Lamborghini Huracán LP 610-4 t
SHIGANAM ZUWA HAUSA NOVELS 24daily postclick here to Homeclick here to hausa novelsAbout me
Ab
click to call admindc10_aircraft2

Abubuwan da yakamata adinga sha alokacin zafi

Abubuwan da yakamata adinga sha alokacin zafi
Malama Maijidda Badamasi Shu'aibu Burji wata kwarariya ce kan fannin abinci kuma malama a makarantar sakandaren 'yan mata da ke Darmanawa a Kano, kuma ta bayyana jerin abubuwan da ya kamata a dinga ci a wannan yanayi. 1. Gurji - Gurji kayan lambu ne da ke kunshe da saindarai daban-daban masu amfani da kare lafiyar jiki da fata 2. Mangwaro - Yana kare konbewar ruwan jiki. 3. Manyan lemon tsami - Yana kunshe da sinadaran bitamin C da B da sindaran Mineral kamar Calcium da Phosporous da Magnesium. Ana iya sarrafa lemon tsami ta hanyar matse shi da kara masa ruwa da sanya sikari daidai idan ana bukata. 4. Kankana - Kashi 95 cikin 100 na kankana ruwa ne kuma shanta na kawar da kishi ruwa sosai. 5. Tsamiya - Ita ma tana daga cikin 'ya'yan itacen da suke taimakawa wajen inganta jiki lokacin zafi. Ana iya dafa ta tare da masoro da na'ana a tace ruwan a sanya dan sikari idan ana bukata a dinga sha. 6. Ruwan Rake - Ya kunshi sinadarai kamar Potatssium da Glucose da Calsium da Magnesium, sannan yana da amfani wajen kara wa jiki ruwa. 7. Ruwan Kwakwa - Shi ma ruwan da ke cikin kwakwa yana da muhimmanci a dinga sha lokacin yanayin zafi. 8. Gwaiba - Malam Maijidda ta ce gwaiba ma wani muhimmin kayan marmari ne da jiki ke bukata miusamman a lokacin zafi, saboda sinadaran da take dauke da su kan masu inganta yanayin jiki ne. 10. Abarba - Ita ma tana da sinadari masu saurin sa abinci ya narke da kuma ruwa sosai a cikinta. 11. Tumatur - Kashi 94 na tumatur ruwa ne. Za a iya cin sa haka ko a markada ko a saka shi cikin abinci. 12. Korayen ganyayayaki - Kusan kashi 80 zuwa casa'in nasu ruwa ne, wanda yake sawa su narke nan da nan idan an ci su. Hakan na sawa su sanyaya jiki. Ganyayyaki sun hada da kamar su zogale da latas da lamsur da alayyahu da sauran su. by:Admin Abdul
Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE
M.sharif