai yake, yana ayyana irin hukunta Lamyah da zai, sannan da abubuwan da zai da dukiyar in sun karbe, tafiya ake ba ta qare ba,dama gasu a gajiye, nan danan bacci yai gaba da su, a hankali daya daga cikin mazan nan biyu ya juya ya zare jakar hannun El- Hassan, rage gudun motar dayan yai,shi ya fice daidai wani gidan katako, da sauri ya bude qofar ya wurga jakar sannan ya rufe ya fito suka sa kai,wani tankamemen gida suka je, wanda kyaun shi ya wuce na tsaya fasalta shi a dan wannan novel, mak gadin gidan na leqowa sakamakon horn da ya ji, ya ga mazannan nan da nan ya washe baki ya bude gidan, shigeea sukai, wanda yai daidai da farkawar su Muhammad, a zuqatan su suna ayyana kudin El-mustapha, washe baki suka hau yi, suna murna, larabci suke ta zubawa, nuni sukai masu da su fito, fuskar su ba walwala, budewa sukai suka saka qafafun su waje, suna gaba suma su Muhammad suna biye, qara kallon gidan suke suna ayyana mugunta kala2 a zuqatan su, wani wawakeken parlor aka kaisu, suka zauna a kujeru na alfarma, kalle2 kawai suke basu ga kowa ba ko wanda suka kawo su basu sake gani ba, dan tin da suka shigo sukai wani babban qofa suka aje su nan basu kuma ganin su ba, leqa qofar nai ganin qwaqwaf👀 wani qasungurmin mutum na gani, mai cikar gashi a fuska, jikin shi ba riga sai wani zani daya daura, shima kamar ya balle, da wata sanda a hannun shi, sai uban sanqo, tubar kallah baqin shi kam ban isa misali ba, ji nai fitsari na neman kufcen da yai magana," weldone Sam and Emma, ur work dey do me well oo, go inside and take two box my boys," " Ahhh oga make am three na? Na three men dey there oo," " k make u carry three then," godiya sukai suka fito dauke da akwati suka wuce su,ko ci kan ku ba su ce masu ba,su kuma har da daga masu hannu, a zaton su Lamyah ce ta sallame su,wata qila sun mata bayanin yanayin su ne ta gane sune, Muhammad ne ya fara kitsa masu abun da zasui data bayyana, suna cikin qus2 suka ga wani jibgegen qato ga tsawo ga qiba yana takawa da kyar dan ko takalmi baya sawa," Ya Rabbiiiii," El- Hassan dake kallon qofar ya fada a matuqar tsorace, suma juyawa sukai,ai suna ganin shi suka firgice suna neman hanyar guduwa, masu gadin dake tsaye a kowacce qofa ce suka shigo suna muzurai, wannan baqin qaton ne ya barke da magaukaciyar dariya ya hau yarabanci, nan da nan na ga su Muhammad suna takurewa a hankali suna dunqulewa sai ihu suke, daga hannun shi sama yai, tini suka tashi sama a matsayin tsintsaye masu kalar fari da blue masu kyau, manya, dan ni kam ko sunan su ban sani ba, nan take wasu maza hudu suka fito ta wata siririyar qofa na gaba dauke da sharbebiyar wuqa, take na sake fitsarin da ya matsen dan tsoro, ta daidai bayan qofar dana maqale suka wuce, ukun ne suka dau tsintsayen nan dake ta kada kai, sukai waje da su,kowa ya bisu, na lallaba nabi bayan su, gani nai sun je gaban wani qaton gunki, sun danne tsuntsayen nan, wannan qaton mutumin ya karbi wuqa a hannun dayan su ya fara yanka kowanne tsuntsu yana surutai da yare, yana gamawa kowa ya daha hannu sama sukai yare sannan suka nuna gunkin, hankalina ne ya tashi ainun, ganin kudi na fita daga bakin wannan gunki, ai qafa mai naci ban baki ba, na fece,kan na zama na baddawa. Shi kenan qarahen akewa qasa, qarshen mai kwadayi da mugunta tare da mugun hali kenan.😭😭 Anyi suna lfy inda Baby yaci sunan El-Mustapha, Lamyah ta yi kuka sosai ranar, wanda Farha da mubarak ke taya ta, dan sun iso a ranar kwana uku kenan da sunan, tai wa Farha godiya ba iyaka, Farha taso a sakaya sunan amma Lamyah ta roqi da su bar shi haka, tana son ta ji ana kiran sunan mahaifin ta, haka zata fi jin dadi sosai, a haka aka bar shi, aiko yaro yaga gata wajen Yah Amee, innace gata ina nufin gata, iya gata, har kudin da za su saka shi makaranta daga play class har University sai da Yah Amee ya bayar, dan yace komai yayi ba zai biya su sunan Abiin shi da suka saka ma dan su ba. A kwana na hudu ne da zuwan su suka shirya tsaf dan zuw Rimin Gata,sosai Farha ta so aje da ita ta qara ganin Inna dan bata hakurin dukan da tasha amma suka hana ta aka ce ta zauna da ita da Tani a ranar suke son dawowa, haka ta hakura, amma matuqa taso zuwa, sannan ta ci wa Delu mutunci, dan ta matuqar tsanar ta, haka Lamyah ta lallaba ta suka tafi aka barta da cizon yatsa tana ta saqa irin tsiyar d zatai da an bar ta. Da misalin qarfe sha daya suka isa, inda Saddiqa na riqe da Lamyah qarama a hannu, Musaddiq ya dau zani ya saka alamar jira yake a saka mai ita ya goye, sukai sallama, leqowa Inna tai, taga su waye, ganin Lamyah ne ya sa ta zaro ido tana leqa bayan Lamyah taga ita da waye? Dan tabbas ba ta son qara haduwa da Farha ko a hanya, ganin ba farha ne yasa ta dan pito waje,fuskar ta ba yabo ba fallasa, dan yanzu ta gama gane komai game da Lamyah, tsananin kishi ne ya sa Delu ke kushe su ai ga shi nan ta ga ishara itama,sannu da zuwa tai mata ta shiga da ita daki, ta saka mata tabarma, su Yah Amee da Bala tare da Baaba da Mubarak na fadar mai unguwa, Momma ce ta fara zama, tana kallon gidan, a nan ne wai akai wa Lamyah wulaqanci? Sai kace wata uwar ke gare su, gaishe gaishe sukai, dai dai lokacin da Musaddiq da Saddiqa suka fito, dan suga su waye, kwata2 qin yarda yai Saddiqa taje gida inda dan ta'addan dan Delu yake balle aiwa iyalin shi irin na Delun, " Lamyah sarkin rikici, nikam Baban Lamyah anya 'yar uwata ba tai rikici ba tana qarama? Ka duba kaga yanda yarinyar nan ke hana mu bacci? Badan inna na taimaka mana ba," " ba wani riki......." maganar shi ta maqale sakamakon arba da Lamyah babba da yai zaune tana ta maka mai murmushin ta mai kyau, da sauri ya daga labulen ya shiga," Lamyah? Os that you?" " ni ce Yah Musaddiq," ta fada tana miqewa, kallon kallo sukai ita da Saddiqa wadda ta isa da hanzari ta rungume Lamyah, gam kamar za a kwace ta, idon ta cike da hawayen dadin ganin 'yar uwar ta,murna sukai sosai da ganin juna, gaisawa sukai sannan Lamyah ta tsokani Musaddiq," Yah musaddiq a ban takwarar tawa mana, duk da dai naji ana man sharrin rikici," ta maida kallon ta kan Saddiqa," Aaa yanzu ai dana gan ki na janye, sai dai gado tai wajennnnnn," tana kallon Musaddiq daya jefe ta da hararar masoyan da suka shaqu da juna su, hamdala Lamyah tai cikin ranta,dan da dikkan alamu burin ta ya cika, " Yah Musaddiq tare nake da Baaba da Yah Amee suna fada," inna ce da ta fitk daga gurya dauke da jug da ruwan randar sanyi ta ce," kash amma dai ke ma akwai wauta, da baki magana ba wannan yaron ya kai masu koda ruwa ne? Maza tashi ka je ka kai masu wannan bari na kawo maku wani, " yana qoqarin miqewa ne yaji shigowar su ciki da Mai Garin, dake babban parlor ne wajen dan haka zai ishe su dika, shimfida akai ma mai garin ya zauna, bayan gaishe2 ne, da ban hakuri, Baaba ya debo kudi masu yawa ya bawa Musaddiq yace a saiwa Baby kwalli godiya sukai sosai,inda Yah Amee yace ya dau nauyin karatun ta itama har University nan take ya rubuta cheque ya basu, dan yace yana son amaryar shi tai karatu sosai, nan akai wasa akai dariya,inda Yah Amee ya buqaci ganin gidan da aka haifi Ammiin shi, nan take mai gari da Inna sika kalli juna suka sadda kai qasa," ranka ya dade na sha fada maku, in kana jin tsoron wancan shashashan a matsayin ka mutanen ka su ji me? Ka dinga daurewa kana nuna isa da izzar ka a matsayin ka na mai shugabantar wannan unguwa," " Bawai tsoro nake kar naje ba Musaddiq, baqin mu ne bana son su fuskanci matsala daga wajen shi musamman in muka je bai bugu yai bacci ba,dan har ni za a je," " me kefaruwa ne?" " ba komai ku tashi mu je," miqewa sukai, Lamyah duk tsoro ya cika ta, da tsoron sake ganin Delu. Shigar su gidan ke da wuya suka ji wani wari sosai,toshe nacin su sukai, suka qarasa tsakar gidan duk datti qasu qananan yara ne, a zazzaune a rakube, sai wani mutum a qasa kayan shi sunyi baqiqqirin, shi kanshi kamar mahaukaci, a hakan wai bacci yake, wata mata ce qemasassa ta bushe bazata wuce 34 ba amma kamar ta fi haka dan wuya, Hamza ne ya fito shima daga wani daki da sanda a hannun shi, ," Kulu su waye nan?" " me gida ban san su ba nima amma dai da mai gari da dan shi babba sai Innar mai gari," " To to to ya yi ku shigo bismillah, Lamyah ce ta tiqe Ameenullah dan tsoro da kuma aman da ke taso mata, da sauri kuwa yace,"A'a nan ma yayi dan va dadewa za mui ba," Inna ce ta je wani qofar daki ta daga labulen Delu ce kwance kamar matacciya, ga qafar ta day ta rube, sai fuskar ta ta gefe da ta dauje wajen ya kumbra shima yana ruwa, aman da Lamyah ke riqewa ne ya balle, aiko ta dinga kwara shi kamar ta amayar da hanjin ta, da kyar Delu tai magana," su waye anan?" AMEENULLAH NE MIJIN LAMYAH DIYAR AMEENAATOU ji tai kamar an kwada mata guduma aka, qoqarin juyar da kan ta tai cikin azaba, da kyar ta kalle su,sai ta saka kuka," yar nan ki yafe min ko na ga daidai kan mutuwa ta, ko Allah ya yafen kadan daga laifukana," shima Hamza rusunawa yai yana kuka yana neman yafiya, Lamyah da kyar take magana itan ma kukan take," in dai haqqi na ne ya kama ku haka na yafe maku,zan so ace mahaifiyata na nan ta yafe maku itama ko kun samu sauqin wannan azabar," Hamza ne ya fara basu labari akan lalurar su. Wata uku da suka wuce ne muna zaune ni da gyatumar mu muka ji kawai an shigo ba sallama,daga kan da zamui sai muka ga dan uwana da ya bar gida sakamakon shaye2 da dabanci,cikin doki Delu ta miqe ta isa gare shi shima ya gaida ta kamar abun arziqi, nan muka bashi abinci da ruwa yai wanka, kwatsam rannan na tafi gona na dawo, sai na tadda dan uwana a dakin iyalina, ta taushe mata baki ba damar tai ihu, Delu naje na kirawo, aiko bai daga ta ba sai da ya ida nufin shi, ya fito yana gyara wando, yana maganar ashe haka nake kwasar gara, daga yau sai dai a raba ta da shi, nai k kukan kura na kwada mai mari, fusatar da yai ta sa ya shaqe ni ya sa gannuwan shi cikin idona ya danne, nai ihun neman ceto , ganin haka Delu ta dakko muciya ta kwada mai, yana juyawa ya kalle ta ta tsorata ta kwasa da gudu, a nata kallon waccan katangar zata iya tsallake ta ne, tana dira qafa daya ta karye, ta fadi kan marmara, bai kula ta ba, ni kuma nan take naji bana gani, munyi kukan azaba ranar ba mataimaki, matata dan qunci da tsamin jiki, dan saida ta sha duka sosai a wajen shi ya samu nasara akan ta, ba zata iya tasowa ba, haka muka wuni zubur, sai da yaran mu sika dawo daga gidan yayar su suka taimaka mana, wannan shine abinda ya same mu bamu da yanda zamui da shi ga shinan kuma bamu da kudin magani. Lamyah sarkin tausayi,kuka take riris,ran Ameenullah kuwa ba qaramin baci yai ba, dan irin kukan da suka sata,miqewa yai ya zaro waya yai waya sannan ya miqa masu kudi masu yawa sosai,yace kar su damu nan da wasu mintuna za a zo a dauke masu shi a kaishi inda ya dace da shi, sannan ga kudi nan su nemi lfyr su, sun tainaka masu ne kawai dan Saddiqa da ko kallo basu ishe su ba, godiya kam sun sha ta, ba iyaka. Bayan sun koma gida ne Lamyah jiki ya tsanan ta, asibiti kawai Ameenullah ya wuce da ita, gaba daya Mubarak da Naufaliyyah sai kuka suke, ganin yanda jikin ta yai, suna isa likita ya duba ta, gwajin farki suka gano ciki dan wata hudu a jikin ta,tsananin mamaki kam Ameenullah da Lamyah sun sha shi, ciki har wata hudu ba su sani ba? Ta yaya? Ikon Allah, shine abinda Lamyah ke ta fada kenan, nan take ko ya hau waya yana sanar wa, kafin kace me su Farha an iso, dan da Bala yace su zauna kuka tasa, sai da aka zo da ita. *Bayan shekara hudu* "Uncle Mubarak zan sha nima" wata kyakkyawar yarinya ce take fadan haka, ta sha gayun ta da irin kayan mutanen Nijer,gashin ta har bayan ta, an raba biyu an daure kowanne gefe, da band kala2, sai rigar ta data sha saqi fara, da zanin ta blue dark, sai dark blue din takalmi, da sarqa da dan kunne farare, na bits, Ameenaa kenan, diyar Lamyah da Ameenullah, Lamyah na gefe, tana karatun ta a Laptop, Ameenullah na zaune yana kallon Mubarak da Ameenaa. Mubarak ne ya miqa mata chocolate din Diary milk tai ta tsalle tana murna kuwa," Mubarak dama baka bata va yarinyar nan so take tafi maman ta shan chocolate fa wasa2," tura bak tai ta tafu wajen Lamyah da gudu ta haye cinyar ta tana shagwaba, " yi shiru Ammii na ki sha abin ki in ma basu baki ba zan siyo maki da kaina," " ai ku kam sai Allah abu daya ne kk qi koya mata har yau a halin ki," matsawa kusa da su yai ya rungume su dika bayan ya bisu da kiss, " meye shi?" " RAWA" harar wasa ta mai, sikai dariya,gani nai Ameena ta miqe da gudu tai wajen Naufaliyya da ta riqo hannun wanj qaramin yaro suna kiran shi Sultan, yaci sunan Baaba Mus'ab, wasa ta ja shi inda ita kuma Naufaliyya ta ke tahowa wajen su, tin daga nesa suke sakarwa juna murmushi. HAUSA NOVELS SOKOTO WHATSAPP NO: 07068808039 ABDULMKIBAB.HEXAT.COM *ALHAMDU LILLAAH NA GODEWA ALLAH DAYA BAN IKON KAMMALA WANNAN NOVEL MAI SUNA 'YAR RAWA, UBANGIJI YA SA MU AMFANA DA ABINDA KE CIKI NA ALKAIRI. WADDA NA BATA WA RAI DAGA FARKON NOVEL DINA ZUWA QARSHEN SHI INA NEMAN TA YAFEN, LAIFIN DA NAI A CIKI ALLAH KA YAFEN.* *HAERMEEN HAERMMAERH NA GODIYA. LOVE U XOXO❤*